YAU kimanin shekara biyu kenan da gwamnatin Jihar Kano ta shirya wa masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood taron sanin makamar aiki domin su samu ilimi a dukkan ɓangarori na sana’ar tasu. An shafe tsawon wata guda ana bayar da horon a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.
Mutane 450 ne su ka samu horon.
Tun daga wancan lokacin ne kuma su ke ta jiran a ba su takardar shaidar karatun da su ka yi, wanda aka yi ta saka rana ana ɗagawa.
Dalilan da aka rinƙa bayarwa na sanya ranar taron ana ɗagawa bai wuce na cewa gwamnan Kano da kan sa ya ke so ya sanya ranar kuma ya miƙa takardun shaidar ga waɗanda su ka samu horon ba.
Bayan ɗaukar lokacin, daga baya aka aje ranar 14 ga Disamba, 2019 domin bayar da takardun.
An yi shirye-shirye masu yawa domin karrama ‘yan fim ɗin, wanda hakan ya sa aka yi ta samun maganganu masu karo da juna dangane da yadda taron zai gudana, domin kuwa surutai sun yi ta yawo a cikin’ yan fim na cewa an yi kyakkyawan shiri na miƙa takardun tare da bayar da wani tallafi ga waɗanda su ka samu horon kamar yadda ake bai wa sauran masu sana’o’i jari na kuɗi ko kayan aiki da gwamnatin jihar ta ke yi.
An yi taron a Gidan Gwamnati a ranar da aka aje.
To sai dai abin ya zo wa da ‘yan fim ɗin da bazata, inda shirya taron aka yi aka gama lami, domin kuwa taron ya jefa ‘yan fim cikin wani sabon tunani da kuma da-na-sani.
Babban abin da ya karya armashin taron dai shi ne rashin halartar gwamna tare da sauran manyan baƙi da aka shirya za su je wajen, domin kuwa duk wani babba da aka tsara zai halarci wajen to wakili ya turo.
Sannan kuma taron an shirya za a fara shi ƙarfe 10 amma sai da ka shafe wuni guda ana zaman jira, kuma haka aka bar mutane cikin yunwa da ƙishiruwa.

Babbar matsalar da mutane su ka yi kuka da ita a wajen kuma aka tafi ana ƙorafi a kan ta ita ce, an tara mutane 450 za a ba su takardun shaida, amma sai wasu shafaffu da mai guda biyar kaɗai aka bai wa, su ko sauran aka ce masu su tafi ofishin Hukumar Tace Finafinai su karɓi nasu bayan an tashi daga taron.
Ga mari ga tsinka jaka, can ɗim ma da su ka je sai su ka ga wasu ‘yan kaɗan aka bai wa. Da dama ma wasu sunan su a cikin jerin sunayen waɗanda su ka samu horon, yayin da wasu kuma aka ce satifiket ɗin nasu bai kammala ba saboda komfuta ta samu matsala.
Ba a yi la’akari da cewar wasu daga nesa su ka taho domin karɓar shaidar ba, tare da tunanin samun wani tallafi daga gwamnati, amma sai su ka tsinci kan su cikin mawuyacin yanayi na rashin samun takardar shaida da kuma tallafin da su ke sa ran za su samu.
Duk wannan ya sa mutane su ka yi ta ƙorafi bayan an gama taron.
Da mujallar Fim ta tuntuɓi shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’ila Na’abba (Afakallah), sai ya ce, “Ai maganar tallafi an gama bai wa su masu fim ɗin tallafi, domin duk wanda aka ba shi ilimin da zai gudanar da sana’ar sa ai babu wani tallafi da ya kai bada ilimi kyauta.”
Duk da haka dai ‘yan fim ɗin sun ci gaba da yin ƙorafi tare da nuna cewar kawai dai an tara su ne, kuma aka yi amfani da taron nasu domin kawai a cimma wata manufa ta siyasa.
![]()







