GA duk mai kallon shirin diramar ‘Daɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa24, irin zaman aure cikin rikici na Adama da Kamaye sanannen abu ne.
To a rayuwar zahiri Adama dai Hajiya Zahra’u Saleh ce, yayin da tsohon jarumi kuma babban furodusa Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa ya ke fitowa a matsayin Kamaye.
Sai dai duk da haka, wasu mutanen sun kasa rarrabewa tsakanin shiri da dahir, har su na yi masu kallon waɗanda su ka dace da zaman aure a rayuwar zahiri, wanda hakan ya sa ake ta yaɗa ji-ta-ji-tar wai za su yi aure da gaske nan ba da daɗewa ba.
Ganin yadda maganar ta ke ci gaba da yaɗuwa ne ya sa mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Hajiya Zahra’u kan al’amarin.
Jarumar ta yi wa wakilin mu bayani dangane da alaƙar ta da Kamaye da yadda ta ke kallon maganar da ake yi a kan su.
Hajiya Zahra’u ta fara da cewa: “To gaskiya maganar auren mu da Ɗan’azimi Baba, wato Kamaye, ni ma dai abin da ni ana faɗa kenan, amma dai tsakani na da shi babu wata maganar aure, domin ko soyayya ma ba ta shiga tsakanin mu ba, kawai dai mutane ne su ke yanke mana hukunci.”
Mun tambaye ta ko ba ta ganin irin yadda su ke zaman aure a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ ne ya sa ake wannan maganar?
Sai ta amsa: “To ai wannan ana ganin Kamaye ne da Adama, amma a zahiri Ɗan’azimi Baba ne da Hajiya Zahra’u.
“Don haka mutane su gane shiri daban, rayuwa ta zahiri daban. Domin ni ina ɗaukar Ɗan’azimi Baba ne a matsayin yaya na kuma ubangida na a harkar fim. Saboda haka mutane su daina kallon mu ma a matsayin masoya. Ni ƙanwar sa ce, kuma ubangida na ne.”
Shin ko Hajiya Zahra’u ta cimma burin ta a harkar fim?
Amsa: “To gaskiya zan iya cewa na cimma buri na, domin na samu arzikin jama’a. A yau ba a nan ƙasar ba duk duniya ina da masoya, kuma ina yin alfahari da su.
“Don haka babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah.
“Kuma ina kira ga ‘yan baya da su gane cewa ɗaukaka ta Allah ce; kada mutum ya rinƙa tunanin shi sai ya ɗaukaka.
“Mu da mu ka shigo harkar ba mu za ta Allah zai kai mu ga wannan matsayin ba. Don haka mutane a rinƙa yin tawakkali ana miƙa lamari ga Allah.”