KARIN maganar nan na “mun zo garin ku mun fi ku rawa” shi ne ya yi daidai da abin da ya samu ‘yan wasan Hausa a bikin karrama ‘yan fim ɗin nan mai suna BON Awards na bana da aka gudanar a Kano.
Bikin, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano a ranar 14 ga Disamba, 2019 ya zo wa masu harkar fim a masana’antar Kannywood da bazata ta yadda su ka kasance ‘yan kallo kawai.
Tun kafin lokacin dai ‘yan fim na Kannywood su ka cika shafukan su na sada zumunta da tallata taron tare da rungumar sa a matsayin taron da su ke da ruwa da tsaki a cikin sa, don haka su ka tashi tsaye wajen tallata bikin.
Sai dai a lokacin da aka shiga taron wasu ‘yan fim ɗin su ka fara gane cewar ba a shirya taron domin su ba, don haka ne ma wasu su ka fice daga katafaren ɗakin taron, yayin da wasu kuma da su ka zauna a matsayin ‘yan kallo.
Wani ɗan fim ya faɗa wa mujallar Fim cewa ko wajen zama na musamman ba a tanadar wa da ‘yan fim ɗin Hausa ba, kuma ba a ba su wata dama ta gabatar da komai a wajen taron ba.
Sannan abin da ya fi jefa tambaya a shi wannan taro na BON Awards, duk finafinan da aka shigar a gasar, babu fim ɗin Hausa, duk kuwa da cewar a Kano cibiyar finafinan Hausa ake gudanar da taron.
Wannan ce ta sa tun da wuri a cikin ɗakin taron wakilin mujallar Fom ya tambayi darakta Yaseen Auwal dangane da rashin finafinan Hausa a cikin gasar, inda ya shaida masa cewar, “Babu wani abu da mu ka sani a cikin wannan ‘award’ ɗin. An dai gayyaci ‘yan fim ne su zo wajen taron, amma maganar shigar da finafinan mu, ba a sanar da mu ba.

“Kuma gasa idan za ka shiga ana sanar da kai ne lokacin da za a fara shigar da fim da lokacin da za a rufe, amma mu dai an ce za a yi taro ne a Kano kuma aka gayyace mu.
“Ko da ya ke na ga an kafa kwamitin taron a cikin ‘yan fim ɗin mu su na aiki a ciki.”
Ya ƙara da cewa, “Amma dai idan ka duba, finafinan da su ke cikin gasar za ka ga ba su kai namu da mu ke yi ba, don haka su ma ba wasu fitattun finafinai ba ne ko a can Nollywood ɗin don haka za ka ga jaruman fim ɗin ma da su ka zo ba wasu fitattu ba ne.”
Shi ma T.Y. Shaba ya yi ƙorafi tare da sukar yadda aka gudanar da taron, inda ya ce, “Abin takaici ne a zo Kano a yi taron amma ‘yan Kannywood babu wata dama da aka ba su, domin babu mawaƙan Kannywood ko ɗaya da aka saka waƴar sa a wajen, duk da kuwa da kuɗin Jihar Kano aka shirya taron amma a gaban Gwamna aka mayar da mutanen Kano baya.
“Kuma wasu abubuwan ma da aka rinƙa yi a wajen cin mutunci Kano ne da al’adun Kano, don haka abin kunya ne a nuna wa duniya cewa a Kano aka gudanar da wannan taron. Akwai abubuwa masu yawa da aka yi a taron wanda ba za su faɗu ba, amma dai mu abin da mu ke gani shi ne an ci mutuncin mu a wannan taron.”
Dangane da wannan ƙorafi, mujallar Fim ta nemi jin ta bakin shugaban Hukumar Tace Hinafinai ta Jihar Kano wanda ha haɗin gwiwar su aka gudanar da taron, wato Alh. Isma’il Na’abba (Afakallahu).
Sai ya kada baki ya ce, “Taron ya wakilci kowa har da mutanen Kano. Amma abin da ya kamata mutane su sani shi ne taron sunan sa ‘Best of Nollywood’, kuma ba yanzu aka fara shi ba, wannan shi ne karo na 11. An yi shi a garuruwa da dama a ƙasar nan kuma an saka ‘yan fim ɗin Hausa a ciki waɗanda su ka samu ‘award’ kamar irin su Rahama Hassan, Fati Ladan, Nafisa Abdullahi, da sauran su.
“To wannan taron da aka zo aka yi a Kano da man nema su ke yi a jihohi, su ba su tallafi don su gudanar da taron su, kuma su na neman tallafi daga kamfanoni, don haka su ka zo su ka nema, kuma gwamnatin Kano ta ga za ta iya yi saboda bunƙasa harkar kasuwanci a jihar, don haka aka zo aka yi.
“Abin da ya kamata ‘yan Kannywood su fahimta, yanzu duniya dunƙulewa ake yi, sai a yi nasara. Amma ka duba duk ‘award’ ɗin da ake yi a Kannywood, kowa tasa ya ke yi, kowa ya girka tasa, amma su waɗannan sai su ka hadu su ka zo da abu guda ɗaya, to don me ya sa ba za su yi nasara ba? Amma kai ba ka da taka guda ɗaya kowa ta sa ya ke yi, to ya za a yi a ci nasara, kuma kowa so ya ke gwamnati ta shiga ta yi masa.
“To amma dai daga yanzu gwamnatin Kano duk shekara za ta rinƙa shirya taron ‘Kannywood Awards’ domin ɗaga martabar jihar mu da kuma masana’antar finafinai ta Kannywood.
“Shi ne ma ya sa mu ka kafa kwamiti mu ka saka ‘yan fim ɗin mu domin su fahimci yadda ake gudanar da taron saboda shirin namu na gaba.”