• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Siyasar Kannywood: Ana zargin T.Y. Shaban da Ahlan da cinye tallafin A.A. Zaura

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 20, 2022
in Labarai
0
TY Shaban (a hagu) da Shariff Aminu Ahlan su na kamfen ɗin A.A. Zaura a Kano

TY Shaban (a hagu) da Shariff Aminu Ahlan su na kamfen ɗin A.A. Zaura a Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA sabuwar dambarwa ta na neman ɓullowa a masana’antar finafinai ta Kannywood a sakamakon zargin da ake yi wa wasu fitattun jarumai na handame kayan tallafin da wani babban ɗan siyasa ya ba ‘yan fim.

Waɗanda ake zargin dai su ne T.Y. Shaban da Shariff Aminu Ahlan, waɗanda su ne shugabannin wata ƙungiya mai suna ‘Kannywood Celebrity Forum’ (KCF4AAZAURA) wadda aka kafa domin ciyar da manufofin fitaccen ɗan siyasar nan da ya yi takarar gwamnan Kano, Abdukareem Abdulsalam Zaura, wanda ake yi wa laƙabi da A.A. Zaura, gaba, musamman a masana’antar. Daga baya ya dawo ya na takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Ƙungiyar, wadda aka kafa kusan shekara ɗaya da ta gabata, ta ƙunshi jarumai da mawaƙa da sauran su, waɗanda su ka haɗe waje guda su na yin aiki tare, har ana ganib ba a taɓa samun haɗuwar ‘yan fim sun yi haka ba wajen tafiya wajen ɗaya.

Domin su ƙara ƙarfin tafiyar tasu, watanni bakwai da su ka gabata sun yi wani taro na musamman inda suka gayyato A.A. Zaura ɗin su ka karrama shi da lambar yabo mai girma tare da nuna masa su ne masoyan sa na haƙiƙa kuma sun shirya tsaf domin yaɗa kyawawan manufofin sa ga jama’ar jihar.

Ganin yadda su ka yi masa wannan karramawar, a nasa ɓangaren sai ya nuna jin daɗin sa sannan ya yi wa ‘yan ƙungiyar alƙawarin zai ba da wata gudunmawa ga masana’antar fim wadda ya kira da tallafin da ba a taɓa yin kamar sa ba.

Wannan ta sa ‘yan fim su ka shiga tsalle su na murna. A zaton su, gudunmawar za ta zo yau ko gobe ko jibi. Kuma abin ka da ‘yan fim, wasu har sun fara shirya abin da za su yi da kayan nasu idan ya zo gare su.

Alhaji A.A. Zaura

Sai dai yanzu rabin shekara kayan bai samu ba. Wasu sun fara ƙorafin yadda aka yi kayan bai samu ba, duk kuwa da yake shi A.A. Zaura ɗin ya ci gaba da raba kayan tallafi da bayar da gudunmuwa ga ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun mutane. Ko a ranar Talata da ta gabata an gan shi a fadar gwamnatin Jihar Kano ya na raba kekunan ɗinki sama da 10,000 ga ƙungiyar teloli ta jihar.

Wannan ya ƙara fito da ƙorafin ‘yan fim ke yi inda su ke jefa ayar tambaya ga nasu shugabannin, su na cewa ko dai an ba su Shaban da Ahlan kayayyakin sun rabe a tsakanin su ba tare da sun gayyato ɗan siyasar zuwa bikin rabon ba kamar yadda sauran ƙungiyoyi su ke yi.

Wasu kuma na zargin ko sun bi ta bayan gida ne sun karve kuɗin a maimakon kayan da za a raba wa jama’a su ka yi gaban kan su. Don haka ne ma wasu su ka yi yunƙurin ƙwatar wa kan su haƙƙin su a wajen shugabannin nasu ko dai su fito masu da kayan da aka ba su ko kuma su yi masu bayanin da zai gamsar da su.

Har zuwa yanzu dai Shaban da Ahlan ba su ce komai ba a kan wannan dambarwa da ta taso. Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin ji daga bakin su, amma kowa ya ƙi yin magana. Hakan ya sa wasu ke tunanin ko zargin da ake masu gaskiya ne.

Loading

Tags: A.A. ZauraAbdukareem Abdulsalam Zauragwamnan KanoKannywood Celebrity ForumKCF4AAZAURAShariff Aminu AhlansiyasaT.Y. Shabantakaratallafi
Previous Post

Fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ ne silar ɗaukaka ta – Saratu Abubakar

Next Post

Ba ku fi ni son zaman aure da Sani Danja ba – Mansurah Isah

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Mansurah Isah: 'Komai fa ƙaddara ce'

Ba ku fi ni son zaman aure da Sani Danja ba - Mansurah Isah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!