Ministar Harkokin Agaji Da Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa a yanzu sabuwar Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa, wato ‘National Disability Commission’, ta riga ta kafu bayan amincewa da naɗa shugabannin ta da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2020.
A cikin wata sanarwa da hadimar ta a ɓangaren aikin jarida, Hajiya Halima Oyelade, ta bayar a ranar Alhamis, ministar ta ce tun daga naɗin ta a bara ta sha alwashin tabbatar da ganin an kafa wannan Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa kuma ta fara aiki.
Ta ce, ‘’Wannan ranar farin ciki ce a gare ni wadda buri na ya cika, ganin cewa wani sashe na mutane masu matuƙar buƙatar tallafi waɗanda na ke jin tausayin su, a ƙarshe sun samu hukuma tasu ta kan su, har an naɗa mata shugabanni waɗanda za su tafiyar da al’amurran ta, kuma ta kare haƙƙoƙin su, sannan ta sama masu kyakkyawan yanayi da za su inganta rayuwar su har su bada tasu gudunmawar ga cigaban al’umma baki ɗaya.”
Ministar ta miƙa godiyar ta ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda rattaba hannu da ya yi kan Dokar Hana Nuna Wariya Ga Naƙasassu ta Shekarar 2019 a bara, wadda ta bada damar a kafa hukumar.
Sadiya Umar Farouq ta ce: ‘’Ta hanyar amincewa da naɗin shugaba da Babban Sakatare da sauran membobin cibiyar gudanarwar hukumar, Mai Girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara nuna sadaukarwar sa ga batun inganta rayuwar mutane marasa galihu a Nijeriya, kuma ya ba su damar su ma su ci moriyar dukkan haƙƙoƙin su a matsayin su na ‘yan Nijeriya.”
Ta taya murna ga naƙasassun da ke Nijeriya waɗanda ta ce yawan su ya kai mutum miliyan 30 saboda wannan babbar nasara da aka samu, kuma ta yi kira a gare su da su yi amfani da wannan dama da aka sama masu.
Hajiya Sadiya ta ce: ‘’Ina taya murna ga ‘yan’uwa na maza da mata waɗanda ke rayuwa da wata naƙasa a Nijeriya saboda wannan cikar buri, kuma ina kira a gare ku da ku yi amfani da damar samun wannan hukuma wajen haɗa kan ku don gina rayuwa mai albarka.”
Har ila yau, ministar ta taya murna ga shugabannin hukumar da aka naɗa tare da yin kira a gare su da su yi aiki tuƙuru.
Ta ce, “Ina taya ku murna sosai, kuma ina kira a gare ku da ku ɗauki wannan wannan naɗi naku a matsayin wata dama da ku ka samu ta zama shugabanni na farko na hukumar, don haka ku shimfiɗa fandeshi mai ƙarko na hukumar, tare da tunanin cewa samun ingancin rayuwar mutum sama da miliyan 30 da ke fama da naƙasa a Nijeriya yanzu ya danganta kan yadda ku ka aiwatar da aikin ku.”
Da zaran Majalisar Dattawa ta amince da naɗin, hukumar za ta shiga aiki gadan-gadan, inji ta.
Minista Sadiya ta ce, ‘’Ayyukan hukumar sun haɗa da fito da tsare-tsare da manufofin da su ka dace tare da aiwatar da su don ilmantar da naƙasassu da kyautata rayuwar su; tsara hanyoyin inganta rayuwar naƙasassu, da kuma kyautata rayuwar su ta hanyar sauya tunanin mutane su daina yi wa naƙasassu kallon banza.”
![]()






