JAMA’A da dama ne su ke yin tururuwa zuwa wajen zaman makokin mahaifiyar shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, wadda Allah ya yi wa rasuwa jiya da yamma a Kano.
Hajiya Aisha El-Mustapha ta rasu ne da yammacin jiya Talata, 29 ga Agusta, 2023 bayan gajen rashin lafiya kuma an yi jana’izar ta tun a jiyan a maƙabartar Ɗandolo da ke Kano.
Marigayiyar, mai kimanin shekaru 67 a duniya, ta rasu ta bar ‘ya’ya takwas – mata biyar, maza uku.
Abba El-Mustapha shi ne babban ɗan ta namiji.

Fitattun ‘yan siyasa da ‘yan fim ne dai su ke zaman makokin da kuma ta’aziyyar a gidan marigayi Alhaji El-Mustapha Inuwa da ke Ƙofar Gadon Ƙaya.
Kadan daga cikin ‘yan fim da su ka halarta sun haɗa da tsohon shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu), da Baballe Hayatu, Aminu Shariff Ahlan, da Nura Hussaini.

