BABBAR furodusa Mansurah Isah ta bayyana cewa a yanzu haka ta yi nisa a aikin shirya wani gagarumin fim da ta ce babu wani fim da aka taɓa yi a Kannywood da ya kai shi.
Mansurah, wadda tsohuwar jaruma ce, ta faɗa wa mujallar Fim cewa sunan fim ɗin ‘Bakandamiya’.
Da ta bayani kan sabon fim ɗin, furodusar ta bugi ƙirji da cewa: “Kowa ya sani ni ‘yar Kannywood ce kuma ina kishin harkar masana’antar da kuma alfahari da ita, don haka a yanzu na ke zuba kuɗi don cigaban masana’antar.
“Kamar yadda a baya na shirya manyan finafinai irin su ‘Akila’ da ‘Fanan’, kuma sai masu kallo su ke tunanin a yanzu wanne fim za su ƙara gani daga kamfanin mu, to a gaskiya mu na finafinai da za mu saka, amma dai a yanzu mun shiga aikin wani gagarumin fim wanda na ke ganin nan da wata mai zuwa na Janairu za mu sake shi a YouTube canel ɗi na mai suna ‘Mansurah Isah Channel TV’ da mutane za su rinƙa kallo.”
Mansurah ta faɗi wani salo da ta zo da shi wanda ya yi kama da tsarin nan na darakta Ashiru Nagoma a shekarun baya da ya riƙa saka dukkan manyan jaruman Kannywood a fim ɗaya, amma ita kuma daraktoci za ta saka. Ta ce: “Kamar yadda na saba yin fim mai ɗaukar hankali, to haka wannan lokacin ma haka zai kasance, ko ma ya fi na baya da ma sauran duk wasu finafinan da aka yi a masana’antar Kannywood. Saboda shi wannan sabon salon da na zo da shi, duk zango daraktan sa daban ne: Zango na farko Isa Alolo shi ne darakta, zango na biyu kuma Hassan Giggs ne, haka dai zai ta tafiya.
“Akwai su Hussaini Ali, Nazifi Asnanic, Ali Gumzak, Kamal S. Alkali, Falalu Ɗorayi, Yakubu Muhammad, Ali Nuhu. Kai, duk wani darakta da ake damawa da shi da ma wanda aka san ya na darakta, shi ma zai shiga cikin aikin a matsayin darakta.
“Duk da dai mutane za su ce wannan abin ai kwamacala ne, to ba haka ba ne. Kawai dai ku jira ku ga yadda labarin ya ke da kuma yadda aikin zai gudana, domin shi wannan aikin mai suna ‘Bakandamiya’, to ya ci sunan nasa saboda na kandamo aikin da yawa, na kandamo labarin da yawa, don haka saƙon da ya ke cikin sa ma mai yawa ne.”
Furodusar ta yi yi roƙo ga Allah kamar haka: “Ina roƙon Allah ya ba mu sa’a mu yi aikin da mutane za su yi alfahari da saƙon da ya ke cikin fim ɗin, ya zama sun amfana da shi.”