• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 12, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

by ABUBAKAR IBRAHIM
July 11, 2025
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana da cikakken ƙudiri na tabbatar da ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi domin zurfafa dimokiraɗiyya da kuma hanzarta cigaba a matakin ƙasa.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Juma’a, lokacin da ya karɓi tawagar Ƙungiyar Tsofaffin Kansiloli ta Ƙasa wadda ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa.

Ya ce: “Ƙananan hukumomi su ne mataki na uku na gwamnati kuma su ne suka fi kusa da jama’a. Shi ya sa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin hikimar sa ya sake duba batun ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.”

Ya tunatar da cewa a bara, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ya nemi fassarar doka daga Kotun Ƙoli, inda kotun ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.

“An samu hukunci daga babbar kotun ƙasa da ke nuna cewa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi buƙatar ƙananan hukumomi su samu ’yancin kai – su kasance masu cikakken iko da damar aiki a fannoni daban-daban, ko siyasa ko kuma kuɗi,” inji shi.

A cewar sa, bai wa ƙananan hukumomi dama za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa da kuma samar da cigaba a cikin al’umma.

Idris ya nuna damuwa kan yadda tsarin ƙananan hukumomi ya raunana a tsawon lokaci, yana nuni da cewa tsarin ya sha bamban da yadda aka tsara shi tun farko.

“Tsawon shekaru, mun shaida yadda ƙarfin ikon ƙananan hukumomi yake ci gaba da raguwa fiye da yadda kundin tsarin mulki ya tanada,” inji shi.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda gwani ne wajen kare dimokiraɗiyya, yana da tabbacin cewa ƙarfafa wannan mataki na gwamnati yana da matuƙar muhimmanci domin cigaban dimokiraɗiyya a ƙasar nan.

“Shugaban Ƙasa ɗan dimokiraɗiyya ne na gaske, kuma yana ganin cewa domin dimokiraɗiyyar mu ta kai inda muke fata, dole ne a ƙarfafa wannan mataki na gwamnati,” inji shi.

Ya buƙaci gwamnoni da su mara wa ƙoƙarin Shugaban Ƙasa baya wajen dawo wa da ƙananan hukumomi ƙarfin su yadda masu tsara kundin tsarin mulki suka nufa tun farko.

Ministan ya kuma gode wa tsofaffin kansilolin bisa jajircewar su wajen kare dimokiraɗiyya, tare da roƙon su da su isar da saƙon gwamnatin Tinubu ga jama’ar ƙasa.

“Ina roƙon ku da ku tallafa wa sauye-sauyen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ba a tsara su domin wahalar da ‘yan Nijeriya ba. E, da farko za su iya kasancewa masu tsauri amma kamar yadda Shugaban Ƙasa ya faɗa, tattalin arzikin mu yana samun daidaito,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa cire tallafin fetur da daidaita farashin musayar kuɗaɗe da aka yi sun haifar da gagarumar riba, wanda hakan ya haifar da ninka kuɗaɗen da ake raba wa jihohi da ƙananan hukumomi domin aiwatar da ayyukan cigaba.

Ya ƙara da cewa kafa kwamitocin cigaba a kowane yanki na ƙasa wani mataki ne na ganin cigaba ya isa kowane lungu da saƙo na Nijeriya.

Tawagar tsofaffin kansilolin ta karrama ministan da Lambar Yabo ta Maida Hankali Kan Jama’a, inda shi kuma ya nuna godiya tare da cewa hakan zai ƙara masa ƙwazo wajen yi wa al’umma hidima.

A nasa jawabin, Sakatare na biyu na ƙungiyar, Mista Cole Michaels, ya yaba da irin yadda ministan yake farfaɗo da hukumomin da ke ƙarƙashin sa domin wayar da kan jama’a kan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.

Ya ce an bada lambar yabon ne saboda gudunmawar sa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar.

Tawagar ta ƙunshi wakilai daga jihohi daban-daban a ƙasar nan, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar, Mista Auwal Kassim Hassan.

* Hoto:
Daga hagu: Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Kansiloli ta Ƙasa, Hon. Samaila Mumin; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, da Shugaban ƙungiyar, Auwal Kassim Hassan, lokacin da ƙungiyar ta miƙa wa ministan kyautar karramawa sa’ilin da suka ziyarce shi a ofis ɗin sa a Abuja a ranar Juma’a.

Loading

Previous Post

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

Related Posts

Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!