• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministar Jinƙai ta jajanta kan waɗanda rugujewar bene ya ritsa da su a Legas

by DAGA ALI KANO
May 2, 2022
in Nijeriya
0
Ma'aikatan agaji su na aikin ceton rai a inda benen ya rushe a Legas

Ma'aikatan agaji su na aikin ceton rai a inda benen ya rushe a Legas

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta jajanta wa gwamnatin Jihar Legas da  iyalan waɗanda su ka rasu a wani haɗarin rugujewar bene a Legas.

Rahotanni sun ce benen mai hawa 3, wanda ya ruguje a daren Lahadin makon jiya a unguwar Ebute-Metta, da ma can hukuma ta yi masa alamar za ta rushe shi saboda ta ga alamun ya susuce, to amma masu zama a cikin sa su ka ƙi tashi.

Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun garzaya wajen ginin bayan ya rushe don aikin ceton rai tare da haɗin gwiwar Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Jihar Legas da Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (SEMA) da kuma ‘yan sanda. Sun yi ƙoƙarin ceto mutum 23 yayin da mutum 8 su ka mutu a cikin ginin.

Ma’aikatan agajin sun ci gaba da aikin ceto da bincike don tserar da waɗanda su ka maƙale a cikin ginin.

Jami’ai su na ci gaba da aikin ceto a Ebute-Metta, Legas

A cikin wata sanarwa ga manema labarai da ta fitar, mai taimaka wa ministar kan yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze, ta ce Hajiya Sadiya ba ta ji daɗin yawaitar bala’o’i da za a iya yi wa rigakafi irin wannan a ƙasar nan ba, kuma ta yi kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su yi aiki tuƙuru don rage aukuwar bala’o’in.

Ministar ta ce: “Wannan bikin Ƙaramar Sallah ne maras daɗi saboda rugujewar bene mai hawa uku a Legas. Ina jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Legas saboda wannan abin baƙin ciki.

“Ina yin addu’a ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukan su  a wannan gini da ya rushe da waɗanda aka ceto da ran su tare da jin raunuka a wannan lamari.

“Da jin labarin faruwar rugujewar ginin a Titin Ibadan a Ebute-Metta, Legas, mun umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su garzaya zuwa wajen tare da sauran hukumomin agaji da su ka dace. Abin baƙin ciki, mutane da dama sun maƙale a cikin ginin kuma an rasa rayuka da dama.

“Haka kuma ya na da muhimmanci cewa waɗanda haƙƙi ya rataya a wuyan su na tabbatar da ana gina ingantattun gine-gine a ƙasar nan su tabbatar da cewa an riƙa bin ƙa’idojin yin gini mai nagarta don kauce wa faruwar waɗannan abubuwan na baƙin ciki.”

Loading

Tags: agajiEid el-FitrHukumar Kwana-kwanaƙa'idojin giniLagosLegasMa'aikatar Harkokin Jinƙai.Ministry of Humanitarian AffairsNEMANneka Ikem Anibezerugujewar beneSadiya Umar Farouq
Previous Post

Gargaɗin Sa’idu Gwanja ga Rarara: Kyautar da ka ke yi cin mutunci ne, don haka kada ka ƙara saka ni a ciki

Next Post

Cewar Gidan Dabino: MOPPAN reshen Kano za ta yi fim zakaran gwajin dafi wanda zai shiga duniya

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Ado Ahmad Gidan Dabino (MON)

Cewar Gidan Dabino: MOPPAN reshen Kano za ta yi fim zakaran gwajin dafi wanda zai shiga duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!