SULAIMAN Adamu, wanda aka fi sani da Ɗanladiyo Mai Atamfa a harkar waƙa, ya na ɗaya daga cikin mawaƙa masu kaifin basira da hazaƙa, wanda har wasu na kamanta shi da fitaccen marubucin waƙoƙi kuma mawaƙi Ibrahim Ibrahim na Kano. Ƙwararren marubucin waƙoƙi ne, sannan ya ƙware wurin rera waƙa da yin kiɗa.
Ɗanladiyo bai tsaya a nan ba, domin ƙwararre ne wurin rikodin ɗin mawaƙi a lokacin da ya ke rera waƙa. Bugu da ƙari, matashin fasihin ya ƙware wurin yin waƙa da irin muryar Sani Musa Danja. Idan ka ji waƙar sa da irin muryar Danja, ba za ka taɓa bambanta su ba.
Irin su Ɗanladiyo ba su da yawa a Kannywood, domin kuwa shi ya haɗa komai a harkar waƙa. Da zaran ka zo wurin sa, to ka gama waƙa ko da kuwa ba ka san yadda za ka yi ka yi waƙar ba.
Ya na shiri da kowa. Dalili shi ne shi mutum ne mai ladabi da biyayya ga babba da yaro, kuma bai ɗauki kan sa a bakin komai ba duk da ɗimbin basira da hazaƙar da Allah ya ba shi.
Ya na yi wa mawaƙa da dama a ciki da wajen Kaduna rubutun waƙa, wasu ma shi zai rubuta sannan ya ɗora waƙar da muryar sa, in ya gama sai kuma wanda zai yi waƙar ya zo ya na bin muryar tasa ana cire ta Mai Atamfa.
Mujallar Fim ta tattauna da Ɗanladiyo Mai Atamfa, inda ya feɗe mana biri har wutsiya game da rayuwar sa, daga yarintar sa har zuwa zaman da ke yi a Kannywood.
Shin me ya sa ya ke shiga ta atamfa a kullum? Ko Bayarabe ne? Ku karanta ku ji.
FIM: Masu karatu za su so jin cikakken sunan ka da tarihin rayuwar ka a taƙaice.
ƊANLADIYO: Suna na Sulaiman Adamu, wanda aka fi sani da Ɗanladiyo Mai Atamfa. Ni haifaffen garin Kaduna ne. Na yi karatu na tun daga firamare har zuwa sakandare duk a garin Kaduna.
Bayan na gama sakandare na, ban cigaba ba, sai na faɗo harkar waƙe-waƙe.
FIM: Me ya ba ka sha’awar shiga harkar waƙa?
ƊANLADIYO: Abin da ya ba ni sha’awar shiga harkar waƙa bai wuce a ce nazari a kan irin abubuwan da su ke faruwa ba, ko kuma in ce fasaha. Kuma na ga ni ma ina da fasahar da zan iya bada gudunmawa a cikin wannan harka, shi ya sa na shigo ta.
FIM: Koyon waƙar ka yi ko da baiwar ka ka shigo?
ƊANLADIYO: Kamar yadda ake cewa ana koya, kuma ka kan shigo da baiwa iya wadda Allah ya ba ka. Daidai gwargwado dai na shigo da baiwa ta. Sai kuma taimakon yadda ake yi da na samu, sai ya ƙara yi mini jagora a kan harkar.
FIM: A wace shekara ka fara?
ƊANLADIYO: Na fara wannan sana’a a shekarar 1994.
FIM: Da wace waƙa ka fara?
ƊANLADIYO: Wasu su na fara waƙa ne da waƙar soyayya. Amma ni na fara gwada murya ta da wata waƙa da na yi da muryar wani fasihin mawaƙi kuma jarumi a shirin fim, wato Sani Musa Danja, don shi ne jarumin da na ke so a harkar fim kuma ya ke burge ni. Waƙar ma na yi ta ne da muryar sa.
FIM: Tsakanin asalin muryar ka da muryar Sani Danja da ka ke yi, wacce ka fi jin daɗin yi waƙa da ita?
ƊANLADIYO: E to, babu muryar da ta fi yi min daɗi kamar ta kwaikwayon, kamar yadda ka ce, don ta fi gamsar da ni bisa asalin murya ta da na ke yi. Yawancin lokuta ma idan ba da salon sa na yi waƙa ba sai in ji kamar ba ni ba ne; gaba ɗaya ba na jin daɗin ta, shi ya sa ma na raja’a kacokam a kan wancan salon.
FIM: Gaya mana wasu daga cikin waƙoƙin ka.
ƊANLADIYO: Wasu daga cikin waƙoƙi na akwai ‘Hattara Mata’, ‘Mutumin Mutane’, ‘Rayuwa Babu Tabbas’, ‘Sabulun Salo’, ‘Ka Fi Tsire’, ‘Unguwar Kanawa’, ‘Silifas’ da sauran su.
FIM: Me ya sa ka ke son waƙe irin su ‘Silifas’, ‘Ka Fi Tsire’, da sauran su?
ƊANLADIYO: Wannan ya samo asali ne daga nazarin da na ke da shi na in ƙirƙiro wani abu da mutane ba su yi, ni kuma sai in zo in sa wa kai na, in takura kai na in ƙirƙiro shi in yi. Hakan ya sa duk wanda ya san ni a industiri su ke cewa ni bauɗaɗɗen mutum ne: idan an yi ta can, sai in yi ta can. Irin wannan ra’ayi na rayuwa ta shi ne ya sa min tunanin cewa irin waƙoƙin soyayya da ake yi ya saɓa wa tunani na, don waƙoƙin soyayya ni a wuri na su na yi masu ma waƙar mutuwar zuciya. Sai zuciyar mutum ta mutu, sai ya zo ya fara waƙa, waƙar ma ta shirme. Kalmar soyayya duk abin da za ka faɗi, an riga da an faɗe ta, ba burgewa ka yi ba, nanata ta ka yi.
Kawai sai na yi tunanin in yi abin da wani bai taɓa tunanin zai yi ba.
Na tuna da wata waƙa da na yi mai suna ‘Silifas’. Mutane sun yi sharhi a kan waƙar sosai, inda su ka rinƙa cewa ba ni da aikin yi da na je ina waƙe silifas. Na tambaye su da cewa silifas ba ya yi maku rana? Ba ku amfani da shi kullum? Su ka ce su na yi. Na ce don me shi ba za a waƙe shi ba? Ku kenan nazarin ku gaba ɗaya ya tsaya ne a kan soyayya?
Da na yi ta, an yi ta damu na in je in kai waƙar kamfanin da su ke yin silifas, na ce ni kawai na yi waƙar ne don a san muhimmancin silifas.
Haka na yi wa sabulun salo. Ya na da amfani an sani, amma ta ya za a yi a faɗa a waƙa Kuma na yi nazarin mutane su na sauraren waƙoƙi fiye da sauraren masu magani. Haka ya sa na ga ya kamata in yi tallar wannan sabulu ta waƙa. A nan wani in ya ji zai ce a’a, menene sabulun salo? A wannan zamanin yara da dama ba su san sabulun salo ba, ballantana su san amfanin sa.
Wannan dalilin ya sa na ke ɗauko abubuwa na ke faɗin amfanin su, sannan in tuna wa waɗanda su ka mance da su.
FIM: Ya gwagwarmayar ka ta ke tsakanin ka da sauran mawaƙa?
ƊANLADIYO: Alhamdu lillah! Gwagwarmaya ana yi, saboda duk wanda ya shigo ɗin, kamar yadda na faɗi a baya cewa daidai gwargwado waƙa ba koyon ta na yi ba, Allah ne dai ya buɗe mani ƙwaƙwalwa daga ciki, sai ya zamana da wannan baiwa na ke gwagwarmaya da sauran mawaƙa ‘yan’uwa na, wanda kuma tun da na fara harkar har zuwa yau duk wanda na yi harka da shi sai dai ka ji ya na sambarka.
FIM: Bayan kasancewar ka mawaƙi, kai marubucin waƙoƙi ne wanda ka na yi wa mawaƙa da dama rubutun waƙa. Ya ka ke kallon kan ka a wannan matsayin?
ƊANLADIYO: Ina ƙara yi wa Allah godiya, sakamakon ban da waƙoƙi da na ke yi na ƙashin kai na, ina kuma tallafa wa wasu a cikin sana’ar. Don haka ina alfahari da haka sosai, saboda basirar ba ni kaɗai ta ke amfana ba, ba kamar irin sauran mawaƙa ba da kan su kawai su ka sani kuma su ka damu da su. Ni na kan haɗa da nawan da kuma na jama’a na yi masu.
FIM: Ka taɓa samun matsala da waɗanda ka ke rubuta ma waƙa?
ƊANLADIYO: Gaskiya ban taɓa ba, kasantuwar sai na zauna na samu tsawon lokaci ina nazari. Na kan zauna da dattijai, ina kuma bincike mai zurfi kafin na miƙa wa mutum aikin sa. Hakan ya sa ban taɓa samun matsala da duk waɗanda na ke rubuta ma mawaƙa ba.
FIM: Daga lokacin da ka fara waƙa zuwa yanzu, waƙoƙin ka aƙalla za su kai nawa?
ƊANLADIYO: Gaskiya su na da yawa, don wasu ma na manta da su.
FOM: Ka taɓa yin album?
ƊANLADIYO: Na yi album guda biyu, amma ban fitar da su kasuwa ba. Na dai yi su na fitar masu da sunaye, na raba wa masoya na da ‘yan’uwa da abokan arziƙi.
FIM: Kasancewar ka na amfani da muryar Sani Danja a waƙoƙin ka, ya alaƙar ka ta ke da shi?
ƊANLADIYO: Alaƙa ta da shi, ni dai masoyi ne. Kuma soyayyar ta sa ba wai shi gundarin sa na ke so ba, muryar sa ce kawai na ji ta yi min a rayuwa. Soyayyar muryar tasa ce ta ja min soyayyar sa, shi ya sa na duƙufa a kan ita ɗin kawai na ke yi.
FIM: Ka taɓa haɗuwa da shi Sani Danja?
ƊANLADIYO: Na taɓa haɗuwa da shi sakamakon waƙoƙin da na yi masa. Idan ba ka manta ba, na ce na yi album guda biyu; ɗaya nashi ne, na yi waƙoƙi goma sha uku duk nashi. Daga nan saƙo ya je masa, ya ji saƙwanni ta inda bai yi tsammani ba, ya ji saƙo ta nan, ya ji saƙo ta can, daga nan har Allah ya haɗa mu, kuma ya yi murna, ya yi amanna, ya ce ya ji daɗi sosai.
Sai na ke ce masa, “Don kada abu ya yi nisa na ke ta abubuwa saboda ka ji, idan kuma ka ji ɗin menene amsar bayanin ka? Shin wannan salo da na ɗiba zan iya cigaba da shi babu matsala? Idan kuma ba mu daidaita ba tsakanin mu, sai in yi haƙuri in daina saboda in ja wa kai na zama lafiya.”
Domin amfani da salon mutum idan bai yarda ba a tsarin wannan masana’anta zai iya kai ka ƙara inda ma ba za ka fita ba. Sai ya amsa da cewa ya ji daɗi, bai ɗauke shi wani abu ba. Shi ya sa sai na cigaba.
FIM: Waɗanne irin nasarori ka samu a harkar waƙa?
FIM: Babu wata nasara a harkar waƙa da ta wuce ka yi abu a amsa. Wannan ita ce babbar nasara. Ta wannan fannin na ƙaru da abubuwa da dama.
Wani lokacin idan ka yi ba za ka samu a ta ɓarayin can ba, wani lokacin ma za ka yi aikin ko asi ba za ka samu ba. A haka ma shi ma sai ya ja maka wani alheri daban, na haɗuwa da jama’a da sauran su. Wannan ma ba ƙaramin babban nasara ba ne.
FIM: Ɓangaren ƙalubale kuma fa?
ƊANLADIYO: Ƙalubalen ba zai wuce ƙwaya ɗaya ba zuwa biyu. Na farko, muryar wannan gwani nawa da na ke yi, wasu su na cewa ina satar salon wane, babu inda za ni, ni kuma sai in ce masu ni ba ina yi ba ne don in fita, ni ina yi ne don shi a san shi ɗin, a kuma san cewa ya na nan kuma har gobe ya na yi, kuma ya na da magaji. Misali, idan wani abu zai zamar masa naƙasu, shi magajin nan nashi zai iya tallafawa.
Na biyu, ko da na shigo harkar akwai yanayin suturar da na canza wa kai na. Ana kira na da Ɗanladiyo Mai Atamfa. Saka atamfa ba gadon gidan mu ba ne, kuma ni ba Bayarabe ba ne. Amma cikin hukuncin Allah sai na kalli kai na na ce ni me ya sa ba zan fita daban ba? Kuma ina so in fita daban ɗin ko da kuwa zai zama na takura.
Haka na takura kai na ta ɓangaren sa atamfofi, domin a yanzu yawancin kaya na duk atamfofi ne. A nan ina ɗan samun ƙalubele, musamman ‘yan’uwa na maza. Misali, idan za mu yi tafiya sai a ce, “Amma ba za ka sa atamfa ba!” Sai in ce, “To yanzu idan ku ka ce ba zan sa atamfa ba, wane kaya na ke da shi da zan sa bayan atamfa? Sai dai idan za a yi min sabon ɗinki!” To, a haka sai mutum ya ga don me zai yi min sabon ɗinki, ba zai tafi da ni ba.
Kuma wani lokacin tafiya da ni ɗin ya na da muhimmanci, don haka dole za a yi haƙuri a tafi da ni a haka. In kuma mu ka tafi sai su ga na ɗauko atamfa ta gangariya na yi mata ɗinki mai kyau. Ni ƙalubalen da na ke fuskanta kenan a wannan masana’anta.
FIM: Duk mai mu’amala da kai ya san cewa kai ranar Litinin ka ke yin hutun ka. Kuma ko nawa za a ba ka ba za ka fito aiki ranar Litinin ba. Menene asalin hutun ranar Litinin da ka ɗaukar wa kan ka?
ƊANLADIYO (Dariya): Wannan dai fage na tonon silili ne! To, abin da ke faruwa, ni wannan hutu da na ɗauko shi ranar Litinin ya samo asali ne tun ina makarantar firamare, tun daga yarinta kenan. Abin kuma ya faru ne dalilin ina ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaƙa a ɓangarori daban-daban.
Sai ya zamana a makarantar da na ke, abubuwa na yi wa malamai da ɗalibai yawa a ranar Litinin, sai ta kasance ina fuskantar fushi da ɓacin rai a duk ranar Litinin. In na zo makaranta sai in zama tamkar ni kaɗai ne a makarantar: je ka can, yi wancan! Ba na gabatar da karatu na yadda ya kamata a ranar.
Hakan ya sa sai na ƙirƙiri wannan hutu na ranar Litinin a makaranta. Shi kenan har zuwa makarantar sakandare na, shi ne har zuwa yanzu.
Daga baya kuma sai na gane cewa wannan hutun ya ƙara ba ni dama in rinƙa zumunci, sannan in samu kai na cikin hutu a wannan ranar.
FIM: Wanene ubangidan ka a yanzu?
ƊANLADIYO: Na ji daɗin wannan tambaya da ka ce “a yanzu”. Domin shi damo da ka ji ana cewa sarkin haƙuri, to ni na zama ɗan maraya ne ma a damon, sakamakon ni ban da ubangida.
Dalili kuwa shi ne tun da na faro ina yi wasu in su ka kalle ni sai su ga cewa ai wannan ma ai bai kai a agaza masa ba. Har sai da kuma ta ɓarayoyi daban-daban, ta irin rubutun da na ke yi wa wasu, wanda ni ban nuna kai na tun tuni ba, sai a ce wanene ya yi rubutun nan? Wani lokacin ba na iya cewa ni na yi, saboda da ma irin yadda aka raina ni, rainin kuma ba daga industiri ta faro ba, tun daga unguwa ne, hakan ya sa sai na ke killace kai na daga cikin yara, in ma yara na wasa ni ba na iya shiga, in ma na shiga ni musguna min ake yi. Sai ya zama ina killace kai na in ta rubuce-rubuce na.
To wannan rubuce-rubucen su su ka yi ‘leading’ ɗi na in na yi wa wane, wasu in su ka gani sai su ce wa ya yi wannan rubutun? Sai a ce wane ne. Sai su ce gaskiya mu janyo shi. Ta dalilin haka sai ya zamana na samu iyayen gida wanda babu wanda ba ya alfaharin na zo kusa da shi.
To, a yanzu dai ina da iyayen gida da dama waɗanda ba zan iya lissafa sunayen su ba, saboda babu daɗi in kira sunan wani ban kira na wani ba.
FIM: Kasancewar yadda harkar waƙa ta koma a yanzu, kowa ya zama mawaƙi, ya ka ke kallon abin ta yadda wasu ma kamar cin zarafin waƙa su ke yi?
ƊANLADIYO: Abin dai babu daɗi. Kuma komai sila ya ke samowa. Ta na iya yiwuwa wani an jefe shi da kalmar ya na tare da mawaƙa me ya sa shi ba zai zama mawaƙi ba? Wani kuma zai duba ne ya ga cewa ya ga a harkar nan ana samun kaza, me zai hana in samu wane ya rubuta min waƙa ni ma in je in yi, shi kenan ni ma in samu? Daga irin haka sai ka ga ya zama mawaƙi.
Haka ɗin ba aibi ba ne in har za ka riƙe ta a matsayin sana’a, kuma ka gyara wa kan ka harka ne.
FIM: Ɗanladiyo, ka yi wa mawaƙa da dama rubutun waƙa a yanzu, wanda har ta kai ga ana iya cewa a garin Kaduna kusan duk wanda ya taso, ko da ko duniya ta san shi, ya ji daɗin aiki da kai. Menene sirrin?
ƊANLADIYO: Kamar yadda ka ce, ina yi wa mawaƙa rubutu, ba ina yi masu rubutu ba ne, ina dai taya su rubutu ne. Wani kawai zai zo ya zaunar da ni ya ce min, “Ka ji salon waƙa ta, to mu cigaba da yi.” Wasu da dama ba su da lokacin rubutu ne, kamar yadda na san ƙila wata rana akwai matakin da zan kai aiki su yi min yawa, wasu da daman su sun fi ni rubutun na sani, amma sai su ce, “Wane, taya ni rubutu saboda ba ni da lokacin yi.” Kawai taimakekeniya mu ke yi da mutane.
FIM: A ɓangaren waƙar dai kuma, ka ƙware wurin naɗar muryar mawaƙa a lokacin da su ke ɗaukar waƙa, sannan kuma in an gama ka gyara waƙar wanda nan ɓangaren ma ka ƙware, har ta kai duk wanda ya yi aiki da kai, sai ya ƙara marmarin ya yi aiki da kai. Wasu ma in ba da kai su ka yi aiki ba, ba su jin daɗi. Menene sirrin?

ƊANLADIYO: Sirrin wannan ɓangaren zan iya cewa iya zamantakewa ne da mutane. Duk wanda aka ce ya zo wurin ka ko da ba ka da basirar kirki, amma ya zo wurin ka da faran-faran, ka ce masa ya ka ke so aikin ka ya zama, ya ka ke son kaza da kaza? Mutane su na son irin wannan al’amari, ka na bin su a yadda su ke so. Don haka babu abin da zai sa gaba idan ya tafi ba zai sha’awar dawowa wurin ka ba. A tunani na, ba zai wuce wannan dalili ba.
FIM: Ya zancen iyali?
ƊANLADIYO (Dariya): Iyali dai ban yi ba. Ko ina tunanin shekaru na ne ba su kai ba? Amma kuma na fi bada cewa lokacin ne bai yi ba.
FIM: Ka na kasuwa ne ko kuma akwai wacce ta yi caraf da zuciyar ka, kuma ta kasa ta tsare, ba ta son ganin wata a tare da kai?
ƊANLADIYO (Dariya): Ɗayan, biyun, uku. Babu abin da ba zai iya kamawa ba a cikin ukun nan!
FIM: Mecece shawarar ka ga mawaƙa ‘yan’uwan ka?
ƊANLADIYO: Shawara ta ga mawaƙa ita ce mu zauna da ƙaunar juna. Kuma duk wanda ya kamata a tallafa masa a kan wannan sana’a, yaro ko babba, a shigo da shi a tallafa masa.
Ta bakin wasu ‘yan industiri da su ke cewa kan-ta-waye. Shawara ga abokan sana’a na shi ne, ka sani, na sani, kan-ta-waye ba daidai ba ne, a daina amfani da kan-ta-waye ana cutar da mutane. Ka yi aiki kawai ta yadda in mutum ya je gaba zai ƙaras da cewa kai ne wane, a haka za ka iya samun shaida mai kyau a industirin.
Ai akwai waɗanda ake yi masu shaidar arziƙi, kai ma ka zama a cikin su. Babu lalatattu a industiri, wasu ne dai ke ɓata wasu.