AN zaɓi Dakta Ahmad Sarari a matsayin Mataimakin Shugaba na Tarayyar Ƙungiyoyin Mashirya Fim Masu Rajista a Nijeriya, wato ‘Federation of Nollywood Registered Guilds and Associations of Nigeria’.
An yi zaɓen ne a yau, 31 ga Maris, 2022 a Airport Hotel da ke Ikeja a Legas.
Sarari shi ne shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Fim ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, wadda ita ce uwar ƙungiyoyin masu shirya finafinan Hausa.
A cewar sakataren MOPPAN na ƙasa, Malam Salisu Mu’azu, shugabannin halastattun ƙungiyoyin fim da Gwamnatin Tarayya ta amince da su ne su ka yi taron su na farko a Legas, inda aka yi zaɓen.
Ya ce: “An tattauna abubuwa masu muhimmancin gaske da su ka shafi kasuwancin fim da kuma horar da masu aikin fim.
“An kuma tattauna yadda haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin zai haifar da cigaba mai ɗorewa.”

Ya ce daga bisani ne aka raɗa wa haɗakar ƙungiyoyin sunan ta na ‘Federation of Nollywood Registered Guilds and Associations of Nigeria’, sannan aka samar da shugabanni.
Shugabar sabuwar ƙungiyar dai ita ce Peace Anyiam-Osigwe, wadda kuma shugabar Ƙungiyar Furodusoshin Fim, wato ‘Association of Movie Producers’ (AMP). Ita ce wadda ta ƙirƙiro gagarumin bikin nan na karrama ‘yan fim da ake kira ‘Africa Movie Academy Awards’ (AMAA).
Shugaban ƙungiyar daraktocin fim na ƙasa, Victor Okhai, shi aka zaɓa a matsayin sakatare, yayin da shugaban ƙungiyar aftoci (AGN), Emeka Rollers, ya zama jami’in yaɗa labarai.
Haka kuma an zaɓi fitaccen ɗan wasan barkwancin nan Bolaji Amusan, wanda aka fi sani da laƙabin ‘Mista Latin’, a matsayin ma’ajin sabuwar ƙungiyar. Kafin zaɓen nasa, shi ne shugaban ƙungiyar furodusoshin wasannin daɓe da finafinai ta Nijeriya, wato ‘Theatre Arts and Motion Picture Producers Association of Nigeria’ (TAMPAN).