• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnati za ta kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar da ‘yan makaranta miliyan 10

by DAGA ALI KANO
May 24, 2022
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq, Minista

Hajiya Sadiya Umar Farouq, Minista

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa za ta riƙa kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar ‘yan makarantar firamare miliyan 10 a kowace rana a shirin ta na ciyar da ɗalibai, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) da ta ke gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan.

Shugabar gungun ma’aikatan da ke gudanar da shirin, Hajiya Aishatu Digil, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi kan hanyoyin rarraba abincin da sake duban fasalin kuɗin da ake kashewa a shirin.

Ta ce Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta samo amincewar a riƙa kashe N100 a kan kowane yaro a kullum a shirin.

Ta ƙara da cewa daga yanzu, za a riƙa kashe N100 a kullum wajen ciyar da kowane daga ‘yan makaranta 9,990,862 ‘yan ajin firamare ɗaya zuwa aji uku da ke cikin shirin da a kullum a tsawon kwana 20 a wata, wanda jimillar kuɗin ya kama N999,086,200 a kullum.

Ta ce, “A da kafin yanzu, mu na kashe N70 ne wajen ciyar da kowane yaro, a abinci zaman ci ɗaya. Haka mu ke yi tun daga 2016, amma yanzu shugaban ƙasa ya amince a ƙara kuɗin zuwa N100.

“Mu na da masu ruwa da tsaki irin su Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Faɗakarwa ta Ƙasa (National Orientation Agency, NOA), da Ƙungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improved Nutrition, GAIN), da Ma’aikatar Aikin Gona da ta Ilimi, da ma wasu, da za su tattauna kan hanyoyin rarrabawar.

“Mun taru a nan ne domin mu kalli hanyar da ta fi dacewa mu yi amfani da ita wajen samun alfanun shirin bisa sabon tsarin kashe kuɗi don inganta kyawun abinci da ake ba yaran.

“Lissafin kashe N100 ɗin shi ne: N70 shi ne kuɗin dukkan kayan haɗa abincin amma ban da ƙwai, sai N14 kuɗin ƙwai da za a riƙa saye ta hanyar gwamnatocin jihohi da haɗin gwiwar Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria).

“Mu na tsara fitar da ranar da za mu kira ‘Larabar Cin Ƙwai’ (‘Egg Wednesday’), inda za a riƙa ba kowane yaro da ke cikin shirin ƙwai guda ɗaya a kowace ranar Laraba; sai N10 ta ladar masu girki, N5 da N6 na tabbatar da lafiyar abinci wanda za a riƙa ba masu girkin, da kuma naira ɗaya ta tabbatar da inganci, wadda za a ba jami’ai masu sa ido, wanda wannan zaɓi ne.”

Digil ta ce shirin zai tabbatar da an tsame muggan halayen aiwatarwa, ta ƙara da cewa ma’aikatar na so ta kawo gyare-gyare.

Ta ce, “Bayan wannan taron, za mu tattaro shawarwarin masu ruwa da tsaki, sannan mu miƙa su ga minista saboda mu aiwatar da sabon tsarin kuɗin ciyarwar, wanda zai fara daga wannan watan.”

A nasa tsokacin, Dakta Umar Bindir, wato jagoran aiwatar da Shirin Inganta Rayuwa na Ƙasa (National Social Investment Programme), ya ce shirin ba haƙƙin Gwamnatin Tarayya ita kaɗai ba ne.

Bindir ya ce domin bada cikon N30 da zai zama N100 wajen ciyar da ‘yan makarantar, ya zama wajibi a tuntuɓi masu ruwa da tsakin.

Manajan shirin na NHGSFP a Jihar Sakkwato, Malam Musa Abubakar, ya ce ‘yan makaranta da iyayen su su na murna da N70 ɗin da aka riƙa kashewa wajen ciyar da kowane yaro.

Ya ce, “To amma yanzu da aka yi ƙari zuwa N100, dukkan su za su yi farin ciki domin hakan zai ƙara yawan masu shiga makaranta.”

Babban Jami’in Shirye-Shirye na hukumar NOA, Chika Ebogha, ya ce N100 da za a kashe wajen ciyar da kowane yaro ya dace ƙwarai.

Mista Ebogha ya yi kira ga Aishatu Digil da ta ƙara maida hankali ga ɓangaren aiwatarwa kamar yadda aka tsara a jihohin da su ke da  matsaloli, ya ƙara da cewa a shirye NOA ta ke ta taimaka wajen sa ido da yin nazari kan shirin a dukkan faɗin ƙasar nan.

Shi kuma Mista Kingsley Anikwe daga Ma’aikatar Aikin Gona da Inganta Yankunan Karkara ta Tarayya, shawara ya bayar cewa a bada ƙwarin gwiwar yin gandun makaranta a makarantu domin su riƙa noma kayan abinci.

Ita ma Manajar Shoɗirye-Shirye ta ƙungiyar GAIN, Irowa Irabor, cewa ta yi ƙungiyar tata za ta riƙa bada ƙwaƙƙwarar shawara da horo ga masu aiwatar da shirin.

Miss Irabor ta ce ƙungiyar GAIN na da sha’awa kan tsarin ‘Larabar Cin Ƙwai’, sannan ƙungiyar za ta tallafa wajen fito da tsarin gani da ido a shirin a dukkan jihohi.

Shi kuma Onallo Akpa, wato Darakta-Janar na Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya, ya yi kira da a yi kyakkyawan haɗin gwiwa da ƙungiyar wajen tabbatar da aiwatar da shirin na ‘Larabar Cin Ƙwai’.

Sai dai kuma wasu masu ruwa da tsakin sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatocin jihohi su jawo wasu cikin shirin, su ka ce a riƙa dafa abincin a cikin harabar makaranta sannan kuma a riƙa tantance manoman.

Loading

Tags: 'Egg Wednesday’ initiativeAishatu DigilDisaster Management and Social DevelopmentMinistry of Humanitarian AffairsPoultry Association of NigeriaSadiya Umar Farouq
Previous Post

Ummi Rahab za ta yi wuf! da Lilin Baba, har an biya sadaki an sa rana

Next Post

Yawancin masu zagin mu ‘yan fim mun fi su asali – Hannatu Bashir (Hanan)

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Hajiya Hannatu Bashir, jaruma kuma furodusa

Yawancin masu zagin mu 'yan fim mun fi su asali - Hannatu Bashir (Hanan)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!