• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Amdaz da Kannywood: Ra’ayi na a taƙaice

by DAGA KABIRU MUSA JAMMAJE
December 2, 2023
in Tsokaci
0
Amdaz da Kannywood: Ra’ayi na a taƙaice

Malam Kabiru Musa Jammaje

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A SHEKARAR 2015 na shiga masana’antar Kannywood domin shirya finafinan Turanci a kan al’adu da harkokin ilimi. A shekarar 2016 na haɗu da Rahama Sadau da Abdallah Amdaz kuma na saka su a cikin fim ɗin ‘Light and Darkness’ na kamfani na. Ganin ƙwazon da Amdaz ya nuna, sai mu ka yanke shawarar ‘casting’ ɗin sa a matsayin ‘lead actor’ a fim ɗin ‘In Search of the King’ a shekarar 2018.

Tun wancan lokacin, akwai alaka mai karfi tsakani na da shi. Waɗanda su ka halarci taron ‘Jammaje Day’ na shekarar da ta gabata, sun gan shi ya na rera waƙoƙi a wajen taron.

Maganganun da Abdallah Amdaz ya yi a gaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun yamutsa hazo matuƙa kuma sun janyo masa farin jini a wajen mafiya yawan al’umma. Sai dai mafi yawan ‘yan Kannywood ba su ji daɗin kalaman nasa ba.

Daga lokacin da na shiga masana’antar zuwa yanzu, na yi ma’amala da nagartattun ‘yan Kannywood irin su Malam Sanusi Daneji, Malam Habibu Sani, Malam Khalid Musa, Alhaji Abdulkarim Mohammed, Alhaji Sa’idu Gwanja, Dakta Sarari, Aminu Ala, Ali Jita, Maryam A. Baba, Sa’a Vocal, A’isha Tsamiya, Halima Atete, Malam Ado Gidan Dabino, Alhaji Ibrahim Mandawari, Alhaji Kabiru Maikaba, Alhaji Hamisu Iyan-Tama, Al-Amin Ciroma, Bala Anas, Fauziyya D. Sulaiman, Hajiya Balaraba Ramat, Farfesa Abdalla, marigayi Umar Sa’id Tudunwada, marigayiya Hauwa Maina, marigayiya Zainab Booth, da sauran su. Sannan kuma na yi ma’amala da wasu daga cikin ‘yan masana’antar waɗanda ba za ka iya kiran su nagari ba.

A gani na, tuntuɓen harshen da Amdaz ya yi shi ne bayyana cewa “akasarin” ‘yan Kannywood ba mutanen kirki ba ne. Ban karɓi wannan ra’ayin nasa ba saboda a shekara takwas da na yi a cikin masana’antar, na fahimci cewa akasarin ‘yan Kannywood mutanen kirki ne.

Kabiru Jammaje (a hagu) da Abba El-Mustapha, Shugaban Hukumar Tace Finafinai

Kuma idan mu ka ce ‘yan Kannywood, ba mu na nufin ‘actors’ da ‘directors’ kawai ba, har da masu ɗaukar nauyi, mawaƙa, ‘yan jarida, marubuta, masu tace hotuna, da sauran su. Mutane da yawa sun ɗauka cewa masu fitowa a finafinai da masu bada umarni kaɗai ne ‘yan Kannywood. Ko kaɗan abin ba haka ya ke ba! Girman da masana’antar ta ke da shi, ya wuce yadda mutane ke zato.

Bincike ya nuna cewa membobin Kannywood sun kai kimanin 700,000. A cikin su masu ɓata wa masana’antar suna su ne mafi ƙaranci. Domin yanzu da za a ce mutum ya fito da gurɓatattun masana’antar guda hamsin, to kuwa an ba shi aiki.

 

Daga ƙarshe, zan so na bayyana cewa akwai matsaloli masu tarin yawa a Kannywood, amma da taimakon Hukumar Tace Finafinai da shugabannin masana’antar za a kawo canjin da kowa zai yi alfahari da shi. Yanzu duniya ta tafi a kan cewa fim shi ne hanya mafi tasiri ta isar da saƙo. Wannan ne ya sa ƙasashen Musulmi irin su Saudi Arebiya, Turkiyya, Marokko, Pakistan, Iran, Bangladesh da sauran su ba a bar su a baya ba wajen shirya finafinai.

* Malam Kabiru Jammaje furodusan finafinai ne a Kano

Loading

Tags: Abba El-MustaphaAbdallah AmdazKabiru Musa Jammaje
Previous Post

Gwamnatin Tinubu za ta dawo wa NTA da FRCN da martabar su – Minista

Next Post

Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita

Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!