HUKUMAR Shari’a ta Jihar Kano ta nemi haɗin gwiwa tare da ƙulla alaƙar aiki da Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta jihar domin kawo gyara da tsaftace tarbiyyar al’umma a jihar.
An bayyana hakan ne a lokacin wata ziyara da Hukumar Shari’a ƙarƙashin jagorancin Kwamishina na 2, Sheikh Ali Ɗan’abba tare da sauran ‘yan rakiyar sa suka kai wa Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a ofishin a jiya Alhamis.
A jawabin sa, Sheikh Ɗan’abba ya ce sun kai ziyarar ne domin ƙarfafa musu gwiwa da bada shawarwarin da suka dace tare kuma da haɗa wannan hannu wajen tabbatar da ingantacciyar tarbiyya a jihar baki ɗaya.
Ya ce: “Muna yaba maka bisa ga yadda muke tunani a kan ka ba haka muka gani ba, domin aikin da kake yi abin a yaba maka ne.”
Haka kuma ya yaba wa shugaban hukumar bisa ga yadda yake ƙoƙari domin ganin an dakatar da dukkanin wasu finafinai da ake ganin za su lalata tarbiyyar al’umma.

Da yake mayar da jawabi, Shugaban Hukumar Tace Finafinai, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana ziyarar a matsayin wani ƙaimi da aka yi wa hukumar sa tace tare da alƙawarin haɗa hannu domin tafiyar da ita yadda ya kamata bisa tsari na tarbiyyar Musulunci.
Ya ce: “Shi aiki idan akwai waɗanda za su taimaka maka, ya fi tafiya yadda ya kamata. Za mu yi duk ƙoƙarin mu domin ganin mun haɗa hannu da ku, domin a tsaftace aikin mu.”