• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

by MUKHTAR YAKUBU
December 14, 2025
in Tattaunawa
0
Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

Malam Kabiru Musa Jammaje

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN furodusan nan na Kano wanda ya saba shirya finafinan Turanci, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya soma wani yunƙuri na shirya fim mai dogon zango nan da ɗan wani lokaci mai zuwa.

A cikin wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim, Jammaje ya bayyana dalilin da ya sa a yanzu ya mayar da hankali kan shirya fim mai dogon zango duk da cewar finafinan da ya yi a baya duk masu gajeren zango ne.

Ya ce: “Mun yi finafinai a baya masu ɗan yawa, ina jin sun kai guda bakwai ko takwas, wanda aka yi na Hausa da na Turanci, ko da yake fim ɗaya ne na Hausa, duk sauran na Turanci ne . Kuma dukkan su finafinai ne masu gajeren zango.

“To amma a yanzu na samu sauyin ra’ayi daga wanda nake kai na ba zan yi fim mai dogon zango ba.

“Gaskiya a baya ina da tunani a kan ba zan yi mai dogon zango ba. To amma dai akwai furodusa Bashir Abubakar Maishadda da Lawan Ahmad, su ne kullum suke ƙarfafa mini gwiwa a kan ni ma ya kamata na yi mai dogon zango ɗin, don haka a yanzu sun ja ra’ayi na zan yi.

“Baya ga haka kuma, ni a karan kai na na duba na ga duk finafinai da ake yi masu dogon zango, babu finafinan da suke koyar da ilimi ta hanyar koyar da wasu darussa; duk finafinan sun shafi soyayya ne da zamantakewar aure.

“To ni kuma ka ga a ɓangaren da aka san ni a fin ina yin finafinai ne na koyar da harshen Turanci da kuma al’adun mu na ƙasar Hausa, musamman ta ɓangaren sarauta,  kasuwanci da kuma koyar da ɗalibai darussan Turanci da yadda ya kamata masu koyon wani yare su kasance.

“Wannan ya ba ni ƙwarin gwiwa na in shiga fannin don ganin an samar da wannan ilimi a cikin finafinai masu dogon zango.

“Don haka a yanzu mun yi nisa wajen samar da labarin, wanda ƙwararru a kan rubuta labari suna can sun duƙufa wajen samar da labarin da zai yi daidai da fim ɗin, ko kuma na ce da kai a yanzu haka ma sun kai matakin ƙarshe na rubuta labarin.”

Da muka yi masa tambaya a kan cewar finafinai masu dogon zango ana saka su ne a YouTube ko a gidajen talbijin, wanda a baya ba shi da ra’ayin hakan, sai ya ce: “Wato ni dai ina ganin cewa YouTube ɗin ba wani biya suke yi ba. Sannan na biyu idan ka yi ba lallai ka kai gidan talbijin su saya su biya ka kuɗin ka ba. Sannan ga wahalhalun da suke cikin yin fim mai dogon zango ɗin. To ni kuma ina da ayyuka na koyarwa da rubuce-rubuce da sauran su.

“Amma dai daga baya sai ya zama duk wannan tsoron da nake da shi zan iya cewa ya kauce. Tunda ka ga shi Bashir Abubakar Maishadda ya ce zai ba ni gudunmawa ta kayan aikin da zan yi. Ka ga wannan ba ƙaramar gudunmawa ba ce.

“Sannan kuma a yanzu na lura da cewa za mu iya ware wani lokaci ko da lokacin hutun makaranta ne, sai mu yi aikin a lokacin. Kuma da yake a yanzu dala ta ɗan yi daraja a yanzu za a ɗan samu.

“Idan a baya ana ganin kuɗin ba wasu masu yawa ba ne, to a yanzu za su zama masu yawa. Daloli ko kaɗan aka biya ka, idan ka canza su da naira za ka ga kuɗaɗen masu yawa ne. Amma dai babban dalilin shi ne ƙwarin gwiwa ko na ce matsawa da nake samu daga wajen Bashir Abubakar Maishadda da Lawan Ahmad.”

Da yake ya saba shirya finafinan Turanci, ko shi ma wannan zai zama na Turanci ne? Amsa: “E to, zai zama kamar Ingausa ne, rabi Turanci rabi Hausa. Saboda fim ne da muka shirya kan gasa ta ɗalibai, shi ya sa ma muka saka wa fim ɗin suna ‘Five Winners’ wanda idan suna yin al’amurran su na rayuwa, za su rinƙa yin Hausa, idan kuma suka zo wajen gasa, da Turanci za su rinƙa yin magana, don haka ina ganin Hausar ma za ta fi yawa.

“Kuma ka ga daman mu finafinan mu za ka ga ana bai wa ilimi muhimmanci sosai. To wannan za ma ka iya cewa, kai-tsaye fim ne da aka yi shi a kan ilimi. Sai dai wasu abubuwa da muka saka da za su ja hankalin masu kallo. Ko soyayyar ma akwai ta a ciki.”

Kenan dai wannan fim ɗin za a saka yi a YouTube da kuma gidajen talbijin? Jammaje ya amsa: “”E haka ne, da man ina da YouTube channel; bai yi wani suna sosai ba, amma dai mutane sun ɗan daɗe suna bibiya idan na ɗan saka shirye-shiryen da nake gabatarwa a gidajen rediyo. Sunan sa Kabiru Musa Jammaje. To a nan za mu rinƙa sakawa.

“Kuma finafinai da muka yi na baya-bayan nan su ma za mu saka su a nan gaba kaɗan. Kuma zan so a samu ya shiga manyan gidajen talbijin wanda zai zame mana kamar riba biyu kenan.”

A game da lokacin da za su fara aikin wannan fim ɗin, babban furodusan ya ce: “To in-sha Allah zuwa nan da farkon wata na sabuwar shekarar 2026 da yardar Allah.

“Kuma muna sa ran bayan Ƙaramar Sallah za a fara kallon fim ɗin.

“Don haka masu kallon finafinan mu su shirya kallon sabon fim ɗin mai suna ‘Five Winners‘. Zai burge ku, kuma zai zo muku da sabon salon da ba ku saba ganin irin sa ba a cikin finafinan da kuka saba kallon su a wannan lokacin.”

Loading

Tags: fimfim mai dogon zangoMalam Kabiru Musa Jammaje
Previous Post

Hukumar NFC ta Ali Nuhu tana nuna mana wariya, inji ƙungiyoyin Kannywood

Next Post

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Related Posts

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Next Post
Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!