SAU da dama idan aka ga wani jarumi ya na taka wata rawa a fim wasu sai su ke ɗauka cewa da man sana’ar sa ce, don haka ya ke yin abin yadda masu sana’ar su ke yi.
Haka ne ya ke faruwa ga jarumi Muhammad Murtala ko Ɗantani Maishayi kamar yadda aka fi sanin sa a cikin shirin dirama na ‘Daɗin Kowa’ da ake haskawa a gidan talbijin na Arewa 24.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, Murtala ya bayyana cewa, “Gaskiya sau da dama mutane sun zata ni ina yin sana’ar shayi ne tun kafin na zo shirin ‘Daɗin Kowa’, kuma ba haka ba ne. Kawai dai an gwada ni ne sai aka ga na dace da wajen, kuma cikin ikon Allah sai na bayar da abin da ake so.
“Amma dai ban taɓa yin sana’ar shayi ba.
“Kawai dai abin da na sani shi ne bayan na samu kai na a matsayin Ɗantani Maishayi, sai kuma na faɗaɗa tunani na, na riƙa zama a wajen masu shayi ina kallon yadda su ke yin mu’amalar su da jama’a, wanda hakan ya sa na ke ƙara samun ƙwarewa.
“Amma dai mutane su gane, shi fim ana isar da saƙo ne, don haka idan mutum ya ƙware zai iya hawa kowane rol da aka ɗora shi.
“Kamar misalin da zan ba ka. Ka ga Sallau a zahiri maigida na ne, shi da Nuhu Kansila. Su ne su ka koya mini fim tun mu na wasan daɓe. To amma ka ga a ‘Daɗin Kowa’ yaro na ne. Wannan duk fim ne ya zo da haka don a isar da wani saƙo.
“Don haka idan na yi ba daidai ba, shi ne ya ke gyara mini saboda maigida na ne.
“Don haka ina kira ga abokan sana’ar mu su riƙa sanin mutuncin mutanen da su ka koya masu wani abu a rayuwa kamar yadda na ke alfahari da Sallau da Nuhu Kansila.”