WATA kotu a Kano a yau ta bada umarnin gaggawa a kamo mata fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) a kan zargin raina kotu. Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari’a Khalid Ibrahim Sarki Yola ya bada wannan umarnin ne saboda bijire wa umarnin kotun ta shari’ar Musulunci da Rarara ya yi kan ya bayyana a gaban kotun domin ya kare kan sa kan wani zargi da ake masa.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wani mutum ya yi barazanar zai maka Rarara a kotu kan tuhumar sa da saka matar sa Maryam a cikin bidiyon wata waƙar siyasa da ya yi a Katsina mai suna ‘Jiha Ta’ da kuma ɓoye matar. An tsara waƙar ne don a nuna alhini kan matsalar rashin tsaro da ke faruwa a Jihar Katsina, kuma Ali Nuhu da Isa Alolo ne su ka bayar da umarni a wajen shirya bidiyon ta.
Maryam na daga cikin ‘yan fim da su ka fito a bidiyon waƙar.
Mijin ta ya yi iƙirarin cewa auren su da ita dududu bai wuce watanni biyar ba, kuma ya sha alwashin maka Rarara a kotu domin ya saka matar sa a fim ba tare da izinin sa ba.
Daga nan ya cika alƙawarin da ya yi na maka mawaƙin a kotu a ranar 1 ga Disamba.
Bisa wannan tuhumar ce kotu ta aike wa da mawaƙin sammaci kan ya bayyana a gaban alƙali a yau Talata, 22 ga wata.
Rarara dai bai je kotun a yau ba.
Sai dai a bayanin da ta saki ta hanyar bidiyo a Instagram, Maryam ta wanke Rarara daga zargin da ake yi masa, ta na faɗin ita yanzu ba ta da aure. Ta ce: “Babu ruwan Rarara, kawai tsohon miji na, ya yi haka ne domin ya ɓata mai suna ya kuma zubar mai da mutuncin sa.” A bayanin nata, sabuwar jarumar ta bayyana cewa shi mijin nata ya na so ne su koma su ci gaba da zaman aure, ta ce, “ni kuma na ce ba zan koma ba.” Ta ce, “Saboda irin sakin wulaƙancin da ya min ne ba zai iya zuwa ya haɗa idanu da iyaye na ba, ya fuskance su ya ce zai dawo da ni; to shi ne ya zagayo ta wannan hanyar don ya zubar min da mutunci ya kuma zubar wa da Rarara da mutunci.” Maryam ta ƙara da cewa ita ba ma Rarara ne ya ɗauke ta ya saka ta a bidiyon waƙar tasa ba.
“Furodusa ne ya ɗauke ni kuma shi ma ba shi ya ɗauke ni ba, ƙawa ta ya ɗauka, shi ne ta ɗauke ni mu ka je. “Kuma da na je sai da na kira mahaifiya ta na haɗa su su kai magana, kuma aka ce in an gama za a kai ni a tantance ni.
“Amma shi ne ya zagayo daga baya ya na cewa ina da aure. To ni ba ni da aure! “Don haka shi Rarara bai ma san ni ba, bai ma taɓa gani na ba sai ranar da za a ɗauki bidiyon, har yake tambaya wace ce waccan da aka ce an zo da ita.”