• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano za ta tura ‘yan Kannywood 5 ƙasar Chana domin karatun ilimin fim

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 5, 2022
in Labarai
0
Dama zuwa hagu: Gwamna Ganduje, Alh. Nabraska da Malam Khalid tare da abokan ziyarar a Gidan Gwamnati

Dama zuwa hagu: Gwamna Ganduje, Alh. Nabraska da Malam Khalid tare da abokan ziyarar a Gidan Gwamnati

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Jihar Kano ta bayyana cewa za ta tura mutum biyar daga masana’antar shirya finafinai ta Kannywood zuwa ƙasar Chana domin su koyo yadda ake shirya fim a zamanance.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ya bayyana haka lokacin da dattawan Kannywood su ka kai masa ziyara a Gidan Gwamnati da ke Kano a daren Lahadi, 4 ga Satumba, 2022.

Sun kai ziyarar ne a ci gaba da ƙoƙarin da su ke yi na samar wa da masana’antar su mafita daga matsalolin ta.

Sun je a bisa jagorancin babban mai taimaka wa gwamna a kan Kannywood, Malam Khalid Musa, da kuma mai ba da shawara ga gwamna shawara a kan farfaganda, Alhaji Mustapha Badamasi Nabraska, musamman domin su yi masa godiya saboda muƙaman da ya naɗa ‘yan fim a gwamnatin sa, wanda ya nuna ya na tare da su kamar yadda su ke tare da shi.

Nabraska na yi wa gwamna wani bayani mai daɗin ji (Hotuna daga: Shafin Mustapha Nabraska a Instagram)

Da ya ke jawabi a lokacin zaman nasu da gwamna, Malam Khalid ya bayyana Ganduje a matsayin wanda ya ke kula da harkar matasa da cigaban su, don haka su a matsayin su masu gudanar da sana’ar a Kannywood, su na godiya da kulawar da su ke samu a gwamnatin sa.

Daga nan ya roƙi gwamnan da cewa su na buƙatar ƙarin ilimi a cikin harkar su don su na da masu fasaha da kuma ƙwazon da idan su ka samu damar ƙarin karatu daga waje, to babu shakka masana’antar za ta ci gaba da bunƙasa, wanda kuma yin hakan cigaban Jihar Kano ne da ƙasa baki ɗaya.

A lokacin da ya ke mayar da jawabi, Gwamna Ganduje ya nuna farin cikin sa a game da haɗin kai da ‘yan fim su ke ba gwamnatin sa, kuma ya yi alƙawarin samar da gurbin karatu na mutane biya daga masana’antar finafinan waɗanda za su je ƙasar Chana  domin su yi karatun a can.

Ya buƙace su da su je su ga Mataimakin Gwamna, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shi ne ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, domin su gabatar masa da ƙudirin.

Ɗaya daga cikin dattawan Kannywood ɗin, wanda tare da shi aka kai ziyarar, Alhaji Sa’idu Isa Gwanja, ya shaida wa mujallar Fim cewa tuni su ka tantance sunayen mutane biyar ɗin da aka nema su ka tura wa gwamnan domin shigar da sunan su.

Ya ce: “Bayan da mu ka dawo, jiya Litinin mu ka tantance sunayen mutane biyar mu ka  tura. Kuma a wajen tantancewar mun kalli waɗanda su ke da ƙwarewa da kuma kishin masana’antar finafinai ta Kannywood yadda idan sun yi karatun sun dawo za su taimaki harkar da ma Jihar Kano baki ɗaya.”

Loading

Tags: Abdullahi Umar GandujeChanafimGidan GwamnatiKannywoodKanokaratuKhalid MusaMustapha NabraskaSa'idu Isa Gwanjaziyara
Previous Post

Abin da Umar M. Shareef ya yi mani mai ciwo a harkar waƙa – Abubakar Shinko

Next Post

Iyan-Tama ya maka mai sharhi a Facebook a kotu kan zargin ɓata sunan ‘yan Kannywood

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Hamisu Iyan-Tama (a hagu) da Imam Aliyu Indabawa

Iyan-Tama ya maka mai sharhi a Facebook a kotu kan zargin ɓata sunan 'yan Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!