• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sadiya Farouq ta yi tir da hare-haren da aka kai a Borno da Adamawa

by DAGA WAKILIN MU
December 28, 2020
in Nijeriya
0
Sadiya Farouq ta yi tir da hare-haren da aka kai a Borno da Adamawa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa,  Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi Allah-wadai da kashe-kashen rayuka da lalata dukiyoyi da aka yi a kudancin Jihar Borno da kuma Jihar Adamawa.


A cikin wata sanarwa da Babban Sakatare na ma’aikatar,  Bashir Nura Alkali, ya rattaba wa hannu, an ruwaito cewar ministar ta girgiza matuƙa da labarin da ta ji na hare-haren ta’addancin da aka kai a ƙauyen Pemi da ke Ƙaramar Hukumar Chibok da wasu ƙauyuka huɗu da ke Ƙaramar Hukumar Hawul a kudancin Borno da kuma garin Garkida da ke Jihar Adamawa.


Ta bayyana hare-haren da sunan marasa tausayi kuma na rashin imani.


Ta ce, “A gaskiya abin baƙin ciki ne a ce an yi waɗannan hare-haren ta’addancin a daidai lokacin da ya kamata a ce mutane su na jin daɗin hutun Kirsimeti tare da masoyan su.


Ta ce, “Ina miƙa jaje na ga gwamnati da jama’ar Jihar Borno musamman iyalan waɗanda wannan abin baƙin cikin ya shafa.”


Ministar ta nanata cewar Gwamnatin Tarayya ta yi tir da hare-haren, kuma ta jinjina wa hukumomi daban-daban da kuma Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ba tare da ɓata lokaci ba ya  kai ziyara a ƙauyukan da abin ya shafa tare da bada umarnin a tsaurara matakan tsaro a yankunan.


Hajiya Sadiya ta bayyana cewar ana nan ana shirye-shirye domin a kai kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa don a rage masu raɗaɗin hare-haren da aka kai masu.


Rahotanni dai sun bayyana cewa a ranar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020, wato ana gobe Kirsimeti, ‘yan Boko Haram sun kai hari a garin Garkida da ke Jihar Adamawa inda su ka kashe mutum biyar sannan su ka banka wa motoci da gidaje wuta, su ka ƙone su.


A Pemi da ke Jihar Borno ma, a wannan ranar, ‘yan ta’addar sun kashe mutum biyar tare da lalata majami’u da makarantu da gidaje. 


Shugabannin siyasa na yankin tare da sauran masu sa ido sun yi tir da hare-haren.

Loading

Tags: fimmagazineHajiya Sadiya Umar Farouq
Previous Post

Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20

Next Post

Matasa ku gane ba dare ɗaya ake yin arziki ba – Abdulsalam Musa, jarumi a ‘Kwana Casa’in’

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Matasa ku gane ba dare ɗaya ake yin arziki ba – Abdulsalam Musa, jarumi a ‘Kwana Casa’in’

Matasa ku gane ba dare ɗaya ake yin arziki ba - Abdulsalam Musa, jarumi a 'Kwana Casa'in'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!