CIKIN yardar Allah tsohuwar jaruma Fati Ladan a yanzu haka ta ɗauki hanyar cika shekara 6 a gidan mijin ta ko tari babu. Fati dai tun da ta yi aure babu mai jin ɗuriyar ta, domin ko a wurin sha’anin ‘yan fim ba ka ganin ta. Wasu lokutan sai mijin ta, Alh. Yerima Shettima, ya riƙa ɗora hotunan su a shafin sa na Instagram. Ko a lokacin da Fati ke industiri ba ta da ƙawa takamaimai. Hakan ne ma ya sa a lokacin bikin ta, yawancin matan fim ba su harlarta ba.
A tsawon shekara shida da jarumar ta yi aure Allah bai azurta ta da samun haihuwa da wuri ba, sai bayan shekara huɗu da auren su Allah Ya ba su ɗa namiji, wanda kafin ranar suna Allah Ya yi masa rasuwa.
Sai kuma a wannan shekara ta 2019 Allah Ya azurta su da samɓaleliyar ‘ya mace a cikin watan Ramadan.
Fati Ladan ta yi wa mujallar Fim ƙarin haske game da sirrin zaman auren ta da abubuwan da ta fuskanta bayan auren ta da kuma harkar fim. Ta fara da bada taƙaitaccen tarihin ta. Fati ta yi wannan hirar ne a gidan mijin ta da ke Gwamna Road, Kaduna, ana sauran kwana biyu a yi shagalin sunan ‘yar ta A’isha Humaira.
FIM: Ki gabatar wa da masu karatu da kan ki.
FATI LADAN: Suna na Hajiya Fati Ladan. An haife ni a garin Kaduna. Na yi firamare da sakandare duk a garin Kaduna.
Kafin na shiga jami’a, na shiga harkokin finafinan Hausa. Bayan na yi aure a shekarar 2013, sai na ci gaba da karatu na.
FIM: Kwatsam! Lokacin da Fati Ladan tauraruwar ta ke haskawa, wanda ana ganin in ba ta zo ta ɗaya ba, za ta zo ta biyu a fagen shirin fim, inda a wannan lokacin wasu burin su a ga cewa sun taso sun yi fice, ke kuma tauraruwar ki na haskawa, kawai sai ki ka yi aure. Me ya ja ra’ayin ki?
FATI LADAN: E, to, babu abin da ya ja ra’ayi na, da ma buri na ne. Kamar lokacin da na shigo industiri waɗanda su ke tare da ni sun san cewa buri na ne, roƙon Allah na ke yi kullum ina fara tashe Allah Ya kawo min miji in yi aure. To, addu’a na ne Allah Ya karɓa min.
FIM: An ce idan ’yar fim ta yi aure ana yi mata zarya, wasu daga cikin masu zuwa su na zuga ta ne don ta fita, wasu kuma masu zuwa su na ƙara mata ƙarfin gwiwa ne don ta zauna. Idan har kin fuskanci irin wannan ƙalubalen, wane abu ki ka ɗauka wanda ya jawo maki sirrin zaman ki har yanzu?
FATI LADAN: Katanga. Ka san Hausawa sun ce sai bango ya tsage ƙadangare ke samu ya shiga. Ni babbar nasara ta a zaman aure na gaskiya katanga na yi, ban bada ƙofa ga irin waɗannan mutanen su shigo gida na ba. Don haka katangan da na yi da kuma taimakon Allah Ya sa na samu nasara.
FIM: Idan ki ka ce katanga, ki na nufin kenan kin ƙaurace wa abokan sana’ar ki da ku ka yi harkar fim tare kenan?
FATI LADAN: Abokan sana’a ta mu na mu’amala. Babu kuma abin da ya canza. Idan na ce katanga, ba ina nufin ’yan fim ɗin mu kaɗai ba. Ai su masu hana ruwa gudu ba a cikin harkar fim ɗin kawai su ke ba, ko a ina za ka iya haɗuwa da su, maƙwabtan ka ne ko abokan zaman ka ne, ko’ina ka na tare da su. Don haka in ka ce ka yi katanga, ba wai ka na nufin mutanen da ka ke sana’a ba ne da su kawai. Kowa ya na da matsala, katangar da ka yi ka killace kan ka daga irin waɗannan tsirarun mutanen da su ke so su hana maka ruwa gudu a cikin zamantakewar auren ka.
FIM: Idan ki ka yi waiwaye, ki ka duba lokacin da ki ke yin fim da irin finafinan da ake yi a yanzu akwai bambanci?
FATI LADAN: Sosai akwai bambanci. Kusan shekara huɗu kenan ko zuwa biyar rabo na da industiri.
Gaskiya akwai bambanci sosai, saboda ina zama ina ɗan kallo jifa-jifa ina ganin yadda abubuwan su ka canza, ba kamar yadda mu ke namu lokacin ba.
FIM: Canji wane iri? Shiga ko saƙon da ake isarwa da sauran su?
FATI LADAN: E, to. Abubuwa dai sun canza, kamar labaran an fi bada ƙarfi a kan soyayya ga baki ɗaya. Yanzu in ka duba, rawa da waƙa sun fi ƙarfin saƙon da ake so a isar. A lokacin mu gaskiya ba a yi raye-rayen nan ba. Yanzu rawa da waƙa ya fi yawa. Kuma su su ke cinye labarin fim ɗin. Waɗannan su ne canje-canjen da aka samu.
FIM: Ki na kewar industiri?
FATI LADAN: Gaskiya ban yi kewar industiri ba.
FIM: Akwai wasu abubuwa da su ke tasowa na rashin girmama na gaba. Ya ku ka yi a zamanin ku? Don ban taɓa ji an ce ga abokiyar faɗan ki ba.
FATI LADAN: Ko lokacin mu ana faɗa, ba wai ba a yi ba ne. Sai dai wanda ake yi yanzu ya bambanta da na lokacin mu. Saboda yanzu ba a girmama na gaba, kowa yanzu ya samu dama ya samu lokaci ya na abin da ya ke so. Sai ka ga yarinya yanzu ta shiga shafin ta na Instagram ta yi abin ta ta harba. Mu kuma a lokacin mu ba mu yi haka ba. Gaskiya an samu ƙarancin tarbiyya da girmama na gaba a industiri. Kuma abin takaicin abin babu babba, babu yaro. In ƙananan su na yi, manyan ba za su iya yi masu faɗa ba, don su ma su na yi. Manyan mu ya kamata su riƙa haƙuri da junan su, saboda ƙanana su taso su ga abin da su ke yi. Ka ga idan babba ya ce “ki bari”, ba za ta iya cewa “ai kai ma na ga ka yi” ba. To, amma sun ga manyan na yi ai dole su ma za su yi. Kuma manyan ba za su iya yi masu magana su ji ba, saboda kowa abin da ya ga dama ya ke yi.
FIM: A yanzu da za ki samu dama za ki iya shirya fim na kan ki?
FATI LADAN: E, zan iya. Lokacin da na yi aure ina da wannan tunanin. Amma yanzu da ya ke abubuwa sun yi mani yawa a kai na, ina harkar kasuwanci na, ina kuma karatu. To, gaskiya ya ɗan ragu ba kamar lokacin da na yi aure ba. Amma ko yanzu ɗin in da hali zan iya yi.
FIM: Idan ki ka zauna ki na kallon finafinan da ki ka yi a baya, ya ki ke ji a ran ki?
FATI LADAN: (Dariya) Ba komai. Kawai ina jin daɗi.
FIM: Wasu na ganin idan ’yan fim su ka yi aure, musamman jarumai mata, yadda su ka saba a waje irin daɗi da walwala, musamman waɗanda su ke da yawan masoya da sauran su, sai ga shi mu na ƙirga shekaru har shida Fati Ladan na nan daram a gidan mijin ta ko tari babu, menene sirrin zaman gidan auren ki da mijin ki?
FATI LADAN: Haƙuri.
FIM: Wanene shi?
FATI LADAN: Miji na? Shettima.
FIM: E. Ya ya ke? Wanene shi a mu’amala?
FATI LADAN: Mutum ne mai haƙuri, son jama’a da barkwanci da kuma nuna soyayya sosai.
FIM: Lokacin da ki ka aure shi, mutum ne sananne. Amma kuma ɗan adawa ko kuma in ce mutum da ya ke so su janyo wa Arewa kwarjini. Domin a cikin kwanakin nan akwai wasu matasa da su ka bayyana shi a matsayin jarumin Arewa bayan tafiyar Sardauna. A lokacin da ku ka yi aure, wanda a lokacin ya kamata a ce kun zauna ku na jin daɗin auren ku, sai ga shi a gidajen talbijin da jaridu ana neman sa “wanted”, saboda sun ce a raba ƙasa da Inyamurai, da sauran su. Ya ki ka ji a ran ki? Ko da ma kin san wa ki ka aura?
FATI LADAN: Ƙwarai kuwa, da ma na san wa na aura. Ba wai kawai na yi auren ne da ka ba. Na san wanene shi kafin na aure shi. Domin na haɗu da shi na ɗan samu tarihin sa. Sannan bayan na haɗu da shi ya faɗa mani wanene shi. Ya kuma faɗa min duk abubuwan nan za su iya faruwa ko bayan mun yi aure. Tun kafin mu yi aure ya faɗa min an sha kama su.
FIM: Ba a ganin Fati Ladan a wurin sha’anin ‘yan fim. Ko menene dalili?
FATI LADAN: E, to, ba wai don ban da son mutane ba ne, a’a, ina da son mutane. Gaskiya ni ina da wani ra’ayi daban: ban cika son shiga harkar cikin harkar biki ba ne da sauran su. Don ko lokacin da na yi makaranta, ƙawaye na uku ne har na gama. Allah Ya yi ni ina da gudun abin magana ne. Shi ya sa na ke yawan keɓance kai na. Ba ina gudun mutane ba ne, sai don gudun abin da zai je ya dawo.
FIM: Ya mu’amalar ki ta ke da iyayen gidan ki na industiri?
FATI LADAN: Iyayen gida na har yanzu ina nan ina mu’amala da su, domin mu’amalar mu mu’amala ce wadda ta ci gaba har bayan na yi aure, aka ɗora su ka ci gaba da yi da maigida na. Iyayen gida na akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin su da maigida na.
FIM: Me ki ke tunawa a lokacin da ki ke harkar fim, wanda in ki ka tuna za ki yi ta dariya ki na yi wa Allah godiya?
FATI LADAN: Abin da na ke tunawa na daɗi shi ne lokacin da kowa ke gudu na, ba a so a sa Fati Ladan a fim, ana cewa ina da matsala. A lokacin tsohon miji na ya zo ya bada kuɗi ya na ɓata min suna ya na cewa matar aure ce ni na zo na shiga fim, kowa na gudu na. A lokacin da idan na zo wuri ma sai a tashi a ce virus ce ta zo! Ana cikin wannan sai Ali Nuhu ya zo ya yi ‘casting’ ɗi na, ya sa ni a wani fim mai suna ‘Adamsy’. Shi ne fim ɗin da ya ɗaga ni, shi ne fim ɗin da aka san ni da shi, shi ne kuma fim ɗin da na ke tinƙaho da shi har yanzu.
FIM: Me ki ke tunawa wanda za ki ga ki na hawaye, wanda ya faru a baya?
FATI LADAN: Ba zai wuce duk ƙalubalen da mutum ya fuskanta a lokacin ya na industirin ba.
FIM: Kin auri miji wanda hannun shi a buɗe ya ke, yau sallama, gobe sallama. Sai kuma duk wacce ta yi aure ta na so ta kasance tare da mijin ta daga ita sai shi ne a ɗaki, sai dai in za su fita. Amma sai ga shi mutum ne kusan kullum waya, jama’a da sauran su. Ya ki ke ji musamman in ya fita waje ya bar ki a gida?
FATI LADAN: Ina jin daɗi. Saboda shi mutum ne na mutane. Kuma duk mutumin da ka gani ba shi da mutane bai cika mutum ba. A haka ina alfahari da shi.
FIM: Kin auri mijin ki a matsayin ɗan gwagwarmaya, kwatsam sai ki ka ji shi ya tsunduma a siyasa, fosta na yawo a gari. Ya ki ka ji a ran ki?
FATI LADAN: Na san da haka da ma. Domin tun da mu ka haɗu da shi ya faɗa min. Ya ce min shi ɗan kare haƙƙin bil’adama ne. Amma zuwa gaba kuma zai yi siyasa.
FIM: Bayan aure sai ga shi Ubangiji ya azurta ki da haihuwa. Ya ki ka ji a ran ki?
FATI LADAN: Na yi farin ciki sosai wanda ba ya misaltuwa saboda da ma buri na kenan. Ba burin da ya wuce ’ya mace ta yi aure, ta zauna lafiya da mijin ta, kuma Allah Ya ba ta zuri’a. Kuma in za ka duba ka gani, ba yau aka yi auren ba, an samu jinkiri wanda ya zama alheri ne. Ga shi Allah Ya azurta mu da ’ya mace yanzu.
FIM: Kin ɗauki shekaru ba ki samu haihuwa ba. Ya ki ka gani ta shi ɓangaren shi in ya kalle ki, akwai damuwa a tare da shi? Bayan shi akwai dangin miji, su na ɗaya daga cikin waɗanda ke hura wutar cewa “ya za a yi ka auro ta har yanzu ba ta haihu ba, me ke faruwa ne?” Kin samu irin wannan ƙalubalen daga wurin su?
FATI LADAN: A’a, gaskiya ban samu ba. Saboda wani lokacin ma ni na ke damuwa in ce ni ban san me ke damu na ba, sai ya ce ai shi da ɗa da ba shi, za mu zauna. Kuma ɓangaren gidan su, ban samu matsala ba. Saboda gidan su, gidan mu ne. Saboda yadda na ke sakewa in yi abu a gidan su a gidan mu ma ba na sakewa haka.
FIM: Me ke ɓata wa mijin ki rai?
FATI LADAN: Roƙo. Ba ni. Yawan ba-ni-ba-ni. Yanzun nan zai buga. Ya na da alheri sosai, amma kuma bai son mutum ya nuna abin shi ya ke so ba shi ya ke so ba; a kan wannan za ku samu matsala da shi.
FIM: Me mijin ki ya fi so?
FATI LADAN: Zara! (Dariya)
FIM: Ya ki ka yi lokacin da ku ka yi aure wurin abinci? Musamman shi mijin ki ya na yawan zama a garuruwan Yarbawa, akwai abubuwan da ya ke ci, ke kuma kin tashi a Arewa. Ya ku ka ƙare a kan abinci?
FATI LADAN: Ai miji na da na aure shi ai ni na ma yi mamaki. Domin mutum ne mai son abincin Arewa, bai damu da abincin Kudu ba. Kuma har yanzu da mu ke maganan ma. Saboda lokacin da mu ka haɗu da shi, burin shi kawai in mun yi aure in ci gaba da dafa masa abincin Arewa kamar irin tuwo da miyar kuka, fate, wato faten tsakin nan, ka san Bazazzagi ne!
FIM: Kin taɓa samun ƙalubale a waje? Don ba lallai ba ne wasu masoyan ki su san kin yi aure, irin wani ya nuna zai yi maki magana ko kun je sayayya haka ko kuma in kun yi tafiya zuwa wani gari?
FATI LADAN: A cikin garin nan ma na sha samun waɗannan matsalolin. Lokacin da mu ka yi aure farko-farko, in mun ɗan fita shaƙatawa haka sai a zo a ce za a yi hoto da ni. Ya na zaune ma sai ka ga wani na nema ya tunkuɗe min miji, in na ce zan yi faɗa, sai ya ce, “A’a, masoyan ki ne; ba wani abu ba ne, soyayya ya kawo su”. Bai taɓa nuna min canjin fuska ba ko ya nuna min cewa shi ya yi da-na-sanin aure na ko wani abu. Bai taɓa ba.
FIM: Mecece shawarar ki ga masu cewa ’yan fim idan su ka yi aure ba su zama?
FATI LADAN: Shawarar da zan ba su shi ne su daina, babu kyau. Saboda ba auren ’yan fim kaɗai ke mutuwa ba. In ka duba, za ka ga in za a ƙirga ’yan fim da auren su ya mutu, ba su fi ’yan tsiraru ba a kan waɗanda ba ’yan fim ba. Amma su ’yan fim da ya ke an san su sai a riƙa cewa auren su na mutuwa. Kuma shi aure da rayuwar sa da mutuwa duk na Allah ne. Babu macen da za taso ta yi aure ta fita, sai in ya zama dole. Don Allah su daina yi mana irin wannan kallon.
FIM: Mecece shawarar ki ga ’yan fim game da abubuwan da ke faruwa?
FATI LADAN: Shawara ta a gare su shi ne manya su san su manya ne su, su riƙa haƙuri. An ce inda saniyar gaba ta sha ruwa ta wuce a nan ta baya ma za ta sha. Duk abin da su ke yi shi ma na bayan za su zo yi, har waɗanda ma ba su shigo ba, su na karantawa, ana bugawa a mujalla. Idan su ka ci gaba da yin haka, za a zo a kai wani matsayi da babu wani babba a cikin masana’antar. Dole ne a matsayin su na manya sai sun yi haƙuri sun danne zuciyar su, ta yadda na baya za su taso su yi masu biyayya. Da ma an ce babba shi juji ne. Wannan shi ne shawara na a gare su.
FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa masoyan ki da na mijin ki game da irin addu’a da su ka yi ta yi maku bayan wannan ƙaruwa da ku ka samu?
FATI LADAN: Godiya ne na musamman. Allah Ya saka masu da alheri, Allah Ya bar ƙauna. In ka tuna shekarar mu na shida kenan, har wasu na cewa bayan auren ai wata uku za mu yi mu rabu, wannan addu’ar masoya ne. Mun gode masu. Allah Ya saka da alheri.
FIM: Mun gode.
FATI LADAN: Ni ma na gode.