A RANAR Laraba, 27 ga Afrilu, 2022 ne aka rantsar da fitaccen marubuci, jarumi kuma furodusa, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, a matsayin Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano. Kamar yadda mu ka ba ku labari, zai jagoranci sabon kwamitin gudanarwar reshen ƙungiyar mai wakilai 12.
Gidan Dabino, wanda ake yi wa laƙabi da Malam Adamu Gwamnan Jihar Alfawa a cikin shirin fim ɗin ‘Kwana Casa’in’ mai dogon zango da tashar talbijin ta Arewa24 ke nunawa, ya ɗare kujerar ne a bisa cancanta. Ya na ɗaya daga cikin mutanen da su ka assasa Kannywood, don haka ya san ta ciki da bai.
Mujallar Fim ta zanta da sabon shugaban domin jin inda ya sa gaba wajen ƙoƙarin kawo wa masana’antar Kannywood cigaba, kamar haka:
FIM: ‘Yallaɓai, ya aka yi aka zaɓe ka sabon shugaban MOPPAN na Jihar Kano?
GIDAN DABINO: Ba zaɓe aka yi ba kamar yadda aka saba. Kundin tsarin mulki (na MOPPAN) ya bada dama a yi sasanci, ko ‘consensus’ inji Turawa. To, gaskiya waɗanda aka kafa a kwamitin haka su ka yi; in an zo irin wannan ‘consensus’ ɗin ta yiwu kai ka sayi fom ɗin P.R.O., wannan ya sayi na shugaba, wancan ya sayi na sakatare, sai a yi ‘adjusting’ a ce wane ya matsa, wane ya hau. A haka dai ko mutum biyu sun haɗu a wuri ɗaya a sasanta a ce wane ya bar wa wane. Haka dai su ka yi su ka aiwatar da wannan abu, ba wai an zo an tara mutane ne an jefa ƙuri’a ba ne.
FIM: Su wanene ‘yan kwamitin zaɓen?
GIDAN DABINO: Kwamitin riƙo ne. Umar Gombe shi ne shugaba, da sauran ‘yan tawagar sa; ba zan iya sanin gaskiya su waye da waye ba. Na dai san akwai Sulaiman Edita a ciki.
FIM: Ganin cewa an zaɓi jajirtattu, kuma waɗanda su ka san masana’antar, wane irin ƙoƙari za ku yi don ganin cewa kun dawo da martabar harkar fim a yanzu, musamman ganin yadda ta taɓarɓare?
GIDAN DABINO: Na farko, kamar yadda na taɓa faɗi cewa an zo an same ni, kafin ma a zo maganar tsayawa takara, akwai wasu yara, Mustapha da Muhammad da Abdullahi Nalapo, su ne su ka yi ta zuwa wuri na su na cewa in zo in yi takara, ina ba zan yi ba. Sun zo ya fi sau goma sha biyu, na ce ba zan yi ba, saboda na san matsaloli da rigingimun da ake fama da su. Kuma na yi shugabancin ANA, na san irin wahalar da na sha.

A ƙarshe dai sai su ka kai ƙara ta wurin Farfesa Abdalla Uba Adamu, su ka ce Malam ga shi ga shi. Kawai sai Farfesa ya kira ni, tunda ofis ɗin mu ɗaya, ya kira ni, na sauka ƙasa. Ya ce, “Yara sun kawo ƙarar ka, sun zo sun ta yin maganar kaza-kaza, ka ce ba za ka yi ba.”
Sai na ce, “In dai maganar shugabanci ne, ba zan yi ba.”
Sai Abdalla ya ce, “Ai ni nan da na kira ka ba shawara na ke ba ka ba, umarni na ke ba ka. Je ka yi!”
Sai na yi shiru. Can sai na ce, “Gaskiya ni ba zan kashe ko kwabo na wurin sayen fom ba.”
Sai ya ce, “Nawa ne?”
Sai aka ce N50,000.
Sai ya ce, “Kawo lambar asusun ka na banki.”
Ina badawa, ba a yi minti biyar ba sai ga N50,000. Sai na ce, “Ga N50,000 sun shigo.”
Sai ya ce, “Ka je ka sayi fom.”
Ya na faɗin haka, sai na ce, “Allah ya sa in an yi zaɓen in faɗi!”
Sai wurin gaba ɗaya su ka fara, “Ciyaman, ya haka?” Masu dariya su na yi, masu mamaki su na yi.
Na ce, “Ai na ce maku ga ra’ayi na, amma tunda an matsa min shi kenan, zan je in yi.”
Ban san dalilin da ya sa ake so sai na zo na yi ɗin ba, amma shi Abdalla ya faɗi dalilan sa da ya sa ya ke son ni ɗin na yi. To ka ji yadda aka yi.
To, daga baya aka yi sabon zubi. Kuma mu na da tsare-tsare wanda in Allah ya yarda bayan uku ga Sallar nan za mu je mu zauna mu fara tsarawa daki-daki. Shi ya sa ko a jawabi na ban yi alƙawarin cewa za mu yi kaza, za mu yi kaza ba, amma dai in mun yi za mu zo mu faɗi. Domin ayyanawar a gabanin ƙaddamar da kai ko gabatar da kai ko rantsar da kai alƙawari ne wanda in ba ka cika ba an samu damar da za a yaƙe ka ko a faɗa maka ba-daɗi, wanda shi ne ya ke damun ‘yan siyasan mu na Nijeriya: a ɗau alƙawari, ya zo ya gagara cikawa. Da za a riƙa cewa, “Zan yi iya abin da ya sauwaƙa gwargwadon abin da Allah ya yi in na zo in faɗi,” ka ga mutum ma ba zai kama ka da laifin ka yi masa alƙawari ba.
Kuma shi da kan sa Farfesa Abdalla ya ba mu wani kundi na wani bincike da British Council ta yi tun 2003, wanda ba a fito da shi ba, a kan yadda za a yi a gyara Kannywood. Wannan ma zai taimaka mana in-sha Allahu da namu tunanin da na waɗancan Turawan da su ka yi bincike da sauran shawarwari da za mu yi amfani da su daga ‘ya’yan ƙungiya, iyayen ƙungiya, ‘elders’, da sauran su. In-sha Allahu za mu yi iya yin mu, mu fitar da jaki daga duma.
Kai ma yanzu ba zan yi maka alƙawarin cewa ga kaza ga kaza da kaza da za mu yi ba. Za mu yi iya bakin yin mu, da taimakon Allah. Kada Allah ya bar mu da iyawar mu, mu ga an samu sassauci da gyara gwargwadon yadda za mu iya, don ba za mu iya gyarawa gaba ɗaya ba.
FIM: ‘Yallaɓai, akwai ‘yan fim da ke ɓata wa masana’antar suna a soshiyal midiya. Wane irin ƙoƙari za ku yi don ganin an daƙile faruwar ire-iren waɗannan abubuwa?
GIDAN DABINO: Ita matsalar soshiyal midiya, abu ne a sama: ba ka ma san gidan wani ba, ba ka san sunan wani ba, ba ka ma san a duniyar da ya ke ba. Wani ya na Chana, in ka bi shi ba za ma ka gane inda ya ke ba, ya ma riƙa sako abin da ba za ka iya ganewa ba. Ba mu da ikon hana saka abubuwa a intanet saboda mu ba hukumar hana wannan abin ba ne. Abu ɗaya mu za mu yi: mu haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin mu da sauran ƙungiyoyin da su ke jagoranci; ba MOPPAN kawai ba, akwai ƙungiyar Arewa, domin idan ƙungiya ta ce za ta yi wannan ita kaɗai da wahala ta samu nasara. Domin wannan sai ya ce, “Ni ba ɗan ka ba ne, don haka ba za ka hukunta ni ba,” amma idan aka ce MOPPAN ta zo, Arewa ta zo, in ma akwai wata sai a haɗu, abu kaza ya na damun mu, kaza ya na damun mu, ya za mu yi mu yi ƙoƙari mutanen mu da mu ka san mun san su, sun samu kuma ko da wa’azi ko da kira ko da shawarwari su daina irin wannan abu da zai zubar wa da mutane mutunci? In mu ka yi wannan, ina ganin Allah zai taimake mu.
Amma ba za mu iya cewa za mu toshe maka kafar sadarwar ka ba, ba za mu ce za mu hana ɗora wani abu ba, sai dai mu ba ka shawara, mu ce ka bar kaza. In ka ce ‘independent’ ka ke fa? Ba za a hana ka ka je inda ka ke so ba.
Saboda haka ina ga ba korar ne muhimmiya ba, illa a yi kira da bada shawarwari da nuna wa mutane addinin su da al’adar su ta na da muhimmanci da kuma me za ka bar wa ‘yan baya; ai za ka yi ‘ya’ya ko za ka yi jikoki ko ka na da ‘yan’uwa, da sauran su; idan ka yi abu mara kyau, zai iya dawowa baya. To idan aka bi cikin lalama da kaza da kaza, akwai abin da za ka yi a yi maka hukunci a fili ƙarara wanda ka yi wa ƙungiya, ka yi wa wane kaza, sai a yi maka hukunci. Amma in ka shiga intanet ka saka wani abu, za mu kira ka mu ce bai kamata ba, in kuma ɗan ƙungiya kaza ne to mu haɗa kai mu ga an sallame shi, an kore shi, domin an sha yi, wata ƙungiya ta yi kora, wata ta ce ba ta goyi baya ba.
Ga duk wanda ya san yadda aka yi rigimar Rahama Sadau, MOPPAN ta kore ta, Hukumar Tace Finafinai sun dawo da ita. To ka ga ita kan ta Hukumar Tace Finafai ɗin sai mun haɗa kai da ita saboda mu yarda da cewa idan za mu kori mutum gaba ɗaya za mu kore shi, wani ba zai dawo da shi ba. Amma matuƙar za ka kori wani kai kaɗai, sai ya ce ya bar ƙungiyar ka ya koma wata. Ka ga ba zai yiwu ba. Dole sai mun haɗu mun fahimci juna, mun san aikin da za mu yi don Allah za mu yi, don mu taimaki masana’anta, harshen mu da addinin mu.
FIM: Wane irin hoɓɓasa za ku yi don ganin cewa an farfaɗo da harkar kasuwancin finafinai?
GIDAN DABINO: A jawabi na, na faɗa na ce kamata ya yi mu riƙa yin finafinai na duniya, ba na Kano ba ko na Arewa ko na Bahaushe kawai ba. Na bada misali, na ce mun shiga gasar finafinai a Kenya, finafinai dubu ɗaya da ɗari takwas da wani abu su ka shiga; an shigo daga Amerika, daga Rasha, daga ina ne, ƙasashe sama da hamsin sun shiga, kuma ‘Juyin Sarauta’ shi kaɗai ne daga cikin finafinan Kannywood wanda ya shiga, kuma ya fito daga cikin finafinai ɗari da za a nuna. An watsar da dubu ɗaya da ɗari bakwai, amma ya fito a cikin ɗari. Sannan ya zo ya samu ‘nomination’ na ‘best production design’. Sai na ce idan har za mu yi ‘Juyin Sarauta’ ya buga da finafinan Amerika da Rasha da sauran su, ashe har sauran gasa da ake yi na duniya za a iya zuwa.
In-sha Allahu za mu bi tsari na irin finafinan da ake so, kuma ya ake so su zama. In ma bada bita ne za mu yi wa mutanen mu, sai mu yi. Ai ga irin su Netflix da sauran su da za ka ga su na karɓar finafinai da kuɗaɗe masu yawa, kuma mutanen kudancin Nijeriya su na yi ana saka nasu. Mu me ya sa ba a saka namu? Sannan kuma ɗan Kudu zai shigo arewacin Nijeriya ya zo ya shirya fim, ya ɗebe mu ya saka mu, kuma a je a nuna fim ɗin a can. Me ya sa mu ba za mu yi ba? Ka ga lallai ya kamata mu zauna mu yi aiki tuƙuru tsakanin mu da masu aikace-aikacen finafinai daban-daban da horo da sauran su. Wannan in Allah ya yarda za mu yi iya yin mu. Kuma ka san kai ka na naka ne, Allah ya na nashi; idan har ka samu ka yi abu mai kyau ƙwara ɗaya wanda zai sama maka kasuwa ta duniya, da an yi ɗaya, biyu, uku a Kannywood to in Allah ya yarda za ka ga hanya ta buɗe.
Kuma ni na faɗa, ko a MOPPAN reshen Jihar Kano ne za mu yi fim zakaran gwajin dafi ƙwara ɗaya wanda zai shiga duniya. In dai Allah ya taimake mu mun samu kuɗin, to mu a ƙungiyance za mu yi shi mu bada misali. Mun je Kenya an yi. Sai ƙungiyar ta nemo kuɗin ta. In ma wani ne za mu nemo ya zuba jari sai a yi fim ɗin da zai shiga duniya, kuma a ce an kalla. Wannan shi ne fatan mu.
FIM: Wace hanya za ku bi don ganin kun ƙulla alaƙa da gwamnati ta hanyar Hukumar Tace Finafinai?
GIDAN DABINO: To, ka san tunda mu ‘yan Kano ne, kuma mu na cikin Kano, kuma gwamnatin Kano tamu ce, yanzu mu na sa ran za mu ziyarci duka masu ruwa da tsaki a gwamnatance, da malamai da ita kan ta Hukumar Tace Finafinai da Hisbah da sarakuna, duka za mu je mu ziyarce su a matsayin wannan sabon shugabanci. Mu na so su ba mu haɗin kai da goyon baya da shawarwari domin mu yi abu mai inganci. Don haka mu na fatan duk wata hanya da za mu bi don a zauna lafiya, a tafi tare a taimaki Jihar Kano, a taimaki masu sana’ar fim, a taimaki Arewa ma baki ɗaya.
Masana’antar tunda Kano ce cibiya, idan ta gyaru ko’ina ta gyaru, kuma MOPPAN ta jihar kamar ita ce ta fi kowa girma a sauran jihohi in ka cire ta ƙasa. In mun bada misalai da za su taimaka, in-sha Allahu sauran za su kwaikwaye mu. Sai dai kuma idan ka je wasu hukumomin in an zo maka da son zuciya sai ka ce ba za ka yarda ba; mun yi lokacin ina ciyaman na ANA, da na ce ba zan yi faɗa da Hukumar Tace Finafinai ba, amma daga ƙarshe sai da aka yi, saboda an zo da wani abu wanda ba ya cikin tsarin dokar, mu kuma mu ka ce ba za mu bi ba.
To ka ga in dai za a bi tsari, ba za a bi son rai ba, ko shugaban da aka saka zai sa son ran sa da son zuciyar sa, in aka ji ‘yan MOPPAN sun ɓalle sun sa zare ba abin mamaki ba ne, an taɓa yi.
FIM: Ya za a yi ku sauya akalar Kannywood don tafiya da zamani?
GIDAN DABINO: Yadda za mu sa ta tafi da zamani shi ne horon nan da bada ilimin nan. Ai mafi yawa ana yin sa ne cikin duhu, cikin rashin fahimtar wasu abubuwa. Kowa ya shigo shi darakta ne, kowa ya shigo shi kaza ne. Sai ka ji mutum ya na cewa, “Cut and action ne fa kawai, menene a ciki?”
Ka ga in aka ce “cut and action” ne, ba za a yi abin kirki ba kenan. Ka ga ba ka san ka yi ‘jump cut’, ba ka san ka yi kaza ba. Kowa a ba shi haƙƙin sa, in marubuci ne kai a ba ka haƙƙin ka na marubuci, in darakta ne kai a ba ka haƙƙin ka na darakta, in furodusa ne ma haka. Idan mu ka rarraba wannan aikin, kowa ya riƙe aikin sa, in-sha Allahu za mu zamanantar da masana’antar tamu, kuma za a riƙa tafiya da mu.
Mu na da labarai. Labaran da mu ke da su sun fi na wasu wuraren da dama. Ko a Kudu ba na jin su na da labarai kamar namu. Amma me ya sa ba mu yin su yadda ya kamata, ko ba mu saka kyamarar da ta kamata, sannan ba mu da kuɗin ma? Ka ga wannan ita ce matsala ta farko. Ana kashe naira miliyan ɗari zuwa sama, kai kuma ka na yin fim na naira miliyan ɗaya, biyu, uku, biyar. Wanda ya saka goma, ashirin ko talatin sai ai ta kallon sa, to ka ga ba za ka iya takara da waɗancan ba. Kyamarorin ma kan su hayar su ma ba za ka iya ba. Dole wani lokacin da ruwan ciki a kan ja na rijiya. Amma dai za mu yi iya yadda za mu yi. In ma ayyukan haɗin gwiwa ne za a riƙa yi, ai ana yin ‘collaboration’ da wasu, masu kamfanoni ne ko NGO ne ko kaza ne, ko kaza ne, duka dai bi’izinillahi Ta’ala, za mu yi dukkan abin da za mu yi mu ga an samar da irin waɗannan abubuwan.
FIM: Me za ku yi don ganin kun faɗaɗa kasuwancin finafinan Hausa kamar yadda ake sayarwa a Netflix, Northflix, gidajen sinima, gidajen talbijin da sauran su?
GIDAN DABINO: Yadda za mu yi, na farko mun san tsarin da su kafafen talbijin ɗin su ke sayen kayan mutane, amma wani lokacin za ka ga sayen babu daraja, sayen babu wata ƙima. Amma wani lokacin mu ne mu ke ci wa kan mu dunduniya da kan mu. Yanzu kamar African Magic da sauran su sun san yadda ake yi, an ce wasu daga cikin jaruman mu ne su ka je su ka soki abubuwa – ban tabbatar ba – amma an ce su ne su ka je su ka ce ai fim ɗin ma ana gama shi ne a titi, da sauran su.

Saboda haka in an zo sai a karya abu, a su raɓa-raɓa wani in ya kashe kuɗi da yawa, in zo ya kwatanta abin da ake sayarwa ka ga ba zai kai labari ba. Ka ga mu na ci wa kan mu dunduniya da kan mu. Kuma wasu su na ganin sun kai wani matsayi, ba su so wani ya kai wannan matsayin, sai su yi ta ƙoƙarin daƙile waɗannan masu tasowar don kar su kai. Sai su ce, “Idan fim babu wane kada ku karɓa,” su kuma sai su ce ba za su karɓa ba.
Su ma masu kamfanonin da su ke karɓar finafinai ya kamata ƙungiyoyin namu mu same su mu tattauna mu ga ya za a yi su taimaka don a gyara waɗannan matsalolin. Wannan shi ne. In ka tafi a ƙungiyance ya fi a tafi a ɗaiɗaiku.
FIM: Ta yaya za ku daƙile kwararowar sababbin jarumai babu ƙa’ida a masana’antar?
GIDAN DABINO: Akwai ‘guilds’ (ƙungiyoyi) da ake da su na daraktoci, masu ɗaukar hoto, ‘yan wasa… su ya kamata a saka wa idanu; iyayen ƙungiyar nasu na ƙasa da jiha a sa masu idanu: ya su ke tantancewar nan, ya su ke yin kaza, ya su ke yin kaza? Ba za ka ce za ka hana mutane shigowa ba, amma ka yi yadda za su shigo cikin tsafta, su san mutuncin masana’antar, su san darajar ta. Wani lokacin za a ce mutum sai ya kawo baban sa, maman sa ko wani shaƙiƙi. Sannan kuma a masana’antar sai an samu wanda zai zame maka ‘guarantor’. In za a ci gaba da irin wannan, ana matsawa, ana sa ido, ɓarkowar masu shigar za ta ragu, kuma za a samu tsafta a ciki.
Matsalar shi ne babu aikin masu son su na shigowa fiye da aikin. Jarumai su na ta shigowa, kuma ba a yin finafinan, sai ‘online’, shi ne za ka ga na YouTube da sauran su. Mafi yawancin jaruman yanzu, maza da matan, da an tambaye su wane fim ka yi ko ki ka yi, sai su ce waƙa. Duk sun zama jaruman waƙa! Ba za ka hana ba, kuma kowa da hanyar cin abincin sa. Mu ba mu zo don mu hana kowa cin abinci ba, amma kuma ba mu zo mu bari a shashance, a sakankance, a yi zaman ‘yan marina ba – kowa na kallon inda ya ga dama. Ya kamata mu kalli hanya ɗaya. Amma hakan ba zai yiwu ba sai mun haɗa kai a ƙungiyoyin mu. Misali, akwai MOPPAN a Kaduna, Zariya da sauran su. Ya zamanto cewa in mun kori mutum daga nan Kano, MOPPAN ta Kaduna ta amince mun kore shi, MOPPAN ta Legas ta yarda, ta Sokoto ta yarda. Idan mu ka yarda da wannan, za mu samu gyara.
Sannan idan Arewa ta kore shi, ta jiha ko ta ƙasa, to an kore shi a Arewa ko ta ina ne. In ma ba Kano ya ke ba, sai ya ce ya koma garin su, in dai ta Kano ta kore shi ta garin su ma ta kore shi, kada su yarda da shi. Wannan ita ce hanyar da za mu bi.
Kuma ba za mu yi hakan ba sai mun cire son zuciya da son mulki, mun cire cewa ni ne wane. In mu ka yi wannan, in Allah ya yarda za ka ga abin da zai faru.
FIM: A ƙarshe, wane kira za ka yi wa su membobin ka?
GIDAN DABINO: Abin da na ke so in yi kira ga su membobi na na MOPPAN na Jihar Kano, su ba mu goyon baya. Duk abin da mu ke so mu cimma nasara, matuƙar ba su ba mu goyon ba ba za mu cimma ba. Kuma rashin ba mu goyon baya a wannan tafiya tamu a bayan su ne, in su na ganin mu su ka yi wa, kan su su ka yi wa mugunta.

Shugabanci ne, an zaɓe mu. Ba mu yi alƙawarin za mu yi kaza da kaza ba. Fatan mu mu yi abu mai kyau. Idan mu ka zo mu ka yi shekara biyu ba mu yi komai ba, da ma ba mai ce mana mun yi alƙawari, sai dai a ce mun gaza, amma gazawar tamu wa ya haifar mana da ita? Su ne ai!
Mu kuma da mu ke a ciki ai tamu ta yi kyau. Babu wanda zai ce bai san Gidan Dabino ba shekara talatin baya. Saboda haka su ake gyara wa saboda su su ke tasowa yanzu, su su ke neman suna, su ke neman ɗaukaka. Mu Allah ya riga da ya yi mana komai.
Kuma ba mu shigo wannan mulkin ba don neman ɗaukaka ko suna ko neman kuɗi. Allah ya sani, na shigo da zuciya ɗaya, kuma zan yi iya yi na da zuciya ɗaya.