SHAHARARRIYAR jarumar masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Hajiya Rahama Sadau, ta bayyana cewa ta buɗe katafaren kamfanin ta na ‘Sadauz Home’ ne domin ta tattaro dukkan harkokin ta na kasuwanci a waje ɗaya, maimakon a da da su ke a rarrabe.
Rahama dai ta buɗe kamfanin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan shagali da aka yi a Kaduna a ranar 10 ga Disamba, 2019.
A wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim, jarumar ta ce ta fi kowa farin cikin buɗe sabon wurin nata, kuma “wuri ne da na daɗe ina mafarkin buɗe shi.”
Rahama ta ce: “Kamar yadda mutane su ka sani, ina ‘different businesses’ masu sunan Sadau; akwai ‘Sadau Pictures’, ‘Sadau Beauty’, ‘Sadau Lip Stick’… Sadau, Sadau ɗin ya yi yawa!
“Sai na ga cewa bai kamata a ce na rarraba kowane Sadau, Sadau da ‘different’ shaguna ko wurare ba. Kawai sai na samu ƙaton gida, wanda na ɗauki duk wani abu da ya danganci Sadau na yi shi a cikin gidan, shi ya sa na ke kiran gidan ‘Sadauz Home’.”

Mujallar Fim ta ziyarci gidan wanda ya ƙunshi sashen aski na maza da wurin gyaran gashi na mata da wurin kwalliya da wurin sayar da abinci da kuma situdiyo.
“Akwai abubuwa da dama waɗanda su ka dangance ni. Shi ya sa na ke kiran shi ‘Sadauz Home’,” inji Rahama.
A kan dalilin ta na buɗe gidan cin abinci, kyakkyawar jarumar ta ce ba ta daɗe da yanke shawarar yin hakan na, ta ce, “Gidan abinci ba wani ‘ambition’ ba ne da na ke da shi da daɗewa ba. Amma duk wanda ya san ni ya san da daɗewa na ke da situdiyo, na ke ‘makeup’ da ‘saloon’. So, sister na ta iya abinci, ‘chef’ ce, sai na ga cewa da mu raba ‘businesses’ ɗin, me zai hana mu haɗa su wuri ɗaya, ko da yaushe mu na wurin. Abin da ya fara jawo hankali na kenan.
“Ɗayan ƙanwa ta ta na ‘makeup’, ɗayar ta na abinci, ni kuma ina da ofis, ‘Sadau’s Pictures’, kawai sai na ga a haɗa su a wuri ɗaya. Abin da ya fara kawo wannan tunanin kenan.”
Rahama ta bayyana cewa abincin da su ke yi, na gargajiya ne da na Turawa, wato ‘continental’.
Ta ce, “Mu na yin na gargajiya, su tuwo, masa da duk sauran abincin gargajiya ana yi. In ka juya kuma, ƙanwa ta ta na yin ‘continental’ irin abincin ‘yan Chana, Potigis da duk dai abincin su na ƙarya!” A nan sai dariya ta kama ta.
Da wakilin mu ya yi mata batun ko wannan sabon wuri da ta buɗe ba zai shafi harkar ta ta fim ba ta yadda ɗaya zai danne ɗaya, sai ta ce, “Gaskiya ba ɗaya ba ne. Ba zan iya cewa wannan ya fi wannan wahala ba. Amma sana’ar fim komai wahala, amma kuma ɗan kallo ba zai gane ba saboda cikin awa ɗaya ya gama kallon fim ya tashi ya tafi. Ka ga ba ɗaya ba ne.
“A nan akwai manaja, sannan akwai ‘operator’ da za ta riƙa ‘operating’, ƙanwa ta Zainab ita ke ganin komai, don haka wahalar ya ɗan ɗauke mani kaɗan.”

Haka kuma ta bayyana cewa za a riƙa ganin ta a ‘Sadauz Home’ cikin ‘yan kwanakin nan saboda sabon wuri ne. Ta ce, “Dole sai na ɗan zauna na wani lokaci, saboda wani zai zo wurin ne kawai don ya ga Rahama.”