SHAHARARREN mawaƙi Alh. Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya bayyana cewa naɗin da aka yi masa na Sarkin Waƙar Masarautar Dutse ya shammace shi, domin bai taɓa hango cewar Sarki zai yi masa wannan karramawar ba.
Ya bayyana haka ne a hirar musamman da ya yi da mujallar Fim bayan naɗin da Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Sunusi, ya yi masa a ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2019 a fadar sa da ke garin Dutse, hedikwatar Jihar Jigawa.
A ranar naɗin, an yi shagali sosai a fadar Mai Martaba Sarkin Dutse.
Taron ya zama na tarihi ga Ala da masoyan sa, don kuwa ɗimbin jama’a maza da mata sun ɓarko daga garuruwa da dama su ka halarta.
An yi hawan Daba na ƙasaita da kuma nuna isa.
Bayan taron ne mujallar Fim ta ji ta bakin mawaƙin dangane da sarautar da aka ba shi da kuma alaƙar sa da masarautar ta Dutse.
Ala, wanda da ma a watannin baya an naɗa shi sarautar Ɗan’amanar Bichi, ya fara da cewa, “To zan iya cewa alaƙa ta da masarautar Dutse tsohuwar alaƙa ce, domin mun daɗe mu na da kyakyawar alaƙa da masarautar.
“Farko ma akwai Ɗan’amanar Dutse, Alhaji Nasiru Dano, wanda ya ke sananne ne wajen yi wa mutane hidima. To shi kuma maigidan mu ne; ya kan gayyace mu duk wani al’amari idan ya tashi a nan Dutse, wanda ya shafi sarautar ko wata hidima ta jama’a.
“To ni kuma na kan je ƙasar Dutse don yin wasu abubuwa da su ka shafi waƙa ko wani uziri na daban, domin mun yi taron Ranar Mawaƙa a Dutse, kuma Mai Martaba Sarki Allah ya ba shi ikon halarta. Kuma ina ganin shi ne Sarki na farko da ya shiga cikin lamarin Ranar Mawaƙa idan aka ɗauke Masarautar Kano.
“To, halartar sa taron ya ba shi sha’awa ganin yadda ake raya al’ada bisa tsari a tsaftace cikin kamewa da mutunci, har ya sanya albarka, ya yi mana fatan alheri.
“Hakan ya sa duk wani taro da za a yi a Dutse ina zuwa.
“Sannan na yi wa Masarautar Dutse waƙa sukutum ta tarihi, wadda Alhaji Nasiru Dano ya ɗauki nauyi. Waƙa ce ta tarihin sarakunan Dutse da kuma masarautar da kuma ita kan ta Masarautar Dutse a matsayin ƙasa mai tarin albarkatu da ma’adinai a cikin ƙasa.
“To wannan shi ne abin da na sani dangane da alaƙa ta da Masarautar Dutse.”
Dangane da yadda ya samu sarautar Sarkin Waƙar Dutse kuwa, Ala ya ce, “To ganin yadda na yi waƙoƙi da su ka shafi masarautar, ashe Mai Martaba Sarki ya ga abin da na yi ya yi masa kyau, don haka ya yi niyyar ni ma ya yi mini abin da zan ji daɗi.
“Sai ya ga me zai yi wa Ala na nuna godiya da ƙaunar ƙasar Dutse da ya ke yi? Don haka ne ma ko a wajen taron, idan ka kula, abin da Sarki ya ce shi ne, ‘Mun ba ka wannan matsayi saboda nuna godiya ga ƙaunar ka ga Masarautar Dutse da kuma irin gudunmawar da ka ke bai wa al’umma da samar da aikin yi da ka ke yi ga matasa da kuma wayar da kai, don haka ne mu ka ƙarfafa maka gwiwa dangane da wannan abubuwa da ka yi, mu ka ba ka Sarkin Waƙar Masarautar Dutse.’
“To, gaskiya wannan abu ya shammace ni, don kamar ayyuka ne na alheri da na ke yi, sai kuma aka ce an gode, aka ƙarfafa mini gwiwa.
“Kuma mutane iri na za su gane lallai za ka iya aikata alheri, kuma nan gaba ka samu sakamakon sa wanda ba ka yi tsammani ba.
“Don haka babu abin da zan ce da Masarautar Dutse sai dai godiya. Kuma Allah ya ƙara wa Sarki nisan kwana.”
Daga ƙarshe, Ala ya yi godiya ga dukkan jama’ar da su ka halarci taron naɗin sa da aka yi a Dutse da ma waɗanda su ka bada gudunmawa, ya ce, “Allah ya saka wa kowa da alheri.
“Kuma ina ƙara godiya ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Dutse. Allah ya ja zamanin Sarki!”