• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba don Afakallahu ba, da yanzu Kannywood ta zama tarihi (2)

by DAGA ALIYU ABDULLAHI GORA II
June 11, 2021
in Tsokaci
0
Ba don Afakallahu ba, da yanzu Kannywood ta zama tarihi (2)
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Cigaba daga ranar 7 ga Yuni, 2021
A CI-GABA da rubutun da na ke yi dangane da muhimmancin Afakallahu a matsayin shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ina mai jan hankalin mai karatu da cewa ya yi min adalci, domin rubutun da na ke yi ya na tamkar matsayin a gudu tare ne a kuma tsira tare.

Dangane da matsaya ta a rubutun da ya gabata, ina mai tabbatar maku da cewa akwai wasu ɗabi’u da ya kamata a tabbatar an gyara matuƙar da gaske ana neman mafita game da harkar fim a ƙasar Hausa. 

Na san an sha kai ruwa rana tsakanin Afakallahu da wasu abokan hulɗar sa, amma wannan ba dalili ba ne da zai sa a yi wa Afakallahu gurguwar fahimta.

Na tuna lokacin da A.A. Kurawa ya ke kan kujerar shugabancin hukumar, wanda ya kasance duk abin da ya shafi harkar fim da shi ake yi, amma saboda kusancin sa da ‘yan fim, haka aka yi ta yi masa zagon ƙasa, kuma daga cikin ‘yan fim ɗin ne. Hasali ma lokacin da wa’adin mulkin shi ya ƙare wasu ‘yan fim ɗin murna su ka riƙa yi tamkar an raba su da ƙaya. Sai daga baya kowa ya yi fargar Jaji, aka gano ashe dai Kurawan ya na da matuƙar muhimmanci a matsayin sa na mai ƙaunar harkar fim.

Ina mai tabbatar maku da cewa duk wani rashin fahimta da za a iya samu tsakanin Afakallahu da ‘yan fim, ni kawai ina kallon lamarin ne a matsayin rikicin cikin gida, wanda za a iya kawo ƙarshen shi cikin sauƙi, zumunci kuma ya ci gaba. 

Ni dai na san duk ɗaukakar da Afakallahu ya samu a yau, ba zai taɓa mantawa da karamcin ‘yan fim da harkar finafinai ba, domin har abada Afakallahu ɗan fim ne.

Da dama su na kallon Afakallahu a matsayin wanda ya kama hanyar sa ƙafar wando guda da harkar fim, amma fa duk masanin tarihin Kannywood ya san kowa ya na da nasa raunin daidai gwargwado.

Aboki na, idan da za a bar ni da ra’ayi na, da na ce har yau ban ga wani ɗan fim mai kishin Kannywood kamar Afakallahu ba. 
Ba zan manta ba, a zamanin Afakallahu ne manyan jami’an gwamnati su ka fara sanin muhimmancin ‘yan fim. 

A zamanin Afakallahu ne ɗan fim ya fara shiga Fadar Shugaban Ƙasa aka kuma karɓe shi hannu biyu-biyu, aka karrama shi. A zamanin Afakallahu ne aka yi wa ‘yan fim jagoranci har garin Daura su ka gana da Shugaban Ƙasa kai-tsaye.

A zamanin Afakallahu ne gwamnati ta kwararo wa ‘yan fim miliyoyin kuɗi domin a bunƙasa harkar finafinan Hausa. Akwai ɗan fim ɗin da ya samu naira miliyan 40, akwai mai miliyan 35, akwai mai miliyan 20, kai akwai ma wanda ya samu naira miliyan 60.

Afakalla (a dama) tare da Dakta Ganduje

Ina so ku sani cewa mafi yawa daga cikin su ƙaurace wa Kannywood su ka yi, kowa ya sauya sana’a don kawai kada ƙananan ‘yan fim su ƙaru da su. To ina kishin Kannywood ɗin ya ke a nan?

Akwai daga cikin su wanda ya kama katafaren otal a Kaduna, ya kuma sha alwashin sai ya kwashe tsawon watanni uku cur bai ga rana ba.

Kun ga kenan kowa ya na da nasa raunin. Don haka, ni a gani na, ya kamata kowa ya dubi kan shi, a taru a gyara inda ke buƙatar gyara, domin ina tabbatar maku da cewa duk ranar da aka ce ba ɗan fim ke kan kujerar da Afakallahu ke kai ba a yau, to tabbas labari zai sha bamban.

Mafi yawa mutum ya fi raina wanda ke da kusanci da shi. A kullum ɗabi’ar mu kawai ita ce “ni na iya, wane bai iya ba”. 

Duk gwagwarmayar nan da ake yi mu ma mun fuskance ta a baya, amma abin kunya wai a ce sau huɗu ana rubuta wa gwamnati takardar ƙorafi a kan Afakallahu, kuma daga ‘yan’uwan shi ‘yan fim! Hasali ma, wani bincike ya nuna yadda aka riƙa zuga wasu da cewa wai su nemi kujerar sa ta bayan fage. To, in dai industirin da na sani ce, na tabbatar da cewa duk wanda ya samu wannan muƙamin daga cikin ‘yan fim sai ya fuskanci irin wannan ƙalubalen.

To amma me ya sa Malam Rabo bai fuskanci turjiya daga ‘yan fim ba kamar yadda Afakallahu ke fama a yau?

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Aliyu A. Gora II tsohon Editan mujallar Fim ne

Loading

Tags: Aliyu Abdullahi Gora IIIsmail na'abba afakallahKano State Censorship BoardMalam Rabo AbdulkareemMOPPAN
Previous Post

Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Next Post

Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa

Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!