• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Agajin marasa galihu: Ma’aikatar Jinƙai ta fara tantance sunayen waɗanda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa a Jihar Katsina

by DAGA WAKILIN MU
December 24, 2022
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta fara tattara sunayen waɗanda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa a wasu ƙananan hukumomi na Jihar Katsina.

Aikin tantance sunayen, wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa wadda Hajiya Sadiya Farouq ce minista, zai ɗauki sunayen ne daga ƙananan hukumomi 11 domin su shiga cikin tsarin masu cin gajiyar shirye-shiryen da ma’aikatar ke samar wa marasa galihu a faɗin ƙasar nan.

Jagorar tawagar da ma’aikatar ta tura Katsina domin wayar da kan jama’a dangane da shirin, Hajiya Nadia Muhammad, ita ce ta bayyana haka.

Hajiya Nadia ta ce: ”Waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa su na cikin wani halin da su ke matuƙar buƙatar samun tagomashin canjin rayuwa.”

Daga cikin tsare-tsaren da za a saka sunayen waɗanda za a tantance ɗin har da shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu, shirin bayar da jarin tallafawa domin a yi ƙananan sana’o’i, shirin N-Power, shirin ciyar da ɗalibai da sauran su.

Da ta ke jawabi, Madam Funke Olatunji, wadda ta wakilci Shugabar Sashen Ayyukan Musamman a ma’aikatar, wato Nadia Muhammad, ta ce matsalar tsaro ta kawo cikas sosai wajen kasa kai kayan agaji da gudanar da ayyukan jinƙai a wasu yankunan karkarar da ‘yan bindiga su ka addabi jama’a da dama.

Ta ce: “Dalilin haka ne wannan ma’aikata ta fito da shirin tantance sunayen domin su riƙa cin moriyar ayyukan wannan ma’aikata kai-tsaye.” 

Ta gode wa gwamnatin Jihar Katsina dangane da ƙoƙarin da ta ke kan yi wa waɗanda hare-haren ‘yan bingida ya shafa.

Wasu waɗanda hare-haren ‘yan ta’addar ya shafa daga ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari da Kurfi, sun shaida wa jami’an shirin cewa su na buƙatar muhalli.

Loading

Tags: agajiFunke Olatunjihare-hareJihar KatsinaN-PowerNadia Muhammadrashin tsaroSadiya Umar Farouq
Previous Post

An ɗaura: Jarumin Kannywood Yusuf Saseen ya zama angon Amina

Next Post

Kannywood: Auren SS Danko da Nusaiba ya tabbata

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ango Ibrahim SS Danko (a dana) tare da mawaƙi Auta MG Boy a wurin ɗaurin auren

Kannywood: Auren SS Danko da Nusaiba ya tabbata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!