FITACCEN jarumin Kannywood kuma mawaƙi Adam A. Zango ya shirya wa ‘yar sa ta fari, Murjanatu, bikin taya ta murnar cika shekara huɗu da haihuwa.
An yi bikin a yau Litinin, 1 ga Fabrairu, 2021 a gidan Zango da ke Kaduna.
A jiya Lahadi, 31 ga Janairu ne Murjanatu, wadda su ke kira da Hajiya, ta cika shekara huɗun da haihuwa.
A bikin, mahaifin ta da matar mahaifin ta Safiya Chalawa, da ‘yan’uwan ta da abokan sana’ ar mahaifin ta da masoyan sa sun taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar, musamman a shafukan su na Instagram.
An ɗauki Murjanatu kyawawan hotuna tare da ‘yan’uwan ta da matar mahaifin ta da ƙanen mahaifin, wato Rabi’u A. Zango.
Hotunan su na nuni da irin murna da farin ciki da iyalan Zango su ke ciki game da wannan rana.

A saƙon taya ‘yar sa murna da ya tura a Instagram tare da hotunan ta, wanda mujallar Fim ta fassaro daga Turanci, Adam A. Zango ya ce: “Allah sa bikin zagayowar ranar haihuwar ki na 4 ya fi na 3 kasancewa abin farin ciki. Ko za ki ci gaba da ba mu irin wannan kyakkyawan murmushin naki, a ko yaushe da kuma har abada?”
A saƙo na biyu da ya tura, shi ma tare da hotunan iyalin sa, jarumin ya ce: “Iyalai na su ne rayuwa ta, sannan komai zai biyo bayan su ne in ana maganar abin da ya fi muhimmanci a gare ni.”
Mujallar Fim ta lissafa cewa sama da mutum ɗari bakwai su ka tura saƙon taya murna a ƙasan hotunan sannan sama da mutum dubu goma sha biyar su ka so saƙonnin nasa. Bayan haka, wasu sun kwafi hotunan sun ƙara turawa a nasu shafukan don taya Murjanatu murna.
Ita dai Murjanatu Adam A. Zango, ita ce ɗiya mace ta farko da Adamu ya haifa, kuma ita ce ta biyar a cikin ‘ya’yan sa.
Ita ce wadda tsohuwar matar sa da ya auro daga ƙasar Kamaru mai suna Ummukhulsum ta haifa masa.
An haifi Murjanatu a ranar Talata, 31 ga Janairu, 2017 a Asibitin 44 na sojoji da ke Kaduna. An yi bikin suna na kece raini a lokacin haihuwar ta, kasancewar ita ce ‘yar sa mace ta farko.
A halin yanzu dai jarumin kuma mawaƙi ya na da ‘ya’ya shida da matar aure ɗaya. ‘Ya’yan su ne Haidar, Khalifa, Amir, Sultan, Murjanatu, sai ‘yar’autar su Mubeena, wadda tsohuwar matar sa A’isha ta haifa masa.
A yanzu matar sa Safiya ce ake jira ta samu rabo a gidan.
Allah ya raya su cikin addinin Musulunci, amin.

