MANAJAN Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, ya yi wa al’ummar garin Kuriga na Jihar Kaduna, al’umma da gwamnatin jihar jaje bisa ibtila’in da ya auku na garkuwa da ‘yan bindiga su ka yi da ɗalibai sama da ɗari biyu.
Ali ya miƙa saƙon jajen nasa ne a soshiyal midiya, inda ya ce, “Ina jajanta wa al’ummar Kuriga, ɗaukacin mutanen Kaduna da gwamnatin jihar kan ibtila’in da ya same su na ɗaliban da aka ɗauke. Allah ya gaggauta fitar da su da kawo mana ƙarshen wannan musiba a ƙasar mu baki ɗaya, amin.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a jiya Alhamis ‘yan bindiga su ka buɗe wuta a makarantar firamare ta Kuriga tare da sace ɗalibai aƙalla 287.