• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, May 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abba Gida-Gida, Kanawa sun biyo ka bashi

by DAGA ALI ABUBAKAR SADIQ
March 20, 2023
in Tsokaci
0
Alhaji Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano

Alhaji Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FALSAFA ta a siyasa ita ce: “Kar ka taɓa son wani don siyasa, sai aikin alherin sa; haka kuma kar ka taɓa ƙin wani don siyasa, sai aikin sharrin sa”. 

Wannan dalilin ya sa a 2019, sakamakon badaƙalar Ganduje mu ka yi caa da jan hankalin Kanawa cewa ba mu cancanci shugaba haka ba. Amma sai aka wayi gari “Mai gaskiya” a sama, ya ɗaure gindin rashin gaskiya a ƙasa. Duk da kamfen ɗin mu ya karɓu wajen al’umma an fito an kada gwamnati, sai “Inconclusive” ya ƙwace nasarar ƙiri-da-muzu. Kwankwaso ya yi rawar gani wajen ƙin tunzura magoya baya kuma aka karɓi ƙaddara. 

Ina kyautata zato Allah ya dubi wancan dattako da ya nuna da haƙurin Kanawa wajen haɗiye baƙin ciki, domin akwai bambancin a zafin an kayar da kai zaɓe da kuma bambancin ka ci zaɓen a ƙwace maka, aka jira shekaru huɗu.

Allah gwani ne na hisabi, domin da ya tashi yin sakayya, a duk cikar APC sai aka rasa waɗanda za a bai wa takara face waɗanda su ka yi ta’addancin da ya kawo tsaiko a zaɓen Gama (Gawuna da Garo), abin da ya haifar da “Inconclusive”, kuma su ka karɓe zaɓe. Amma sai Allah ya zaɓo su a APC domin cikar hisabin, yadda a rana irin ta yau sai ga shi an wayi gari Abba Kabir ya kayar da su ya zama gwamnan Kano, abin da su ke ta hanƙoron samu. Wannan babban darasi ne ga duk wani mai tsoron Allah ya gane cewa duk wata isa, ƙarfin iko ko wayo da tsageranci ba ya ba da mulki. Allah dai shi ne tutiyal mulk.

Ina taya Kanawa murnar wannan babbar nasara domin ba nasarar Kwankwaso ko Abba ba ce. Tarihin mu ya nuna cewa tun daga Jamhuriya ta Biyu, Kanawa na canza masu mulki da ƙarfin ƙuri’a, domin mun ga yadda Gwamna Rimi ya faɗi zaɓen 1983; Kabiru Gaya ya kayar da Magaji Abdullahi a 1992; Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003, Kwankwason ya kada jam’iyya mai mulki a 2011. 

Wannan gwaninta ta siyasar mu ta yi yunƙurin ɗorawa a 2019, amma aka daƙile ta. Amma sakamakon jajircewa irin ta Kanawa sai ga shi a 2023 wannan ɗabi’a ta siyasar mu ta dawo daram. A gani na, wannan shi ne babbar nasarar mu, ba kawai cin Abba Gida-Gida ba. Nasara ce ga ‘yanci da siyasa da al’ada, nasarar kowa ce, har Gawuna da Garo da su ka faɗi a yau, domin idan Abba ya gaza, su na iya dawowa a 2027.

Allah ya ce mana idan mu ka gode wa ni’imar sa sai ya ƙara mana, wanda kuma duk Allah ya ni’imta amma bai gode ba, da sannu azabar Allah za ta riske shi. Kamar yadda duk da ƙwace zaɓen 2019, maimakon APC ta kyautata wa Kanawa, sai aka buɗe sabuwar sharholiya tare da ƙuntata wa al’umma da yin abubuwa, a kalmar Madugu, na “Rashin daraja”. Ba a taɓa ƙazantar mulki ba irin ta waɗannan shekaru huɗu a mulkin Kano. Malamai marasa daraja sun kasa faɗa wa masu mulki gaskiya, sun ɓige da zama kakakin su. Duk filayen jiha an sayar da su. A baya-bayan nan, daf da zaɓe, mun ga yadda Allah ya taimaka aka daƙile yunƙurin sayar da filin gwaf na Kano Club, fili tilo da ya rage mana a matsayin lambu.

Abba Kabir, zaɓaɓɓen gwamna, ina fatan cewa shekarun 2019-2023 ba wani Bakano da ya cancanci wa’aztuwa da cewar mulki ya na da iyaka, kuma aikin ka shi ne hisabin ka, sama da kai domin da kai Allah ya nuna mana aya. Mu na kyautata maka zato, sanin cewa kai ne ginshiƙin ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta bijiro da su a 2011-2015. Don haka a yanzu da kai ne wuƙa-da-nama, mu na tsammanin ka zarta haka. 

A baya kun gina dubban azuzuwa amma ba kayan aiki, ba ‘welfare’ ta malamai. Dole a yi haka idan ana son farfaɗo da ilimi. Kun yi gadar sama, abin da ya zama wani abin kwaikwayo da ma’auni ga gwamnoni a Arewa. Yanzu ba lokacin gina gada ba ne, lokaci ne na gina masu hawa gadar. 

Kwankwaso a baya ya gaza wajen kashe biliyoyi a zangon sa na biyu, ba tare da saka jari a hanyoyin da za su samar wa jiha kuɗaɗen shiga ba (musamman a harkar noma). Wajibi idan ka na son nasarar ka da ta Kanawa ta ɗore, dole ne ka cire mu daga jerin jihohi almajirai, waɗanda kullum ƙoƙon su a hannu sai ƙarshen wata a garzaya Abuja a samo ‘yar tsaba. Da zarar an biya albashi (kusan biliyan 10) sai ka ga an yi wawason ragowar an zuba aljihu sannan a hari watan gaba. Wallahi Kano ta fi ƙarfin haka idan akwai shugabanci mai hangen nesa. 

Kano na iya samar da kuɗaɗen shiga da ba sai ta jira ‘allocation’ ba. Misali, madatsun ruwa sama da 16 a Kano wallahi za su iya samar da biliyoyin daloli, ba naira ba, ga gwamnati. A noman kifi kawai a waɗannan madatsun, Kano na iya karɓar cinikin dala biliyan biyar a duk shekara na kifin da ake shigowa da shi Nijeriya. Kuma harka ce da ba ta buƙatar wani gagarumin zuba jari. Kuma ana iya noma tsawon shekara na tsaba (alkama, shinkafa) da musamman kayan marmari (shi ne ma tambarin jam’iyyar ku ai). Baya ga samar da lantarki, musamman ganin yadda sabuwar dokar ƙasa ta sahale wa jihohi yin hakan.

Kada ka mayar da hankali wajen cewa sai ka taɓa komai, da zarar ka jajirce wajen samar wa Kano hanyar kuɗaɗen shiga, ka ci kashi hamsin na ƙalubalen ka. Ka guji kuskuren Kwankwaso wajen yin ayyuka irin na rukunin gidajen kwankwasiyya, Amana da Bandirawo. Ka ga dai idan ka ɗauke Abuja, duk Nijeriya babu inda ake da ‘estate’ irin su. Rashin tsari wajen ƙirƙira da aiwatar da aikin, musamman na rashin la’akari da ‘continuity’, dubi irin asarar da ya jawo wa Kanawa. 

Wata shawarar gare ka ita ce ka lalubo makusanta waɗanda su ka san ka ka san su, waɗanda za su iya kallon ƙwayar idon ka su gaya maka gaskiya ba tare da tsoro ba. 

A ƙarshe, Kwankwaso ya kamata ya yi la’akari da cewa duk yadda ya kai dai horar da kai, bai kai yadda ya horar da Ganduje ba amma aka wayi gari sun yi hannun riga. Ya kamata ya sakar maka mara, ya zama uba ga kowa. Sannan kada ka manta cewa Kanawa ne ke bin ka bashi daga yau, domin an yi maka iya halacci, kuma ɗan halal shi ne ke rama halacci da halacci. 

Allah ya ba ka ikon biyan bashi kuma ya kare ka daga maimaita kurakurai irin na Kwankwaso da Ganduje. Allah ya taya ka riƙo, Excellency Sir.

Loading

Tags: Abba Gida-GidaAbba Kabir YusufAbdullahi GandujeAPCGawunaGwamnan Jihar KanoKanawaNNPPRabi'u KwankwasoZaɓen 2023
Previous Post

‘Yan iska sun ƙone gidan mawaƙi Rarara saboda siyasa

Next Post

Abba Gida-Gida ba zai watsar da ‘yan fim na Kano ba saboda ƙalilan ne su ka mara masa baya, inji Iyan-Tama

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Gwamna Abba Kabir Yusuf

Abba Gida-Gida ba zai watsar da 'yan fim na Kano ba saboda ƙalilan ne su ka mara masa baya, inji Iyan-Tama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!