FITACCEN makaɗi kuma mawaƙin nan, Rabi’u Yakubu Dalle, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na yin wani gangamin taron mawaƙa na arewacin ƙasar nan a Kaduna.
Dalle, wanda shi ne ya ƙirƙiro taron kuma a ƙarƙashin kamfanin sa na Lafazi za a yi shi, ya faɗa wa mujallar Fim cewa za a gudanar da shi ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2022 a ɗakin taro na Gamji Gate.
Ya ce taron, mai taken ‘Dallejo All Arewa Celebrity Concert’, ba a taɓa shirya irin sa ba a harkar waƙoƙi irin na zamani a Arewa ta fuskar tsari da kuma yanayin yadda za a gudanar da shi, musamman ganin cewa ba wata ƙungiya ce a cikin ƙungiyoyin mawaƙa ta shirya shi ko za ta ɗauki nauyin gudanar da shi ba.
Yayin da ya ke bayyana manufar taron, mawaƙin ya ce: “Abubuwan da su ka jawo shirya wannan taron su na da yawan gaske, musamman idan ka duba yadda ake gudanar da harkar waƙoƙi a wannan lokacin.

“Ko da yake mun daɗe da wannan tunanin, amma duba da yadda harkar waƙar ta samu kan ta a yanzu mu ka ga ya kamata mu yi wani yunƙuri domin yi wa tufka hanci.”
Ya ci gaba da cewa, “Yanzu idan ka duba yadda waƙar Ado Gwanja ta tayar da ƙura, abubuwa ne da in aka bari su ka ci gaba, to abin ba zai yi wa harkokin waƙa a nan gaba daɗi ba.
“Ba wai lafazin da ake amfani da shi ba ne abin dubawa, a’a, yadda ake juya abin ya koma wata ma’ana ta daban, da yadda wasu su ke juya lamarin don wata biyan buƙatar su.
“Yanzu idan ka duba waƙar Ado Gwanja da a ke ta surutu a kan ta, ba ina nufin ya yi abin da ya dace ba, amma dai yanayin lafazin bai kai har a zo ana ta irin wannan surutai ba. Amma da yake akwai wasu da su ke da wata manufa da su ke ganin sai sun yi amfani da maganar za su samu biyan buƙatar su, sai su ka yi ta yawo da maganar.
“Haka ma baton Safara”u, duk wani abu ne da idan aka bi shi a hankali ba zai kai ga haka ba.”
Ya ƙara da cewa, “Don haka ne mu ka samar da wannan taron wanda zai kasance da manufar wayar da kai a kan shigar da waƙoƙin zamani, yadda za su dace da kyawawan al’adun mu na Hausawa da Fulani.
“Saboda haka, a wannan taro mu na so duk wani mawaƙi da ya ke Arewa kuma ya ke waƙa da Hausa ya zama ya samu gayyata zuwa wajen wannan taron, don haka ne tsawon lokaci mu ke ta fafutukar yadda za a gudanar da shi cikin nasara.”
Dalle ya nemi gudunmawar duk wani mai kishin Arewa da kuma yaren Hausa da ya shigo ya bayar da tasa gudunmawar domin ganin taron ya gudana.
Ya ce, “Haka nan mawaƙa su sani wannan taron nasu ne, don haka duk wani mawaƙi ya na cikin harkar. Don haka ƙofa a buɗe ta ke kowa ya shigo a yi da shi.”
Gaskiyahanyayi Allah yabamu nasara baba ali zakinwaka