FITACCEN mawaƙi kuma jarumin barkwanci, Ado Isa Gwanja, ya ƙara shiga ƙwaryar manya, domin kuwa ya samu haihuwa a karo na farko a rayuwar sa. Allah ya azurta Ado da matar sa Maimuna da samun haihuwar ‘ya mace santaleliya.
A ranar Asabar, 17 ga Agusta, 2019 dai Allah ya nufi Maimuna da haihuwar ‘ya mace wadda ta zo cikin ƙoshin lafiya.
An yi taron suna da sati ya zagayo, inda aka raɗa wa jaririyar suna Asiya, wadda ake yi wa laƙabi da Balaraba. Kuma da yamma aka shirya wani shagali na musamman a wani ɗakin taro da ke Titin Zariya, inda mawaƙa da ‘yan’uwa da abokan arziki su ka taru domin taya shi murnar ƙaruwar da ya samu.
Da fatan Allah Ya raya Balaraba, Ya albarkace ta.
