• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 22, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba ku fi ni son zaman aure da Sani Danja ba – Mansurah Isah

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 20, 2022
in Labarai
4
Mansurah Isah: 'Komai fa ƙaddara ce'

Mansurah Isah: 'Komai fa ƙaddara ce'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A KARON farko tun bayan mutuwar auren ta da fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja shekara ɗaya da rabi da ta gabata, Mansurah Isah ta fito ta yi hira a kan mutuwar auren. Ta ce komai fa ƙaddara ce daga Allah.

A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim kwanan nan, tsohuwar jarumar ta bayyana cewa tun bayan rabuwar su da Sani ta ke ganin maganganu kala-kala a game da al’amarin a soshiyal midiya, inda har wasu su na zagi, wasu kuma na nuna ɓacin rai a game da rabuwar da su ka yi.

Mansurah, wadda ke da ‘ya’ya huɗu da Sani – mace ɗaya, maza uku – ta ce ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da duniya labarin rabuwar su, ta yi hakan ne domin kada a matsayin ta na fitacciya a gan ta a wani waje ko ta tsaya da wani a riƙa yi mata kallon ta na yin wasa da aure.

Sani da Mansurah

Ta ce: “Na san mutane su na sha’awar zaman auren mu, har ma ana kafa misali da mu a cikin ‘yan fim da mu ka shafe tsawon lokaci mu na zaman aure. Don haka rabuwar ba ta yi wa kowa daɗi ba. 

“To amma mutane su sani, duk rashin jin daɗin su, mu mun fi su rashin jin daɗin hakan saboda mu ne mu ke zaune da juna kuma mu ka rabu.

“Mutane su sani, ba mun yi aure ba ne don mu rabu, domin idan mun yi ne don mu rabu babu yadda za a yi mu shafe shekaru goma sha huɗu mu na tare. Don haka Allah ne ya kawo ƙarshen zaman mu.

“Kuma duk son mu da zama tare, idan aka kawo wajen da zama ya haramta, to dole a yi haƙuri da juna. 

“Don haka kamar yadda mutane su ke nuna mana so da ƙauna, kuma su ke yi mana fatan alheri, mu ma mu na yi masu fatan alheri.

“Kuma ina ba su haƙuri da ƙaunar da su ke nuna mana. 

“Masu zagi kuma su je su yi ta yi, ba za mu hana su ba.”

Idan masu karatu sun tuna, mujallar Fim ce ta fara ba da labarin mutuwar auren Sani da Mansurah, a ranar 27 ga Mayu, 2021, bayan tsohuwar jarumar ta wallafa sanarwar rabuwar su a Instagram, saƙon da ta goge bayan minti kaɗan.

Mansurah Isah

Tun daga surutai su ka cika kafafen yaɗa labarai kan faruwar al’amarin, kowa na tofa albarkacin bakin sa a kai.

Ita kan ta Mansurah, ta fito ta yi tsokaci a kan maganganun da ake yi, waɗanda har yanzu ba su kau ba.

Loading

Tags: aureMansurah IsahrabuwaSani Musa Danjasoshiyal midiyasurutai
Previous Post

Siyasar Kannywood: Ana zargin T.Y. Shaban da Ahlan da cinye tallafin A.A. Zaura

Next Post

Garzali ya jaddada ƙaunar sa ga matar sa Habiba

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Garzali Miko tare da Habiba da ɗan su

Garzali ya jaddada ƙaunar sa ga matar sa Habiba

Comments 4

  1. Khadijat Mahuta says:
    3 years ago

    Allah ya kyauta ya Bata wani mijin

  2. AHMED MOHAMMED says:
    3 years ago

    Allah yarupamana asiri

  3. Pingback: Ba ku fi ni son zaman aure da Sani Danja ba – Karon Farko Mansurah Isah Tayi Magana Game Da Mutuwar Auren Ta - LastNg
  4. Pingback: Ba ku Fi Ni Son Zaman Aurena Da Sani Danja Ba ~ Mansurah Isah - NAIJASMART

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!