WANNAN takardar alama ce ga irin abinda muke fada ko? Intolerance ya kai iyaka tsakanin mu.
Da za a yi Arewa Republic, jinin da za a zubar sai Allah ya san iyakar sa. Idan a cikin jami’ar Gwamnatin Tarayya, wani ɓangare zai tada jijiyar wuya kan ambaton Allah da wani zai yi a masallacin jami’a har sai hukumar jami’ar ta ba da kashedi, ina ga abin da zai faru a cikin gari idan ɓangare ɗaya ke mulkin jiha ko tarayya? Idan hukumar jami’a za ta kira zikiri a masallaci “unlawful activity,” to ina ga irin mu mutanen gari?
Malam ai idan kaulasan ya gitta, to jini ne zai biyo baya sai dai idan ba a samu dama ba. Boko Haram kam sun ba kan su damar. Da mu da ‘ya’yan mu da dukiyoyin mu duk halas ne gurin su.
Wannan shi ya sa tun da Boko Haram suka bayyana, na zame mai da’awar Nijeriya ta zauna yadda take, kuma mai ‘secularism’ ɗin da aka bar kowa ya yi addinin sa iya fahimtar sa. Gwamnatin kuma ta zauna kan ta kowa ce, ba nuna wa kowa bambanci na addini ko aƙida.
Malam addini ɗaya kenan fa. Ina ga bambancin addini da ƙabila da siyasa da Dujalawa da ke son raba Bahaushe da Bafulatani?
Allah ka ƙara mana haƙuri da juna.
* Dr. Aliyu U. Tilde marubuci ne kan al’amuran yau da kullum a Bauchi