• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Gidan Kashe Ahu’ da Ranar Harshen Hausa ta Duniya

by DAGA KABIR UMAR PRO
August 26, 2020
in Tsokaci
0
Dandalin 'Duniya Gidan Kashe Ahu' a lokacin da Shata ke wasa

Dandalin 'Duniya Gidan Kashe Ahu' a lokacin da Shata ke wasa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ZAN sadaukar da rana mai kamar ta yau, 26 ga Agusta, 2020, watau Ranar Harshen Hausa ta Duniya, ga yadda gagarumin shirin nan na ‘Duniya Gidan Kashe Ahu’ ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban harshen, musamman idan mu ka yi la’akari da yadda makaɗa da mawaƙa da kafar sadarwa na wancan lokacin su ka inganta harshen Hausa, ɗabi’u da al’adun Malam Bahaushe.
 
Da an ambaci shirin ‘Duniya Gidan Kashe Ahu’,  babu abin da zai zo wa mai karatu sai gidan talabijin na NTA Kaduna. Maƙasudin shirin shi ne domin a nishaɗantar da ilimantar da masu kallo daga akwatinan su na talabijin. 
 
Shirin ya na da burin zaƙulo fitattu da masu tasowa na makaɗa da mawaƙa na gargajiya a wancan lokacin. Ya kuma ci nasarar sada zumunci a tsakanin ‘yan kulob, makaɗa, mawaƙa da ma’aikatan gidan talbijin. Haka kuma ya yi nasarar jawo ƙanana da manyan masu kallon tashar NTA wajen ci gaba da kallon ta. Ya kuma inganta ayyukan ‘yaan kulob da ƙara ƙarfafa masu gyiwa a tsakanin su. 
 
A cikin shekara ta 1976 akwai shirye-shiryen talbijin irin su ‘Kukan Kurciya’, ‘Tambari’, ‘Sahoro Da Sahorama’, ‘Galhanga Da Shiba’, da ‘Samanja Mazan Fama’ waɗanda ake gabatar da su da dare don nishaɗantar da masu kallo kafin su kwanta barci. 
 
Bayan gidan talbijin na ƙasa NTA ya koma gabatar da shirye-shiryen sa ta talbijin mai kala a lokacin mulkin soja na Janar Murtala Ramat Muhammed ana ta ƙoƙarin gudanar da bikin al’adun baƙar fata na duniya, wato FESTAC, a 1977.
 
Garba Yakubu Suleja ya na ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan  NTA a lokacin wanda ya yi shawara da mutane irin su Musa Aliyu Keffi (Mijin Hajiya), Umar Kwantagora (Sanƙira), Sani Gwarzo (Tumbuleƙe), Hajara Ibrahim (Hajjo Ta Binta Ƙasaitatta) aka ƙirƙiri tare da gudanar da wannan shirin na ‘Duniya Gidan Kashe Ahu’. 
 
A shirin, ana gayyatar makaɗa da mawaƙa  a duk sati tare da ‘yan kulob domin gudanar da shirin. 
 
An fara gabatar da shirin ne da Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina a gidan talbijin, an kuma bi shi har Mairuwa a Funtuwa. Ba a bar shi ba lokacin da shirin ya koma daji (Mararrabar Jos); nan ma sai da ya ba je basirar shi. 
 
Shata ya gabatar da waƙoƙin da su ka haɗa da ‘Tumbuleƙe Ɗan Hajiya’, ‘Ka Ga Rawar Tumbuleƙe’,  ‘Hajjo Ta Binta Ƙasaitatta’, :Da Akwai Daɗi Zaman Ƙauye’; har shi kan shi ‘Gidan Kashe Ahun’ bai ƙyale shi ba. Ya baje kolin hikima, fasaha, azanci, basira, da kwarjinin waƙoƙin sa fiye da kima. 
 
Bayanai a nan ba za su gamsar da mai karatu ba sai ya gane wa idon sa shirin a faifan bidiyo. 
 
An gabatar da shirin a garuwa da su ka haɗa da Kaduna, Mararrabar Jos, Zariya, Funtuwa, Katsina, da sauran su. 
 
Bayan gabatar da shirin na watanni uku, sai aka ba masu kallo damar jin ra’ayin su na ci gaba da shirin ko akasin haka. Mutane masu kallo su ka aminta da haka. Shi kuma gidan talbijin ɗin ya shiga neman masu ɗaukar nauyin shirin. Alhaji Sani Marshall Kano (mai kamfanin Ƙaura Biscuits da Macaroni), Alhaji Muhammadu Adamu Ɗankabo,  masu kamfanin jirage na Harka Airline, na daga cikin waɗanda su ka ɗauki nauyin shirin har ya yi wannan tsawancin rai. 
Alhaji Mamman Shata a wurin ɗaukar shirin ‘Gidan Kashe Ahu’ a cikin 1986
Mawaƙa da makaɗa da su ka samu damar shiga cikin wannan shirin sun haɗa da Binta Zabiya, Haruna Musawa, Ibrahim Na-Habu, Barmani Choge, Haruna Uji, Hussaini Jikan Boka, Aliyu Mai Kukuma Sokoto, Garba Super, Abdu Karakara, Shehu Katsina, da sauran su. 
 
Baƙin da ake gayyata da su ka shahara sun haɗa da Malam Korau, Inunu Mai Dankalin Turawa, Mamman Shu’aibu Gadar Gayan, Shehu Liberty Soba, Salisu Mai Ƙaraurawa,  Lifidan Zazzau, Ladi Mai Fura, da sauran su. 
 
Waɗanda su ka bada umarni wajen gudanar da shirin a lokuta mabambanta sun haɗa da Garba Yakubu, Ibrahim Ɓoyi, Aminu Baba Ahmad, Umaru Soba, Tafida Yola, Yakubu Wukari, Isah Mayo Balwa Yola, da sauran su. 
An fi ɗaukar shirin da safe inda ake amfani da motar ‘Outside Broadcasting Van’ (O.B. Van) domin naɗar shi a faifai kafin a je a yaɗa shi ta akwatin talbijin. 
Hajiya Barmani Choge na wasa a ‘Gidan Kashe Ahu’
Godiya ta musamman ga Shafi’i Zayyad (Baban Abba), Alhaji Bello Sule (tsohon Babban Daraktan Mulki a hedikwatar NTA da ke Abuja, Alhaji Abdul Ibrahim (tsohon mai ɗaukar ma shirin hoto kuma tsohon Daraktan Shirye-Shirye a NTA Katsina), da Alhaji Sani Gwarzo (Tumbuleƙe) wajen haɗa wannan bayani. 
 
Kabir Umar Saulawa P. R.O. manazarci ne da ke Katsina.
GSM: 07034610481

Loading

Previous Post

Bikin Finafinai na Kaduna ya kankama ta hanyar intanet

Next Post

Hukumar Naƙasassu: Na cika alƙawari, inji Minista Sadiya

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Hukumar Naƙasassu: Na cika alƙawari, inji Minista Sadiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!