• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu za ta dawo wa NTA da FRCN da martabar su – Minista

* Za mu yi masu garambawul cikin gaggawa, inji shi

by DAGA ALI KANO
December 2, 2023
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tinubu za ta dawo wa NTA da FRCN da martabar su – Minista

Minista Mohammed Idris ya na jawabi ga shugabannin FRCN da NTA a Kaduna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati mai ci yanzu a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta ƙudiri aniyar aiwatar da wasu tsare-tsaren gyara da za su dawo da martabar da aka san mashahuran kafafen watsa labarai biyu ɗin nan biyu da su, wato Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya (FRCN).

Hadimin musamman na ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin takardar sanarwa ga manema labarai cewa Ministan ya sha wannan alwashin ne a Kaduna a jiya Juma’a lokacin da ya kai ziyarar aiki a ofishin hukumomin biyu.

A yayin da ya ke magana kan babbar rawar da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da gidan talbijin na NTA Kaduna su ke takawa wajen jan akalar ra’ayin jama’a da watsa labarai da ɗabbaka musayar al’adu, Ministan ya ce kafafen biyu sun samu koma-baya a ‘yan shekarun nan da su ka gabata saboda watsi da su da aka yi, da rashin tarbiyyar aiki, da tsofaffin wuraren aiki da kayan aiki, wanda hakan ya karya alkadarin su wajen yin shirye-shirye da taka muhimmiyar rawa.

Daga hagu: Daraktan Shiyya na FRCN Kaduna, Malam Buhari Auwalu, ya na bayani; Daraktar Shiyya ta NTA Kaduna, Hajiya Saudatu Suleiman; Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama, da Darakta-Janar na NTA, Malam Salihu Abdulhamid Dembos a lokacin da Ministan ya kai ziyarar aiki a NTA da FRCN Kaduna a jiya Juma’a

Sai dai kuma Idris ya bada tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta farfaɗo da kafafen kuma ta mayar da su kan gaba a aikin rediyo da na talbijin a Nijeriya.

Ya ce: “Yadda za a iya mayar da NTA da FRCN matsayin wakilan ƙwarai a tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya sosai, tilas sai mun yi la’akari da babbar gazawar su a yanzu a fagen da ke cike da gasa, da amfani da basira, da amfani da fasahohin zamani.

“Dalilin zuwa na nan tare da Darakta-Janar na NTA da na FRCN shi ne domin mu nemo cikakkiyar hanyar da za mu bi don magance waɗannan matsalolin, wanda ya na kan gaba cikin abubuwan da mu ka ba muhimmanci.

“Za mu duba dukkan zaɓi da ke gaban mu domin tabbatar da cewa mun dawo da martabar da NTA da FRCN su ka rasa.”

Ministan ya ce matsalar FRCN a matakin ƙasa da na jihohi ya ma fi ta’azzara, musamman ma a Rediyon Nijeriya, Kaduna, wanda ya bayyana da cewa “a da wuri ne mai daraja na yaɗa labarai wanda ya samar da zaƙaƙuran ma’aikatan rediyo.”

“Hakika, Rediyo Nijeriya Kaduna na buƙatar a farfaɗo da shi da gaggawa. Babu shakka za mu ɗauki mataki da sauri a wannan aiki na ceto,” inji shi.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya na yin jawabi ga ma’aikatan FRCN Kaduna da NTA Kaduna, lokacin da ya kai ziyarar

Idris ya ce a lokacin da ya kama aiki, ya samu kiraye-kiraye masu yawa daga sassa da dama masu ruwa da tsaki a kan lalacewar kafafen biyu, ya na mai nanata cewa lallai aikin da ke gaban sa shi ne tabbatar da cewa an yi wa NTA da FRCN garambawul domin su cimma manufofin kafa su.

Ya ce: “Ina tabbatar wa da shugabanni da ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki a NTA da FRCN cewa Shugaba Tinubu ya naɗa Malam Salihu Abdulhamid Dembos da Dakta Mohammed Bulama a matsayin Darakta-Janar na NTA da FRCN ne bayan cikakken nazari kan ƙwarewar su wajen iya kawo kyakkyawan sauyi a hukumomin biyu waɗanda babu hukumomin aikin talbijin da rediyo kamar su wajen girma a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.

Ministan ya na duba tashar watsa shirye-shiryen FRCN da ke Jaji

“A shirye na ke in duba kowace dama da ke akwai wadda za ta bayar da duk abin da ake buƙata don tabbatar da cewa sama wa NTA da FRCN kayan aiki na zamani, bai wa ma’aikatan su cikakkiyar horaswa da kuma biya masu haƙƙoƙin aiki an yi su da gasken gaske.”

Ministan ya ce ya kamata hukumomin yaɗa labaran biyu su tashi tsaye su rungumi yanayin aikin jarida wanda zamani ya kawo wajen aiki da kayan fasaha na zamani idan har su na so a yi gogayya da su, su inganta kyawun aiki, kuma saƙwannin su su kai ga ɗimbin masu kallo da masu saurare.

Waɗanda su ka take wa Ministan sawu a lokacin wannan ziyara dai su ne Darakta-Janar na NTA, Salihu Abdulhamid Dembos, da takwaran sa na FRCN, Dakta Mohammed Bulama.

Ban da hedikwatar tashoshin biyu, sun duba muhimman kayan aikin tashoshin biyu da ke cikin garin Kaduna da kuma garin Jaji a babban titin Kaduna zuwa Zariya.

Daga dama: Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama; Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Darakta-Janar na NTA, Malam Salihu Abdulhamid Dembos; hadimin Minista, Abdulmalik Muye, da Hadimin Musamman na Minista, Malam Rabi’u Ibrahim, lokacin da ministan ya kai ziyara a Kaduna a ranar Juma’a

Loading

Tags: FRCNgarambawulkafafen yaɗa labaraiMohammed IdrisNTAziyarar aiki
Previous Post

Tinubu zai fara biyan sabon tsarin albashi daga Afrilu 2024 don rage tsadar rayuwa – Minista

Next Post

Amdaz da Kannywood: Ra’ayi na a taƙaice

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Amdaz da Kannywood: Ra’ayi na a taƙaice

Amdaz da Kannywood: Ra'ayi na a taƙaice

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!