UMMULKHAIRI Sani Panisau, wadda aka fi sani da sunan Khairat Up a soshiyal midiya, ta na ɗaya daga cikin fitattun marubutan onlayin waɗanda ake yayi a yau. Shi dai rubutun onlayin ya samu tagomashi ne tun bayan da masu karatu su ka raja’a kan karatu a intanet maimakon zuwa kasuwa su sayi littafi.
Ummulkhairi, wadda matar aure ce, ‘ya ce ga fitacciyar marubuciya Hajiya Sadiya Garba Yakasai. Mujallar Fim ta tattauna da ita domin jin tarihin ta da yadda ta zama marubuciya da yanayin rubutun onlayin, musamman ma ƙalubalen sa da yadda ake cin gajiyar sa.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki.
UMMULKHAIRI SANI PANISAU: To, da farko dai suna na Ummulkhairi Sani Panisau. An haife ni a garin Legas a 1997 a sakamakon aiki da ya kai mahaifi na can, sai dai na tashi a garin Kano saboda iyaye na ‘yan asalin garin Kano ne. Na yi karatun firamare da sakandare ɗi na a garin Kano, sannan na yi NCE ɗi na a ‘College of Arts Science and Remedial’, wadda aka fi sani da CAS; na karanci fannin ‘languages’, wato English/Hausa.
FIM: A wace shekara ki ka fara rubutun onlayin kuma ya aka yi ki ka fara?
UMMULKHAIRI: Na fara rubutun onlayin a shekarar 2014, kuma abin da ya ja hankali na kan fara rubutu gaskiya mahaifiya ta ce. Na tashi na ga mahaifiya ta ta na yin rubutu sai abin ya ke ba ni sha’awa, tun ina karatu a ɓoye har na ji ni ma ina son na ga na yi rubutun ko da sau ɗaya ne. Lokacin da na gama ‘secondary school’ ina zaune a gida, kawai na ɗauko waya ta, a take na ji labari ya zo min, sai na ɗauko waya ta na fara ‘typing’ a kafar sadarwa ta Whatsapp. Littafi na na farko sunan sa ‘So’. Daga nan kuma sai rubutu ya zame mini ‘passion’, har yanzu ina yi.
FIM: A wane ɓangare na soshiyal midiya ku ka fi yaɗa rubutun naku?
UMMULKHAIRI: Mu na yin rubutun onlayin a kafofin sadarwa kamar su Wattpad, WhatsApp, Facebook, blog, da arewabooks.
FIM: Me ya bambanta ku da masu rubutun littafi?
UMMULKHAIRI: Abin da ya bambanta rubutun onlayin da wanda ake bugawa ɗaya ne zuwa biyu. Na farko su buga shi su ke yi a matsayin littafi. Wannan shi ne bambancin duniyar mu da tasu.
FIM: A matsayin ki na marubuciyar soshiyal midiya, wane jigo ki ke yin amfani da shi?
UMMULKHAIRI: Na fi yin amfani da jigo a kan gwawarmaya da mata ke sha a gidajen auren su da yadda wasu mazan ke kallon mata a wannan zamanin. Ina yin amfani da jigo na soyayya a wasu lokutan ma. Ina yin amfani da jigon cin amana da a kan samu a fannin aboki ko ƙawa a rayuwar aure.

FIM: Ana ganin kamar duk jigon rubutun ku iri ɗaya ne kuma ku na yawan saka batsa a rubutun ku.
UMMULKHAIRI: Ba gaskiya ba ne wannan. Kowane marubuci ko marubuciya na da nashi salon rubutu; wani zai yi amfani da salon da ya ga ya kwanta masa ko ya ke ganin in ya yi zai ilimantar da makaranci ko kuma in ya yi zai isar da wani saƙo ga makaranci. Sannan akwai marubutan da ba su san ma me ake kira da rubutun ba, kawai sun faɗa harkar ne don su yi suna ko ta wane hali, sai su ke ganin ta fannin yin rubutun batsa ne zai sa a san da su ko kuma su yi suna, su a tunanin su wannan hanyar shi ne daidai da su. Salo na rubutun batsa ba salon kowane marubuci ba ne, sai dai wasu daga cikin mu su ke ɓata mana suna.
FIM: Akwai ɓoye suna da ku marubutan soshiyal midiya ku ke yi. Me ya sa hakan?
UMMULKHAIRI: To, ni dai ban san na saura ba amma ni abin da ya sa na ɓoye suna na a wancan lokacin ina tsoro kar a kama ni a gida ina rubutu, sai na mai da suna na Khairat Up, wato “Ummulkhairi Panisau”.
FIM: Ko ku na cin gajiyar rubutun ku na soshiyal midiya a yanzu?
UMMULKHAIRI: To, alhamdu lillahi, yanzu marubatan onlayin mu na cin gajiyar rubutun mu ba kamar lokacin da mu ka fara rubutun onlayin ba. Yanzu mu na saida littattafan mu ta onlayin.
FIM: Ko ku na da ƙungiya ta ‘yan onlayin?
UMMULKHAIRI: Marubutan onlayin na da ƙungiyoyi da dama masu zaman kan su.
FIM: Wane ƙalubale marubutan soshiyal midiya su ke fuskanta?
UMMULKHAIRI: Mu na fuskantar ƙalubale musamman daga wajen makaranta. A lokuta da dama idan mu ka yi rubutu idan ƙarshen littafi bai yi musu ba su kan yi sukar rubutun ta hanyar faɗar maganganu ko kuma ma wata ta zage ka kai-tsaye. Wasu lokutan kuma ba sa yi mana uzurin rashin yin ‘typing’ a kan lokaci, sai su fara faɗar maganganu, su na mantawa bayan fa rubutun nan mu na da tamu rayuwar da mu ke da ita, ba iya rubutun ne aikin mu ba. Wannan shi ne ƙalubalen da mu ka fi fuskanta. Ƙalubale na biyu kuwa shi ne sai ka yi rubutun ka sai wani/wata su yi amfani da littafin ka a matsayin nashi/nata, su sauya sunan littafi wani lokacin har ma da suna, wasu kuwa ba ma sa yin hakan sai dai su cire sunan marubuci su saka nasu. A kan samu masu yin harkar fim ma su na ɗaukar labarai ba tare da sun tuntuɓi mai rubutun ba.
FIM: Wane buri ki ke so ki cimma a harkar rubutun da ki ke yi?
UMMULKHAIRI: Babban burin da na ke son na cimma a harkar rubutun onlayin shi ne makaranta su amfana da rubutu na, ko da bayan rai na a karanta littafi na a yi alfahari da alƙalami na.
FIM: Ko ki na da tunanin nan gaba ki buga littafin ki a takarda?
UMMULKHAIRI: Ina da sha’awar nan gaba na fitar da littafi na ta yadda zai yaɗu ga jama’a. In-sha Allahu nan ba da jimawa ba zan fitar da littafi.
FIM: Menene saƙon ki ga marubutan soshiyal midiya ‘yan’uwan ki?
UMMULKHAIRI: To saƙo na ga ‘yan’uwa na marubuta shi ne a yi ƙoƙarin yin rubutu da aka san shi ne daidai ko kuma abin da ya ke faruwa a duniya don isar da saƙo na ilimi ga masu karantawa. Masu yin rubutun batsa kuma Allah ya shirye su, ya sa su daina, ya sa su gane ba sai sun rubuta batsa za su yi suna ba. Kar mu manta, duk abin da mu ka rubuta – na alkhairi ko sharri – sai Allah ya tambaye mu. Ina kira ga ‘yan’uwa na marubuta da mu ci gaba da zumunci da kuma haɗa kan mu.
FIM: To, madalla. Mun gode.
UMMULKHAIRI: Ni ma na gode.