Dakta Bilkisu Yusuf Ali aminiya ce ta kurkusa ga marigayiya Hauwa Lawan Maiturare, wadda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 1 ga Oktoba, 2025. Tun da aka yi rasuwar, mujallar Fim ta so jin ta bakin ta a game da wannan babban rashi da irin alaƙar marubutan biyu, amma yanayin da ta samu kan ta a ciki ya sa hakan bai samu ba.
A ƙarshe dai, mun tattauna da Dakta Bilkisu kan wannan al’amari na rashi wanda ya girgiza duniyar marubutan Hausa.
FIM: Ya aka yi kika samu labarin rasuwar Malama Hauwa Lawan Maiturare?
BILKISU YUSUF ALI: To, inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Lallai na yi babban rashi na aminiya ta, Hauwa Lawan Maiturare. Kuma labarin rasuwar ta ya fara zuwar mini ne kamar almara ko ji-ta-ji-ta domin na farko dai na san a ranar take tarewa a gidan ta, don haka akwai hidimar baƙi na tarewa a gidan ta, don haka na san lafiyar ta ƙalau. Kawai na buɗe Facebook cikin dare sai na ga an saka hoton ta da alamar ta rasu. Kawai ina gani sai na ce, “Wannan wanne irin wasa ne?” Sai kawai na ji rai na ya ɓaci, saboda ba na son ma na ji wani abu maras daɗi, don haka sai na kashe wayar ma.
To amma na zo na kwanta sai kiraye-kirayen waya; mutane suka rinƙa kira na a waya, sai na ga mutane suna ta kira na a jere a jere: Sadiya Garba, Teema Ɗanborno Abu Hidaya. Sai gaba na ya faɗi. Ina ɗaukar wayar kuwa sai na ce, “Wai me yake faruwa ne?” Sadiya ta ce, “Hauwa Lawan Maiturare ta rasu.” Na ce, “Ba gaskiya ba ne, don na san tana tarewa a gidan ta yau.” Sai aka ce na bincika.
To, daga nan sai na ga ban san ma abin da zan yi ba. Daga baya dai Abu Hidaya ya kuma kira na, na ce, “Na ji maganar, amma ƙarya ne.”
Sai ya ce ba ƙarya ba ne, na kira waya.
Sai Teema Ɗanborno ta kira ni ta ce abin nan fa da gaske ne. To daga nan jiki na ya yi sanyi. Duk daga lokacin da yake dare ne haka na zauna har garin Allah ya waye. Ƙarfe bakwai ina gidan su. Na ga gawar ta, gaskiya ne ga ta a kwance, na tabbatar da ba wasa ba ne.
Kuma gaskiya ba zan iya kwatanta yadda na ji ba a lokacin da na gan ta a kwancen nan. Kawai dai idan abu ya faru babu abin da za a ce sai dai haƙuri.

FIM: Ko za ki iya tuna iya daɗewar da kuka yi tare da ita?
BILKISU: To, na farko dai na san ta kamar shekaru ashirin a baya. Amma shaƙuwar mu da ita kamar shekaru sha uku zuwa sha huɗu ne. Kuma a yadda na san ta, mace ce mai haƙuri, mai kazar-kazar, da kuma tawakkali ga Allah a komai nata. Sannan a rayuwar ta mace ce mai tsananin son Shugaba Salallahu Alaihi wa Sallama, don haka kullum za ka gan ta cikin salati da yabon Annabi; ko aiki take za ka same ta cikin yabon Annabi.
Saboda mai son aiki ce, ba ta son zama waje ɗaya. To amma kuma tana aikin tana yabon Annabi. Sannan tana da kulawa, don ta fi ni. Duk lokacin da ta ji ni shiru kwana biyu sai ta nemo ni. Haka idan muka ɗauko wani aiki za mu yi, to ta rinƙa bibiya ta kenan. Kuma fa aikin ba nata ba ne, nawa ne. Don haka duk wani abu da na ce zan yi, to sai ta fi ni damuwa a kan ta ga abin ya tabbata. Don ko lokacin da nake rubutun kundin kammala karatu na na jami’a haka ta ƙarfafa mini tare da ba ni gudunmawa, da haka har na kammala, tana taya ni.
To duk abin da yake da muhimmanci a wajen ka ita za ta ɗauke shi da muhimmanci, kuma ta fi ka damuwa da abin har ta ga abin ya tabbata. Tana da wannan abin.
Sannan ba ta da son kai. Ta fi nuna damuwa a kan abin wani a kan nata.
Don haka gaskiya na yi babban rashin da zan ce babu irin sa, don haka yana da wahala na samu aminiya irin ta.

FIM: An fi ganin ki tare da ita fiye da kowace marubuciya. Ko me hakan yake nunawa?
BILKISU: To abin da ya sa aka fi ganin mu tare da ita, muna da wasu abubuwa ne da muka zo muke da shi iri ɗaya. Ai da akwai marubuta da na san su kafin na san ta, kuma ina mu’amala da su har yanzu, to amma ita abin da ya sa ita alaƙar mu da ita ta fi ƙarfi, na farko dai ita ‘yar Ɗariƙa ce, ‘yar Faira, saboda haka duk wani lokacin da za a je wani taro ko Mauludi, ko wani abu da ya shafi Shehunnai na ziyara, tare da ita za mu je. To wannan ya sa mun zama muna da shaƙuwa. Sannan kuma ɗalibar jami’a ce, na san ta lokacin tana digirin farko ni kuma ina digiri na biyu. To wannan abin ya ƙara haɗa mu, saboda abu ɗaya muke karantawa; tana karanta Hausa, ina karanta Hausa. To sai ya zama duk abin da ba ta gane ba ni za ta zo ta samu, aikin da aka ba ta ni ce. Na ‘yan ajin su ni ce, komai da nata da ba nata ba, sai ta ɗebo ta sa na yi musu. To wannan ya ƙara kusanci na da ita.
Sai kuma wani abu da ya ƙara haɗa ni da ita: tana da son ibada. Don tun Lokacin da mahaifi na yana raye tana zuwa wajen sa har ta kai idan ma bai gan ta ba, zai ce, “Ban ga ‘ya ta ba.” To akwai wasu abubuwa ma na Malam da yake yi na Ruƙiyya, ni ba na zuwa amma ita tana zuwa, saboda sun ta da addu’ar da ƙaunar ta je wajen Malam su zauna su yi hira, sai ta mayar da ranar da zai zauna ya ga baƙi ranar zuwan ta.
To wannan zuwan ta gidan mu wajen Malam nan ma ya kuma sawa mun shaƙu.
Sannan sai kuma harkar iyali. Duk abin da ya shafi yara na – na gida ne, na makaranta, harkar biki ne – duk tana gaba a kai. Ko wa ya ga harkar bikin ‘ya ta da aka yi ita ce komai. To wannan ma ya ƙara shaƙuwar mu da ita.
Sannan kasancewar ta marubuciya ta sa duk wani abu da ya shafi rubutu a jami’a duk tare muke zuwa ko’ina.

Sannan kuma wani abu da ya ƙara haɗa mu shi ne tana da ƙaunar waƙa, kuma tana yin waƙar, don haka duk abin da ya shafi waƙa da mawaƙa a ko’ina ne aka gayyace ni sai mun tafi tare da ita.
Don haka abubuwa ne da yawa suka haɗa mu, shi ya sa haɗuwar mu kusan kullum za a gan mu tare.
Kuma tana ƙoƙarin ta kashe duk wata rigimar da ta taso; ko ba tata ba ce sai ta yi ƙoƙari ta yi wannan.
Don haka abubuwa da dama na alkhairi da zumunci Hauwa Lawan Maiturare ta yi fice a kan su, kuma ta kasance gurbi mai wuyar cikewa. Babu abin da za mu ce sai dai Allah ya jiƙan ta. Allah ya yafe mata, ya sa ta huta. Annabi ya san da zuwan ta.
FIM: To, madalla, mun gode.
BILKISU: Ni ma na gode sosai.
![]()







