• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jaruman Kannywood, Abdul M. Shareef da Maryam Malika sun zama ɗaya

by Editors
June 27, 2025
in Uncategorized
0
Jaruman Kannywood, Abdul M. Shareef da Maryam Malika sun zama ɗaya

Amarya Malika da ango Abdul M. Shareef a wurin dinar auren su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BURIN jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef (Abdul M. Shareef) da Maryam Muhammad Ƙaura (Maryam Malika) ya cika a yau domin kuwa an ɗaura masu aure.

An ɗaura auren Abdul da tsaleliyar sahibar tasa a yau Juma’a da misalin ƙarfe 1:15 na rana, bayan an gama sallar Juma’a a Masallacin Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.

Ango Abdul M. Shareef tare da masoya a wurin ɗaurin auren sa a yau
Daga hagu: Musa Mohammed Abdullahi, Ali Nuhu, da Tijjani Faraga a wurin ɗaurin auren

Wasu daga cikin ‘yan fim ɗin da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, da Malam Tijjani Faraga, Malam Musa Muhammad Abdullahi, Sanusi Oscar 442, Daddy Hikima, Mustapha Nabraska, Naziru Ɗanhajiya, Nasiru Naba, Nura MC Khan, Umar Gombe, Lawal Ahmad, Waziri Garba Bado, Hannafi Rabilu Musa, Hamza Talle Maifata, Salisu S. Fulani da ƙanen ango, wato Umar M. Shareef.

Kafin ranar ɗaurin auren, an yi shagulgula da suka haɗa da wankan amarya (bridal shower), ƙwallon ƙafa da dina.

A ranar Talata da ta gabata ne aka gudanar da wankan amarya ɗin a ɗakin taro na otal ɗin Hamdala da ke Titin Muhammadu Buhari. Sai dai bikin na mata ne zalla.

A shekaranjiya aka buga wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakanin abokai (friendly match), a filin wasa na otal ɗin Hamdala. ‘Yan fim da dama, musamman na Kaduna, sun halarta.

Sai kuma jiya aka gudanar da ƙasaitacciyar dina, inda ‘yan Kannywood maza da mata daga jihohin Kano, Katsina, Jos da Kaduna suka haɗu.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Abdul yana da mata ɗaya da ‘ya’ya biyar, ita kuma Maryam tana da ‘ya’ya uku a gidan tsohon mijin ta.

Ango yana gaisawa da abokan arziki a wurin ɗaurin auren

Loading

Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

Next Post

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

Related Posts

Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi
Labarai

Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi

November 2, 2026
Kamfanin Tozali ya yi kira da a tallafa wa waɗanda suka tsira daga matsalar tsaro a bikin Henna Ball karo na 8
Al'adu

Kamfanin Tozali ya yi kira da a tallafa wa waɗanda suka tsira daga matsalar tsaro a bikin Henna Ball karo na 8

November 2, 2026
Hotunan taron Tozali Henna Ball da karramawa
Labarai

Hotunan taron Tozali Henna Ball da karramawa

November 1, 2026
Isa Ja ya karɓi kyautar Tozali, yayin da Naziru da Amal suka ƙaurace
Labarai

Isa Ja ya karɓi kyautar Tozali, yayin da Naziru da Amal suka ƙaurace

October 31, 2026
Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja
Labarai

Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja

October 24, 2026
Zaɓen 2027: Gidan Dabino, Rarara, Abdul Amart da wasu ’yan Kannywood 14 sun shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano
Siyasa

Zaɓen 2027: Gidan Dabino, Rarara, Abdul Amart da wasu ’yan Kannywood 14 sun shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano

October 24, 2026
Next Post
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

MOPPAN ta yi wa al'ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!