MASU iya magana sun ce rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A yau dai uwar ɗiyar ba ta ji kunya ba, domin kuwa an ɗaura auren mawaƙiya kuma marubuciya Sa’adatu Isah Muhammad (Sa’a Vocal) kamar yadda aka tsara.
An ɗaura auren Sa’a da sahibin ta mai suna Haiwatu Sa’id Daud da misalin ƙarfe 11:15 na rana a yau Lahadi, 20 ga Disamba, 2020 a babban masallacin Juma’a na Umar Bin Khaɗɗab da ke shataletalen Dangi kusa da Titin Gidan Zoo, a Kano, a kan sadaki N50,000.

Taron ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki. Sai dai mujallar Fim ba ta ga fuskar abokan sana’ar amaryar ta waƙa ko marubuta a wajen ba.
Ita dai Sa’a matashiyar marubuciyar labaran hikaya na zube ce kuma sananniyar mawaƙiya a masana’antar finafinan Hausa.
Haka kuma ma’aikaciya ce a gidan talbijin na Arewa24 da ke Kano.
‘Yar asalin Kano, Sa’a Vocal ta na aikin waƙa ne yawanci tare da fitaccen mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa).
Ɗimbin waƙokin da ta yi tare sun haɗa da ‘Mai Waƙa’, ‘Ba Zan Sake Ki Ba’, ‘Mati Da Lado’ da kuma ‘Mati a Zazzau’.
Haka kuma ta yi waƙa da Nazifi Asnanic mai suna ‘Ƙasar Mu Najeriya’, da dai sauran mawaƙa.
A ɓangaren rubutu kuma, Sa’a Vocal ta rubuta littattafai da su ka haɗa da ‘Ƙauna Ce Sila’ da ‘Ƙaddarar Mu’.
Mu na addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba ita da angon ta, amin.

