ABUBAKAR Shinko ya na ɗaya daga cikin matasan mawaƙa masu tasowa a garin Kaduna. Matashin ya ɗauki tsawon lokaci ya na waƙa, amma sai a yanzu ne tauraruwar sa ta fara haskawa.
Mujallar Fim ta tattauna da wannan fasihin, inda ya feɗe mana biri har wutsiya kan ko shi waye da yaushe ya fara waƙa da ko wanene ubangidan shi, da abin da ya sa ya yi waƙar ‘Mutuwar Budurwa’ da kuma wani abu mai ciwo da fitaccen mawaƙi Umar M. Shareef ya yi masa. A sha karatu lafiya.
FIM: Ka faɗa wa masu karatun mu tarihin ka a taƙaice.
ABUBAKAR SHINKO: Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai. Suna na Abubakar Shinko. Ni ɗan garin Kaduna ne.
Na yi karatu na na firamare a Nurul Islam da ke unguwar Rigasa, na kuma yi ƙaramar sakandare na a GSS, duk a nan cikin Rigasa. Daga nan kuma na koma Arewa Model School, inda a nan na kammala karatu na na sakandare. Bayan na gama ne kuma na shiga harkar waƙa.

FIM: Wane yare ne kai?
SHINKO: Ni Bahaushe ne. Mahaifin mu ɗan Jihar Sokoto ne, ita kuma mahaifiyar mu ta na ɓangaren Kano da Katsina ne.
FIM: Shekarun ka nawa a duniya?
SHINKO: Zan kimanin shekara 25 a duniya.
FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka a harkar waƙa?
SHINKO: Na tsinci kai na a harkar waƙa dalilin ta na burge ni. Kuma da ma ni mutum ne mai sha’awar isar da saƙo ta hanyar waƙa. Duk wasu abubuwa da ke faruwa na rayuwa zan iya ɗauko shi in sa shi ta waƙa, domin ya fi sauƙin isa wurin jama’a.
FIM: Ta ina ka fara?
SHINKO: Na fara da waƙoƙin yabo. Tun a lokacin ina Islamiyya, duk ranar Laraba ni ne ke tashi in rera waƙar yabo. Da haka na fara. Sai wani aboki na da ake kiran sa Tijjani ya ce min, “Abubakar, yadda na ga ka iya waƙar yabo, za ka iya irin waƙoƙin Hausa da ake yi.” A lokacin akwai wani kamfanin su, ya ɗauke ni mu ka je wurin, ya ce in kwatanta yi masa waƙa. Da na yi, sai ya ce min gaskiya ta yi daɗi kamar da ma a cikin harkar na ke. A haka dai ya yi ta jan ra’ayi na har ta kai ga yanzu ina cikin harkar dumu-dumu. Yanzu haka na saki album ɗi na mai suna ‘Abokan Juna’, na biyun kuma mai suna ‘Mutuwar Budurwa’ ya na kan hanya.
FIM: A wace shekara ka fara waƙa?
SHINKO: Na fara waƙa a shekarar 2007 zuwa 2008.
FIM: Ka yi waƙoƙi aƙalla za su kai nawa?
SHINKO: Gaskiya ban san adadin su ba.
FIM: Ko za aka iya lissafa mana wasu daga cikin waƙoƙin ka?
SHINKO: Akwai ‘Abokan Juna’, wanda na yi tare da Nura M. Inuwa. Akwai ‘Ameera’, ita ma tare da Nura na yi ta. Akwai ‘Maryama’, wanda na yi tare da Umar M. Shareef. Akwai ‘Bakandamiya’, ‘Sabo Da Juna’, duk tare da Umar na yi su.
FIM: Wace waƙa ce bakandamiyar ka?
SHINKO: ‘Maƙabarta’ ita ce bakandamiya ta. Amma kuma duk waƙoƙi na babu wacce ba na so.
FIM: Me ya sa ka yi waƙar ‘Mutuwar Budurwa’?
SHINKO: Gaskiya labari ne mai tsawo. Mun taso tun mu na yara tare da yarinyar, har ta kai ga mun shaƙu mu na ƙaunar junan mu, har iyayen mu su na mamakin abin. Ko da wani wuri za ta je, sai ta faɗa min. Daga baya sai na fahimci iyayen ta ba su so na da yarinyar; ina ganin canji a idanun su. Daga baya sai su ka ce min za ta yi tafiya, za ta ziyarci dangin baban ta a Kano. Sai na ce mata ya za a yi kenan za ta tafi ta bar ni? Sai ta ce, “Ai sati ɗaya zan yi.” Da ta tafi, sai aka kawo saƙon cewa ita ta rasu, aka kawo gawar ta Kaduna duk a cewa ita ɗin ce ta rasu. Amma ko a lokacin ban yarda da cewa ita ce ta rasu ba, duk da cewa ban duba gawar ba. Labarin na da tsawo, idan ka saurari waƙar za ka fahimci abubuwan da ke ciki. Abu ne wanda ya faru a zahiri.
FIM: Ka na da ubangida a harkar waƙa?
SHINKO: Gaskiya babu wanda zan ce ga shi shi ne ubangida na. Tun da na fara harkar waƙa da kuɗi na na ke zuwa na biya na yi waƙa na. Ka san da man na ce maka na fara tun daga Islamiyya da waƙoƙin yabo, ka ga ai ba zai ba ni wahala ba. Amma dai a situdiyon Umar M. Shareef na ke waƙoƙi na. Amma ko lokacin da na je, na je masu a matsayin mawaƙi ne. Amma kuma daga baya na koma situdiyon Musa Mairabo.
FIM: A lokacin da ka ke Shareef Studio, wane irin tallafi shi Umar ɗin ya ba ka?
SHINKO: Gaskiya ya yi min tallafi ta fannin yi min kiɗa mai kyau da kuma yi min aiki mai kyau. Sannan ya na yi min sauƙi wurin biyan kuɗi, domin na kan biya kuɗin waƙa ne kamar guda biyar a lokaci ɗaya.
FIM: Amma bai yi maka ƙoƙarin ya tallafa maka wajen duniya ta san ka kamar yadda duniya ta san shi ba?
SHINKO: Gaskiya bai yi min ba, domin akwai album ɗi na wanda na nemi dama mu yi hoto da shi a saka a bangon album ɗin kafin saki album ɗin a kasuwa, da shi da Nura M. Inuwa, na yi wa Nura magana ya ce in yi wa Umar ɗin magana, da na yi masa magana, sai ya ce min ba zai yiwu na saka hoton su ba, sai dai in saka sunan su. Ya dai nuna min ba zan iya ɗaukan hoto da su ba. A gaskiya ban ji daɗin abin da Umar ya yi min ba.
FIM: A lokacin da ya yi maka wannan abin, ya ka ji a ran ka a matsayin sa na maigidan ka, tunda ka za zauna a ƙasan shi, kuma ka na ba shi girma?
SHINKO: Gaskiya ne! Amma ko da na fara waƙa a Shareef Studio, duk da dai ina zuwa da kuɗi na ne, na je masa matsayin kamar maigida na; ina ba shi girma, da sauran su, amma kuma biyan kuɗi na na ke yi. Amma ka ga duk da wannan ya kasa yi min wannan alfarmar.
FIM: Waɗanne irin nasara ka samu a wannan harka?
SHINKO: Alhamdu lillah, na samu nasarori da dama, tunda ga shi yanzu ina ta ƙara samun masoya. A baya ba a san ni ba, amma ga shi yanzu an san ni. Ina kuma samun saƙonni daga masoya na. Kuma ina samun waƙoƙin biki, na sarauta, suna da sauran su. Waɗannan nasarori ne ba ƙanana ba.

FIM: Ka taɓa yin waƙar fim?
SHINKO: A’a. Ba a taɓa sa waƙa na a fim ba, amma na yi waƙoƙi daban-daban wanda za a iya saka su a fim.
FIM: A ƙarshe, menene saƙon ka ga masoyan ka?
SHINKO: Ina godiya ga masoya na da kuma maƙiya na. Don Allah ku riƙa taya mu da addu’a, kun san yadda yanayin sana’ar ya ke. Ɗan’adam ajizi ne.
![]()







