GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara sa hannu kan irin finafinan da ake shiryawa ana yaɗa su ta hanyar intanet ba tare da an tace su ba.
Irin waɗannan finafinan, har ma da waƙoƙi, ana kiran su da Turanci ‘Over the Top content’ (OTT a taƙaice).
Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (National Film and Video Censors Board, NFVCB), Alhaji Adedayo Thomas, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a otal ɗin KAP Hub da ke Ikeja a Legas.
Ya ƙara da cewa hukumar ta na aiki ba ji ba gani wajen ganin ta riƙa sa ido kan ƙaruwar ayyukan da ake shiryawa ana yaɗa su ba tare da an tace su an saka su a rukunnan kallo da su ka dace ba.
Ya ce hukumar za ta fito da tsarin hukunta masu karya dokar hakan.
A cewar sa, “Cigaban da ake samu wajen inganci da yanayin finafinan da ake shiryawa tare da isar da su ga jama’a ya inganta cuɗanyar da jama’a ke yi sannan ya ƙarfafa yaƙi da ake yi da masu satar basira tare da haɓaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma faɗaɗa kasuwanci na abaubuwan da ake ƙirƙira.
“Wannan shi ya sanya Hukumar Finafinai ta ɗauki batun saka hannu kan ababen OTT da matuƙar muhimmanci.”
Haka kuma babban daraktan ya bayyana cewa hukumar ta tace finafinai ta na nan ta na shirin gudanar da wani babban taro inda za a tattauna kan irin waɗannan finafinan da ake ɗorawa a intanet.
Yayin da ya ke bayyana manufar taron, wanda ya ce na kwana biyu ne, Thomas ya ce za a shirya taron ne don a samar da kyakkyawan yanayi ga masu shirya irin waɗannan finafinan.
Ya ce, “Za a yi taro na kwana biyu kan hajar ƙirƙira ta zamani da ake shiryawa a Nijeriya don a tattauna al’amuran da za su bada dama a inganta harkar kasuwanci a masana’antar.”

Mujallar Fim ta fahimci cewa za a gayyato kamfanonin yaɗa finafinai a kafofin sadarwa na zamani zuwa taron, ciki har da Netflix, Amazon Prime, Showmax, Telcos da ma wasu.
Ana sa ran cewa a taron za a yi maganganu kan duk wani abu da ake gani ko ake tunani a kan sa dangane da yadda za a haɓaka harkar shirya finafinai a Nijeriya.