• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta yi wa masu zaɓe 30,449 rajista a Filato

by DAGA WAKILIN MU
November 1, 2021
in Nijeriya
0
INEC ta yi wa masu zaɓe 30,449 rajista a Filato
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa mutum 30,449 rajistar yin zaɓe a Jihar Filato a cigaba da ta ke yi na gudanar da aikin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar nan, wato Continuous Voter Registration (CVR), wanda aka fara yi a ranar 28 ga Mayu.

Malam Halilu Pai, kwamishinan zaɓe mai zama a jihar, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Jos, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai kan watanni uku na farko na wannan shekarar. 

Pai ya ce a cikin wannan lokacin, mutum 111,276 masu yin rajistar zaɓe ne su ka nemi yin rajistar.

A watanni uku na farkon shekarar aikin rajistar masu zaɓen, mutum 88,573 ne su ka nemi yin rajista, kuma 24,654 aka yi wa rajistar, inji shi.

Haka kuma katin masu zaɓe (PVC) guda 1,524 ne aka musanya, yayin da katin zaɓe 13,898 ne aka yi wa tiransifa zuwa sabon wurin da masu zaɓe su ka koma. 

Ya ce, “A wa’adin watanni uku kashi na biyu na shekara, waɗanda ya ƙare a ranar Juma’a, 29 ga Oktoba, mutum 21,001 su ka nemi yin rajista, aka yi wa 4,653 rajistar, aka musanya katin zaɓe guda 6,66, sannan aka yi wa 3,347 tiransifa zuwa sabon wurin da masu zaɓe su ka koma da zama. 

Kwamishinan ya ce a ƙoƙarin da hukumar ke yi na yi wa ‘yan Nijeriya aiki tuƙuru a wajen yin wannan rajista, ta kafa gidan yana na musamman, wato: cvr.inecnigeria.org.

A cewar sa, an yi gidan yanar ne saboda sababbin masu son yin rajista da waɗanda ke da rajistar su fara rajistar a intanet ta hanyar cike fom da tura shi tare da hoton su idan sun ƙare. 

Ya ce daga nan za su nuna buƙatar su a gidan yanar ta a ba su rana da lokacin da za su ziyarci ofishin INEC na jiha ko ƙaramar hukuma domin a kammala yi masu rajistar ta hanyar ido da ido inda za a ɗauki zanen yatsan su.

Duk waɗanda su ka riga su ka yi rajista a matsayin masu zaɓe su ma za su iya zuwa su gudanar da waɗansu ayyukan na yin rajista, misali tiransifa, gyara a bayanan su da kuma musanya katin zaɓe da ya yi dameji ko ya lalace ta hanyar yanar gizo.

Ya ce, “Ana fatan cewa ta hanyar wannan gidan yana za mu rage cinkoson mutane a cibiyoyin yin rajista , musamman da yake har yanzu ana fama da annobar korona (COVID-19), don a sauƙaƙa yin rajistar, a ba ‘yan Nijeriya kyakkyawar damar shirya wa yin zaɓe.

“A lura da cewa rajista ta hanyar yanar gizo kyauta ake yin ta, babu wani shagon da za a ce shi ne INEC ta yarda da shi kuma babu katin kuɗi da ake saye domin yin rajistar ta hanyar yanar gizo.”

Pai ya tabbatar wa da masu so su yi rajista da cewa ban da yin rajista ta hanyar gidan yana, jama’a za su iya takawa da ƙafar su zuwa kowace cibiya inda za a yi masu rajistar.

Ya ce za a ci gaba da gudanar da wannan aiki har zuwa wajen watanni uku na kashi na uku na shekarar 2022.

A cewar sa, saboda haka akwai isasshen lokaci da hukumar za ta kai kowane lungu da saƙo na jihar.

Ya ce, “A kan haka, bari in tabbatar wa da dukkan mazauna Filato cewa babu wanda ya cancanci yin rajista da za a ware ko a ina ya ke zaune ko kuma wani halin rayuwa da ya ke ciki. 

“Zan nanata cewa aikin rajistar katin zaɓe na ‘yan Nijeriya ne da ke cikin waɗannan rukunnan: waɗanda su ka cika shekara 18 da haihuwa zuwa sama kuma ba su yi rajista ba.

“Akwai kuma masu zaɓe waɗanda su ka yi rajista kuma su ka samu matsala da rajistar su a lokacin tantancewa a zaɓuɓɓukan baya ko dai da katin su ko na’urar yin rajista ta kasa ɗaukar zanen yatsan su, da kuma waɗanda su ka yi rajistar amma su na so a yi masu tiransifar wurin kaɗa ƙuri’ar su zuwa wani wurin daban.

“Haka shi ma wanda ya yi rajista amma ya na so ya gyara wani abu a cikin bayanan sa kamar rashin rubuta suna daidai da kwanan watan ranar haihuwa.”

Loading

Tags: Continuous Voter Registration (CVR)Hukumar Zabe ta KasaIndependent National Electoral CommissionINECJihar FilatoJosMalam Halilu PaiProfessor Mahmood YakubuRajistar masu zabe
Previous Post

An gina kabarin Umaru Kasagi kwana biyu kafin rasuwar sa, ya na da shekara 71

Next Post

Attah Dabai: Ba rabo da gwani ba…

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Alhaji Attah Dabai a bangon sashen Bahaushiya na cikin mujallar Fim ta Janairu, 2014

Attah Dabai: Ba rabo da gwani ba...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!