HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, (MOPPAN), tare da haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, (NFVCB), za su gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki don a tattauna kan bunƙasa harkar fim.
Kakakin ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya bayyana a wata sanarwa da ya aiko wa da mujallar Fim cewa: “Taron kwanaki biyu, wanda aka shirya za a gudanar daga ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022 zuwa Alhamis, 10 ga Maris a Kano.
Jigon taron shi ne: ‘Haƙƙin Da Ya Rataya a Wuyan Rassa da Ƙungiyoyi Kan Harkar Shirya Fim Da Fitowar Su a Soshiyal Midiya, Alfanu Da Illa Ga Al’umma”.
Ya ce za a gayyato wasu ƙwararru domin su gabatar da maƙaloli, waɗanda mahalarta za su iya tattaunawa kan su tare da nazartar maudu’in da su ka ƙunsa.
Ciroma ya ce maƙalolin za su ta’allaƙa ne kan samar da wayar da kai da zurfin fahimta a kan sashen soshiyal midiya, alfanun ta da wasu illoli da ta is da su ga al’ummaSaboda haka, a cewar sa, mahalarta za su samu kyakkyawar fahimta game da cigaban harkar shirya fim na zamani.
Ya ce: “MOPPAN za ta gabatar da babbar tattaunawa a rana ta biyu inda za a tattana kan muhimman batutuwa da su ka danganci tsarawa da ƙalailaice duk wani naƙasu da aka samu a babban taron shekara biyu-biyu da aka gudanar a Janairun 2022.”
![]()







