FITACCEN jarumi Rabi’u Muhammad Rikadawa (Dila) ya bayyana dalilin da ya sa ba a ɗaura auren ‘yar sa Hauwa’u kamar yadda aka tsara za a yi ba a ranar Asabar, 5 ga Maris, 2022.
A hirar da ya yi da mujallar Fim bayan an ɗaura auren yarinyar da ya ke riƙo, wato Naja’atu, ya ce: “Ka san a wannan zamanin da ake ciki duk wanda ya wahalar da kan sa shi ya so. Na yi niyyar in aurar da su gaba ɗaya kamar yadda aka ga kati ya nuna. Bayan da mu ka gama komai da komai, sai ya kasance akwai irin gwaje-gwajen nan da ake yi kafin a yi aure, wanda za a duba shin an dace a yi auren? Dukkanin wasu irin cututtuka da idan an yi aure wata cuta na iya tasowa.
“Bayan gwajin ‘geonotype’, sai aka gano angon da ita Hauwa’u nau’in ƙwayar halittar su ɗaya ne, akwai yiwuwar idan su ka yi aure za su iya haihuwar ‘ya’yan nan da ake kira sikila. To ka ga da muguwar rawa, gara ƙin tashi. In ma ka an ce an yi auren, ƙarshe da-na-sani zai biyo baya”.

Rikadawa ya ƙara da cewa: “Duk wanda ya san masu cutar sikila, ya san yadda su ke fama da kan su, haka iyayen masu ciwon sikila su ke fama da su. Saboda haka idan ka ƙulla irin wannan alaƙa daga baya sai dai ka yi kuka, ba ka da abin da za ka yi, su ma ka ga za yi su a kuka share-share babu yadda za su yi. Gara duk abin da za a yi a ba juna haƙuri tunda ba cewa aka yi ba za su yi auren gaba ɗaya a duniya ba, kowa sai ya nemi abokin burmin sa, shi ya nemi wacce idan su ka yi aure za su haifi ‘ya’ya lafiya lau, ita ma ta nemi wanda idan su ka yi aure za su haifi ‘ya’ya lafiya lau. Wannan shi ne kawai, ba wani abu ba.
“Kuma duk wanda ya ji wannan abu kuma ya ce zai yi auren a haka, ya jahilci kan sa, duk abin da ya biyo baya kuma shi ne da kan sa.”
Da mujallar Fim ta tambaye shi abin da zai ce game da wannan rana ta farin ciki a gare shi, sai ya ce: “Wannan rana ce ta farin ciki, domin duk mutumin da ya wayi gari a matsayin sa na uba, ya na da ‘ya’ya mata har su ka kai munzali, ba shi da burin da ya ke da shi illa ya ga ya kauda su a gaban sa.
“Alhamdu lillahi, Naja’atu yau an yi auren ta da Muhammad Mubarak. Ina yi masu fatan alkhairi, ina kuma roƙon Allah ya sa abokan arzuƙan juna ne. Wannan wani nauyi ne da na sauke, kuma ina farin ciki sosai.
“Duk da cewa Naja’atu ba ni na haife ta ba, ‘yar wani aboki na c,e ba wai aboki na ƙud da ƙud ba, mun taso ne a unguwa ɗaya, tun mu na matasa, an yi yawo tare, wurin zaman hira ɗaya da sauran su, aka girma kuma kowa ya yi aure ya kama gaban sa.
“To shi mahaifin ta sai ya auri ƙanwar mata ta. Allah cikin hukuncin sa yau da gobe, kowa da sanadin sa, shi sai Allah ya jarabce shi da ciwon suga, sai ya rasu, ita ma mahaifiyar ta ɗin ta na da hawan jini, haka dai duk su ka rasu. To ga shi ta ɓangare na aboki na ne, ta ɓangaren mata ta kuma ‘yar ƙanwar ta ce, wannan dalilin ya sa mu ka ce bari mu ɗauko ta, tunda da ma akwai sa’o’in ta in ka haɗe su za ka ga tare za su taso; da wadda na aurar bara, Fatima, da ita tazarar su ba zai wuce ‘yan watanni ba.”

Daga ƙarshe, Rikadawa, wanda aka fi sani da Baba Ɗan Audu a yanzu, ya miƙa saƙon godiyar sa ga abokan sana’ar sa, ‘yan’uwa, iyalin sa da sauran jama’a. Ya ce, “Alhamdu lillah, musamman su abokan aiki su ne waɗanda na fi zama a cikin su kafin ‘yan’uwan da kuma iyali na, yanzu mafi yawancin rayuwar ta fi a cikin abokan sana’a. To kuma abokan sana’a da ma ka san mu, in ana magana irin wannan na wata hidima ta same mu, ko wannan ƙungiya ta 13×13 da mu ke ta surutun ta cikin ‘yan kwanakin nan abin da ake ta jaddadawa kenan, mu riƙe zumunci, kar ya zama cewa sai lallai wane da wane kaɗai na ke hulɗa shi, kusan kowa a yi hulɗa ɗaya, saboda haka a wurin ‘yan kallon mu uwa ɗaya uba ɗaya mu ke.
“Ka ga kamar ni yanzu ɗan wasan da na daɗe ban gan shi ba, sai wani ya bugo min waya ya ce ina wane ko kuma ba shi waya mu gaisa, a wurin su uwa ɗaya uba ɗaya mu ke. ‘Yan’uwa da abokai tun na tasowa da waɗanda aka haɗu a tsakiyar tafiya, alhamdu lillahi babu wanda bai yi ƙoƙari iya na shi ba, kuma da ma zumunci ne, babu abin da ya wuce in ka na da hidima irin wannan mutane su zo su taya ka, in na kuka ne a taya ka, in kuma na farin ciki ne shi ma a taya ka.
“Kamar yadda ka ke gani, manya da ƙanana da ‘yan siyasa da sauran ‘yan kasuwa babu wanda bai zo ba. Gaskiya wannan abin farin ciki ne a gare ni. Na ji daɗi sosai. Ina yi wa kowa fatan alkhairi, Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.”
Tun kusan mako biyu da su ka gabata Rikadawa ya fara raba katin bikin ‘ya’yan sa Hauwa’u Rabi’u Muhammad Rikadawa da Naja’atu Yusuf. An dai ɗaura auren Naja’atu Yusuf da sahibin ta Muhammad Mubarak Ibrahim a ranar Asabar, 5 ga Maris, 2022 a babban masallacin unguwar Kabala West da ke Titin Nnamdi Azikiwe Way (Bypass), Kaduna, da misalin ƙarfe 1:20 na rana a kan sadaki N100,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa Alhaji Sani Sha’aban (Ɗanburam Zazzau), Musa Muhammad Abdullahi, Abubakar Anka, Abdul M. Shareef da Abubakar Waziri Bado.
Mu na fatan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.




Ina taya yan uwa da abokan arziki murnar saura kwana kadan a fara azumi