MATA masu harkar fim a Jihar Kaduna sun zaɓi tsohuwar jaruma Hajiya A’isha B. Umar a matsayin shugabar su ta riƙo a ƙarƙashin Ƙungiyar Matan Kannywood, wato ‘Kannywood Women Association of Nigeria’ (K-WAN).
Hakan ya biyo bayan kafa sabon reshen ƙungiyar a jihar.
A ranar Talata, 29 ga Maris, 2022 aka gudanar da taron kafa reshen ƙungiyar na jihar, a ƙarƙashin kwamitin amintattu (BoT), wanda ya ƙunshi su Hajiya A’ishatu Umar Mahuta da Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj).
Tun da farko dai akwai ƙungiyar ta ƙasa da Hauwa A. Bello (Edita) ke jagoranta.
Taron, wanda ya gudana a ofishin Kadawood da ke Amal Complex, Mogadishu Layout, Kaduna, an fara shi ne da misalin ƙarfe 2:50 na rana.
Tun da farko sai da Hajiya A’ishatu Umar Mahuta ta gabatar ga Malam Musa Muhammad Abdullahi, kuma ta sanar da shi tsare-tsaren su, sannan ta roƙe shi da ya sanya wa ƙungiyar albarka.
Malam Musa ya fara da yabo da kuma bayyana irin gudunmawar da marigayiya Hauwa Maina da Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj su ka bayar a Kannywood baki ɗaya, sa’annan ya tunatar da mahalarta cewa ƙungiyar ta na tare da MOPPAN, don haka za su iya yin amfani da kundin tsarin mulkin MOPPAN.
Sai dai kuma nan take Hajiya A’isha ta sanar da shi cewa su na da nasu kundin tsarin mulkin tun tuni. Kuma ya yarda da haka.
Malam Musa ya shawarce su da cewa ya kamata su mallaki ofis na ƙungiya, sannan su rubuta wasikar gabatar ga gwamnan Jihar Kaduna da matar sa da kakakin Majalisar Dokoki ta jihar da dukkan sauran ‘yan takarar da ke neman kujera.

Ya ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha yin ƙorafi a kan yadda ƙungiyoyin masu nishaɗantarwa ba su gabatar da kan su ga gwamnati, sa’annan ya bada shawarar ƙungiyar ta rubuta wa sababbin shugabannin jam’iyyar APC wasiƙar taya su murnar samun muƙami da su ka yi.
Haka kuma ya bada shawarar su haɗa kan su, su jawo kowa a jika.
Ita ma Hajiya Fatima Lamaj ta tofa albarkacin bakin ta, inda ta yi wa Malam Musa Muhammad Abdullahi godiya da irin gudunmwar da ya ba su, sannan ta roƙe shi da ya ja kunnen membobin, kuma su ɗauki ƙungiyar da muhimmaci.
Lamaj ta yi ƙorafi game da yadda wasu matan Kannywood ke amfani da soshiyal midiya ba a bisa ƙa’ida ba, wanda ka iya taɓa mutuncin su da na industiri ɗin baki ɗaya, kuma ya taɓa raruwar su ta gaba.
A nasa ɓangaren, tsohon shugaban ƙungiyar furodusoshi ta jihar, Malam Murtala Aniya, cewa ya yi, “Mu tsaya da maganar samun membobi a yanzu, domin in mu ka ce sai ‘yan wasa mata sun yi rajista za mu iya rasa ƙarfin mu. Mu bari sai mun kafu ta yadda ƙungiyar za ta iya jan ra’ayin mutane; wannan zai sa mutane su ‘joining’ ɗin mu.”
Hajiya A’isha Mahuta kuma ta ce, “Maganar da Naziru Ahmad ya yi a kan matan Kannywood ta sa uwar ƙungiyar ta ƙasa ta ga ya dace a kafa rassa a jihohi.”
Ta yi gargaɗin cewa dukkan wata jaruma da ba ta sayi fom ba, ba za ta sha romon ƙungiyar ba, haka dukkan wani abu da ya same ta ƙungiya ba za ta tsaya mata ba.
Daga nan kuma sai aka shiga miƙa wa waɗanda aka zaɓa a matsayin shugabannin riƙo takardar shaidar kama aiki. Malam Musa Muhammad Abdullahi ne ya miƙa wa shugaba da sakatare.
A’ishatu Mahuta ta miƙa wa sakatariyar tsare-tsare da sakatariyar kuɗi, yayin da Murtala Aniya ya miƙa wa jami’ar walwala da jin daɗi da kuma mai bincike kuɗi ta 2.
Uku daga cikin shugabannin su ne: Shugaba – A’isha B. Umar; Sakatare – Ummulkhairi Mukhtar Usman, da Sakataren Tsare-tsare – Fatima Musa Abdullahi (Macijiya).
Za su riƙe ragamar ƙungiyar na tsawon shekara ɗaya da rabi ko shekara biyu.
Wasu daga cikin matan Kannywood waɗanda su ka halarci taron su ne: Hadiza Maina, A’isha Abubakar da Karima Dikko.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.