• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

by ABUBAKAR IBRAHIM
July 8, 2025
in Nijeriya
0
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A DAIDAI lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zaɓen 2027, Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai bari hayaniyar siyasa ta karkatar da shi daga aikin sa na kawo sauye-sauye masu ma’ana da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa domin amfanin ɗaukacin ‘yan Nijeriya ba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Talata, inda ya ce gwamnatin na ci gaba da aiwatar da muhimman manufofin da suka shafi cigaban tattalin arziki da jin daɗin al’umma, tare da nisantar duk wata hayaniya ta siyasa da ka iya janyo koma baya.

Idan an tuna, hayaniya ta turnuƙe kwanan nan kan wata haɗaka da waɗanda ‘yan siyasar adawa suka yi da nufin ƙwace ƙwaryar mulkin ƙasar nan daga hannun gwamnati mai ci yanzu a babban zaɓe mai zuwa.

Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.”

Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba.

“Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta ne, amma ‘yan Nijeriya sun damƙa wa Shugaba Tinubu wata gagarumar amanar sauyi, wadda aka gina bisa Shirin Sabunta Fata,” inji shi.

A cewar sa, shekaru biyu kacal bayan hawan Tinubu mulki, gwamnatin ta fara samun gagarumin cigaba a fannonin tattalin arziki da tsaro inda ake samun raguwar satar ɗanyen mai, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na daidaita, da kuma ƙarin ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas.

“Fasa bututun man fetur ya ragu ƙwarai, ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas na dawowa, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na samun daidaito, ana fuskantar matsalolin tsaro kai-tsaye, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya — iyalai, ɗalibai, masu aikin hannu, da ‘yan ƙananan sana’o’i — na amfana daga shirye-shirye irin su lamunin karatu, samun bashi na kayayyakin masarufi, sauya motocin haya zuwa masu aiki da iskar gas, da ingantattun ayyukan gwamnati da ababen more rayuwa,” inji Ministan.

Ya kuma bayyana wasu muhimman matakai da aka ɗauka kwanan nan, ciki har da rattaba hannu kan dokoki huɗu na gyaran haraji da za a fara aiwatar da su daga shekarar 2026, da kuma ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injuna a aikin gona da aka taɓa yi a Nijeriya.

“Makonni biyu da suka wuce, Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu kan dokoki huɗu masu muhimmanci na gyaran haraji, wanda ke zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin kuɗi da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya. Ana sa ran waɗannan gyare-gyare za su haɓaka walwala da cigaban iyalai da ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar nan,” inji shi.

“Kafin hakan, Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injina a aikin gona da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya — wanda ya kasance fara aiwatar da Shirin Sabunta Fata na amfani da injina a aikin gona. Wannan kuwa yana daga cikin jerin manyan shirye-shiryen amfani da injina a aikin gona da ake aiwatarwa domin tabbatar da wadatar abinci,” inji shi.

Ministan ya zargi wasu ‘yan siyasa da ƙoƙarin dagula hankali domin a ɗauke hankalin gwamnati daga cigaban da ake samu. Ya ce gwamnati ba za ta amince da hakan ba.

“Ba abin mamaki ba ne cewa sababbin haɗakar siyasa da ƙungiyoyin adawa ba sa son a ci gaba da maida hankali kan irin cigaban da Nijeriya take samu. Sai dai gwamnati ba za ta bari a jawo ta cikin hayaniyar da waɗanda ke son Nijeriya ta tsaya cak maimakon ta ci gaba da samun sauyi suka ƙirƙira ba,” inji shi.

A ƙarshe, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da ƙudirin ta na inganta rayuwar al’umma.

Ya ce: “Gwamnatin Tinubu tana maida hankali sosai tare da jajircewa wajen gina Nijeriya mai wadata ga kowa da kowa.”

Loading

Tags: BolaTinubuMohammedIdrisSabuwarAjandazaɓen2027
Previous Post

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

Next Post

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu'a

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!