• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda za a gyara harkar finafinan Hausa, daga bakin Rahama Sadau

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 14, 2019
in Labarai
0
Rahama Sadau

Rahama Sadau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
RAHAMA Sadau, fitacciyar jarumar Kannywood, ta bayyana cewa babu wani ci-gaba da masana’antar fim ta samu a wannan shekara mai shuɗewa ta 2019.
 
Ta yi gargaɗin cewa idan har ba a ɗauki babban mataki ba, to babu yadda za a yi a samu ci-gaba a harkar.
 
Rahama ta yi wannan kalami ne a wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim.
 
Jarumar, wadda kuma ita ce furodusar fim ɗin ‘Rariya’, ta ce, “Gaskiya babu maganar ci-gaba a masana’antar fim a wannan lokacin da mu ke ciki. Saboda idan ka duba gaba ɗaya idan furodusa ya yi fim a wuri ɗaya ya ke iya saida fim ɗin sa – siniman Kano. 
 
“Mu na da jihohi 19 a Arewa, kuma duk su na kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon finafinan Hausa a kan na Kudu. Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim. 
 
“Shin fim ɗin da ka yi ɗan Kano kawai ka yi ma wa? Ina sauran jihohin da su ma su na da buƙatar kallo? 
 
“Idan ba ku manta ba, na yi ‘Rariya Tour’; in ka ga mutanen da su ka zo su ka kalla… mun je Yola, mun je Gombe duk mun nuna, amma saboda rashin gidajen kallon ba a kai masu finafinai. 
 
“Yanzu sai dai ka yi fim kawai ɗan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda ci-gaba ya ke. Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim ɗaya sai ka yi kuɗi. 
 
“Ban da yanzu, saboda kowa ja baya ya ke yi, babu wanda zai zuba kuɗin sa ya yi fim, kuɗin su ƙi fitowa.”
 
Da mujallar Fim ta tambaye ta shawarar da za ta bayar don a shawo kan wannan matsala, sai Rahama ta amsa da cewa ko dai a koma amfani da hanyar intanet wajen tallata finafinan ko kuma a gina gidajen sinima aƙalla guda biyar a Arewa, maimakon guda ɗaya rak da ake amfani da ita a Kano.
 
Ta ce: “Kullum in mu ka zauna mu na magana, na kan ce dole sai mun haƙura mun tafi ‘digital’, kamar yadda duniya ta tafi. 
 
“Idan ba za a yi ‘providing’ sinimu da yawa ba, a yi ko da guda biyar ne a garuruwan da aka san cewa sun fi kallon finafinan Hausa. 
 
“Idan kuma ba za a yi wannan ba, sai dai mu tafi ‘digital’. Saboda duk furodusan da na haɗu da shi, sai na tambaye shi, ‘Ka na da dibidi a gidan ka?’ Bai da shi! Kowa a waya ya ke kallo. Sai a nemi hanyar da za a tafi ‘digital’ ɗin da ɗan kallo zai sa a wayar shi ya kalla. Wannan shi ne kaɗai mafita.”
 
Ta ƙara da cewa, “In kuma ba za a iya wannan ba, gwamnati ta yi haƙuri, ta daure – saboda mu na biyan haraji, babu kamfanin da zai yi fim bai biya haraji ba; duk da ban dai sani ba, amma ni ina biya – a daure a gina mana sinimu ko da guda biyar ne a gani, a ce yau wancan ya saida dubu biyar a Kano, ana yi maka maganar miliyoyi ne. 
 
“Wannan shi ne mafita, in ba shi ba sai dai a haƙura.”

Loading

Previous Post

Haihuwa ta 2: Rahama Sirace ta samu Fatima

Next Post

Dalili na na buɗe ‘Sadauz Home’ – Rahama Sadau

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Rahama Sadau (a hagu) tare da ƙanwar ta Zainab Sadau a wajen bikin buɗe 'Sadauz Home'

Dalili na na buɗe 'Sadauz Home' - Rahama Sadau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!