ALLAHU Akbar! Rai baƙon duniya! Sai ɗazu na samu labarin rasuwar shahararren makaɗi kuma mawaƙin Hausa ɗin nan Alhaji Attah Dabai – kwana huɗu bayan rasuwar sa. An ce ya rasu a ranar Juma’a da ta gabata a garin Dabai da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja a Jihar Katsina. An ce ya haura shekara ɗari a duniya.
Dattijon arziki ne, Alhaji Attah Dabai.
A wannan hoton, za a gan ni ina tattaunawa da shi a gidan shi a cikin watan Nuwamba, 2013 (yanzu shekara takwas cur). Editan Mujallar Fim a lokacin, Aliyu A. Gora II, wanda tare mu ka je Dabai daga Kaduna, shi ya ɗauki hoton. A ɗaya hoton kuma Alhaji Attah ɗin ne a bangon Bahaushiya (wani sashe a cikin mujallar Fim), a fitowar ta ta Janairu 2014 lokacin da aka wallafa waccan hirar da na yi da shi. Ni na ɗauki hoton.

Gani na na ƙarshe da shi (tare da ‘ya’yan sa, su Alhaji Saleh Dabai) ya faru ne a cikin Afrilu 2018 a garin Abeokuta, Jihar Ogun, a wajen bikin kaɗe-kaɗen gargajiya na nahiyar Afrika (African Drum Festival). Su sun je ne daga Katsina a matsayin wakilan jihar a bikin, ni kuma na je daga Legas a bisa gayyatar masu shirya bikin (su Wole Soyinka) saboda wata alaƙa ta da su mashirya bikin.
Na san cewa da yawa matasan yanzu ba su san waƙoƙin marigayi Attah Dabai ba kamar yadda su ka san waƙoƙin Shata ko Ɗanƙwairo. To ai kuwa ya yi waƙoƙi da dama, inda har ya samar da wasu mawaƙan, kamar misali Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguziri.

Attah Dabai ya ciri tuta ne a fagen kiɗan dandali wanda ake kira “saran marke”, inda su ke kaɗa wata ƙaramar ganga. A wannan fage, duk ƙasar Hausa babu kamar Attah Dabai da ‘ya’yan sa. Idan ka ga wasan sa, musamman lokacin da ya ke matashi (ina da bidiyon hakan), to ba za ka taɓa mantawa da salon kiɗa da rawar ba, domin har daga kwance ya na kiɗa! Zarrar da su ka yi a fagen ya sanya a ko yaushe ake shigar da su bukukuwan al’adun gargajiya.
Hasali ma dai, babu makaɗin Hausa da ya kai Attah Dabai yawo ko ziyartar ƙasashen duniya. E, har Shata! Daga shi, sai Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos. Shi ne ma Sarkin Kiɗan Sarkin Katsina.
Shata ubangidan sa ne. Shata ne ya biya masa kujerar aikin Makka ɗaya da ya je, bayan ya yi wa Shatan kiɗa a Bakori lokacin da ya auri wata mace.

Hausawa sun ce ba rabo da gwani ba, kafin a samu gwani daga ne! Labarin Alhaji Attah Dabai ya na da tsawo, sai dai a taƙaita. Ina yi wa iyalin shi ta’aziyya. Allah ya jiƙan Baba, ya kyautata makwancin sa, amin summa amin.