FITACCEN jarumi a Kannywood, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya bayyana cewa akwai kuskure a maganar da furodusa Malam Sani Muhammad Sani ya yi a kan malaman jami’a masu nazarin finafinan Hausa.
Idan kun tuna, Sani ya faɗa a wani rubutu a Facebook, wanda mujallar ta fassara ta buga, cewa shi ne ya fara saka Ali Nuhu a fim, sannan yawancin tarihin da malaman jami’a su ke bayarwa kan Kannywood “ƙarya ne kawai.”
Sani, wanda shi ma jarumin fim ne, ya ce: “Yawancin tarihin Kannywood ƙarya ne kawai wasu da ake kira furofesoshi da masu son kai, marubuta masu nuna ɓangaranci, marasa ƙwarewa, waɗanda ba su damu da su ƙosar da jama’a da ƙarya a yayin da su ka hakimce cikin ofisoshin su ba.”
To amma a saƙon da ya turo wa mujallar Fim, Iyan-Tama, wanda shahararren furodusa ne, ya ce wannan maganar kuskure ce.
Ya ce: “Ai tarihi riwaya-riwaya ce, kowa da nasa source ɗin.
“Ko a hadisan Manzon Allah SAW ana samun riwaya daban-daban.
“Ya na da kyau idan mutum ya ba da tarihin da bai yi maka daidai ba, to kai ma ka rubuta naka, ka zo da hujjojin da masu karatu za su gamsu, shi kenan faƙat!
“Amma cewa akwai wasu furofesoshi da su ke rubuta tarihin fim ko ‘yan fim kaza-kaza, wannan kuma wani abu ne daban. Mu mun gamsu da riwayar su da kuma hanyoyin da su ka bi domin tabbatar da rubuta tarihin Kannywood da ‘yan Kannywood.
“Kowa ya na da damar rubuta nasa tarihin, amma ya zo da hujja.
“Rubutun da Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi a kan Kannywood babu wani mahaluƙi da zai ce akwai son zuciya ko ɓangaranci ko wariya, sai dai shi ma ko dai ya na son nuna nasa ɓangaranci ne ko kuma wariyar. Hujja tun daga tushe ita ce hujjar Farfesa Abdalla Uba Adamu. Kowa ya zo da tasa hujjar da ta fi tasa.
“Daga ƙarshe, Sani Muhammad Sani kana da ‘yancin faɗar cewa kai ne ka fara saka wanda ake magana a kai a fim. Idan ta tabbata kai ɗin ne, domin shi dai ‘credit’ ya na tabbata ne ga wanda ya ke da shi, ba wani ba.”