TSOHUWAR fitacciyar jarumar Kannywood, Fati Ladan, ta bayyana wa matan Nijeriya sirrin zama mai ɗorewa da mazajen auren su.
Fati ta yi maganar ne a wata hirar musamman da ta yi da mujallar dangane da cikar ta shekara takwas cur a gidan aure.
Idan kun tuna, kwanaki kaɗan da su ka gabata mun kawo maku labari da kuma hotunan cika shekara takwas da auren tauraruwar ta Kannywood a ɗakin mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum).
Fati da Yerima dai su na da ‘ya ɗaya a tsakanin su, kuma su na zaune ne a garin Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu.

Wakilin mujallar Fim ya samu tattaunawa da Hajiya Fatin game da wannan babbar nasara da ta samu a rayuwar ta, duba da yadda ake ce-ce-ku-cen cewa matan fim ba su zaman aure.
Da farko wakilin namu ya tambayi Hajiya Fati Ladan abin da za ta ce game da cikar ta shekara takwas da aure. Sai ta amsa da cewa, “Ina yi wa Allah (s.w.t.) godiya da ya nuna mana wannan lokaci, domin wannan ba ƙaramin abu ba ne, don an ce ko kwana ɗaya ka gani ka gode wa Allah, ballantana wannan shekaru.
“Ina yi wa Allah godiya da Allah ya tabbatar min da wannan zama namu da maigida na, kuma ina farin ciki sosai.
“Sannan kuma ina yi wa ‘yan baya waɗanda su ka yi da waɗanda ba su yi ba Allah ya tabbatar da su a gidan mazajen su kamar ni yadda na ke. Waɗanda ba su yi ba kuma Allah ya ba su nagari. Wannan shi ne kawai fata na.”
Ana yawan cewa ‘yan fim mata ba su zaman aure, sai kuma ga shi ita ta samu wannan gagarumar nasara a rayuwar ta. Shin wane mataki ta ɗauka don ganin hakan ta tabbata?
Sai ta ce, “Kamar a ce ‘yan fim ba su zaman aure, wannan ba adalci ba ne. Allah subhanahu wa ta’ala da ya yi aure, kuma ya yi saki, to abu ne wanda ba wai sabon abu ba ne; kamar rayuwa ce da mutuwa: yadda ka tabbatar da cewa yadda ka rayu, wata rana za ka mutu, ka zama labari. To haka aure ma rai gare shi, duk lokacin da wa’adin shi ya cika dole zai mutu.
“In ka duba, yanzu matan da ba su da aure – zawarawa kenan – waɗanda ba ‘yan fim ba sun fi yawa a kan ‘yan fim ɗin. Tunda ‘yan fim ɗin dududu guda nawa ne, ƙalilan ne.
“Amma mu da yake an san mu dole wance, wane abu na faruwa da su sai a maida shi labari. Amma yanzu zawarawa nawa ne ke yawo a cikin unguwa? Kai, a unguwa ba ka wuce gida ɗaya, biyu ba ka samu bazawara ba, kuma kowa ya sani wannan magana haka ta ke.
“Saboda haka ba wai ‘yan fim ne ba su zaman aure ba, kowane aure ya na da wa’adin sa, komai na rayuwa akwai muƙaddari.

“Akwai wanda in ka aura mutuwa ce kawai za ta raba ka da shi, akwai wadda za ka ji an ce auren ta goma, kuma ba wai don ba ta son auren ba ne, in ba ta son ta zauna da ta yi ɗaya, ta yi biyu, ta yi na uku za ta haƙura. Amma sai ta yi ta yi, har a fara ƙirgawa ta yi aure goma; ba wai don ba ta so ba ne, ta na ta gwadawa ne ta gani, har Allah ya sa ta dace.
“Don haka babu macen duniya da ba ta so ta zauna a gidan mijin ta, duk wadda auren ta ya mutu, muƙaddari ne; tun ran gini, tun ran zane, sai Allah ya sa auren nan ya mutu!
“Allah ya dauwamar da duk wata mace da ke gidan miji a gidan mijin ta tare da farin ciki da kwanciyar hankali a gidan mazajen mu ga baki ɗayan mu.”
Shin Fati Ladan ta taɓa samun wata daga cikin ‘yan fim ko kuma wata daga waje don ta ba su shawara game da zaman aure?
Ta ce, “Ƙwarai kuwa, akwai su sosai ma. Akwai ƙawaye na waɗanda ba su yi auren ba da waɗanda ma su ka yi auren, su kan tambaye ni menene sirri na tsakani na da miji na, sai in ce masu wallahi in ban da so da ƙauna da ke tsakani na da shi babu wani abu. Abu na biyu kuma shi ne haƙuri; duk yadda namiji ke son ka, in dai ba ka da haƙuri babu yadda za a yi ka zauna da shi, shi ma babu yadda za a yi ya iya zama da kai.
“A zamantakewar aure tsakanin mata da miji akwai matakin da kowa ya ke takawa, ko da namjin bai da haƙuri, in dai macen ta na da haƙuri ta na kai zuciyar ta nesa, yi na yi, bari na bari, sai ki ga komai ya zo miki da sauƙi.
“Babu inda ba a samun matsala. Kowane abu na rayuwa ya na da ƙalubalen sa. Ni lokacin da za a yi min aure, iyaye na cewa a yi haƙuri, kowa ya zo sai ya ce min a dai yi haƙuri. Sai na ke cewa wai ya za a yi ai ta cewa in yi haƙuri, bayan kuma auren soyayya na yi ba auren ƙiyayya na yi ba? Ya za a yi a rinƙa ce min in yi haƙuri?
“Sai daga baya yanzu na gane cewa lallai ga ‘point’ ɗin su, saboda duk yadda mijin ka ya ke son ka ka ke son shi, wallahi zaman taren nan ya wuce wasa; kwana ɗaya, biyu, uku, har a fara ƙirga shekaru babu yadda za a yi ka ce ba ka samun matsala da mijin ka, ko ma menene sai ka yi haƙuri.
“Don haka in ka yi haƙuri sai ka ci ribar zaman auren ka, amma kuma in ba ka yi haƙuri ba sai ka ga abubuwa sun zo maka ba yadda ka ke so ba. To haƙuri shi ne ‘key’, shi ne komai.”
Mujallar Fim ta waiwayi tsohuwar jarumar dangane da wata gidauniyar agaji da ta ƙaddamar a shekarar da gabata, wadda za ta riƙa taimaka wa marasa ƙarfi, marayu da sauran su. Sai Fati ta ce, “Ta na nan har yanzu, kuma ta ci gaba da aiki, sai dai da yake ni na fi so in zan yi taimako na ban fiye so a san ni na yi ba, zan iya aika manaja na in ce ya yi, in kuma akwai buƙatar a yi a wani wurin ma shi zai zo ya same ni ya ce kin ji, kin ji akwai matsala a wuri kaza, akwai inda ake neman taimako, sai in ce ka je a yi, in ka yi kamar ni na yi ya wadatar.

“Saboda yadda sadakar ya kasance na yanayin yanzu na wannan zamanin da mu ke ciki, za ka ga komai an maida shi soshiyal midiya; da zarar ka yi abu sai ka ga ana yaɗawa. A addinance ya na da kyau idan ka yin ka ɓoye inji Ubangiji, shi ya sa mu ke kwatanta hakan.
“Mu ba mu ce ‘yan goma ba ne, duk ɗan’adam ɗan tara ne. Wani ya na da lalura ya na so ya kawo kukan sa ya ce maka ka taimaka masa, amma ya na gudun kada ka ɗauke shi a kyamara ka yaɗa; kamar ka tona masa asiri ne, ya gwammace ya zauna da wannan laluran nashi ko kuma ya je ya bi wata hanya da ba ta kamata ba.
“To ka ga sirri ya na kyau ko a addinance. Ya na da kyau in za ka yi wa mutum abu ka rufa masa asiri. In mutum ya buƙaci ka bayyana shi za ka bayyana shi, amma idan mutum ya buƙaci ka sirrinta alkairin da ke tsakanin ka da shi, saboda haka mu na amfani da wannan. Ba mu cika bayyana mutumin da ba ya son ya san halin da ya ke ciki ba.”
Ko Fati Ladan ta na soshiyal midiya kuwa? Fati ta amsa da cewa, “Gaskiya ni ba na Instagram. Abin da na ke yi a soshiyal midiya shi ne WhatsApp. Miji na ya hana ni dukkan wani abu da ya shafi soshiyal midiya kamar su Instagram, Facebook da TikTok. Miji na ya hana ni.
“Abin da ya yarje min kawai in yi shi ne WhatsApp, shi kaɗai na ke yi gaskiya.”
Mecece shawarar ta ga abokan sana’ar ta? Amsa: “Shawarar dai ba ta wuce duk yarinyar da ke cikin harkar nan in Allah ya kawo mata miji, kuma hankalin ya kwanta da shi ta na son shi, ni shawara ta gare ta ta yi haƙuri ta yi aure. Saboda shi wannan ‘stardom’ ɗin ya na da lokaci, ko kin tafi ko ba ki tafi ba, ki na nan za ki ga an kawo wasu da su ka zo su ka danne ki.

“Don haka ni ina ganin yin auren ya fi miki zaman a haka, saboda za ki zo ki kai lokacin da ki na neman auren ma ba ki samu ba, amma idan ki ka yi amfani da damar da ki ka samu a wannan sharafin na ki sai ki ga kin samu miji da za ki rinƙa alhamdu lillahi, kuma kowa na yi miki fatan alheri. Shawara na kenan.
“Da waɗanda ba su yi auren ba da waɗanda su ka yi su ka fito, don Allah duk wacce ta samu miji, in har ta tabbatar da ta na son shi, ta yi haƙuri ta yi auren nan. Shi ne babban rufin asirin kowace mace ta duniyar nan.”