(Wannan bayanin likitoci ne muhimmi a kan ƙwayar cutar korona da na ci karo da shi. Ya yi ma’ana ƙwarai da gaske, shi ya sa na sadar da shi gare ku)
JAMI’AR Johns Hopkins (wadda ke bin diddigin yaɗuwar ƙwayar cutar korona) ce ta samar da taƙaitaccen bayanin da zai kare yaɗuwar ƙwayar cutar.
1. Ƙwayar cutar koronabairus (‘coronavirus’) ba rayayya ba ce, ta kasance ɗan ƙaramin sinadarin furotin ne lulluɓe da mayanin kitse (maiƙo). Mayanin kitsen ne ya ke ba ta kariya, watau za ta lalace da zarar an goge ko an narkar da kitsen. Da zarar ta gwamutsa da tubalin halittar jiki (‘body cells’) na idanu ko hanci ko baki (waɗanda su ka kasance masu lema-lema), sai ta rikiɗa a cikin tubalin, ta sauya yanayi zuwa fitinannun ƙwayoyin halitta masu ruɓanya da kai farmaki.
2. Tunda an ce ƙwayar cutar nan ba rayayya ba ce, ƙaramin sinadarin furotin ne kawai da ke samun kariya daga kitse, kenan ba za a iya kashe ta ba, sai dai ta na rugujewa ne ta lalace da kan ta. Wannan rugujewar ta danganta ne da yanayin zafi ko sanyi ko danshi da kuma fasalin abin da wannan ƙwayar cutar ta sauka a kan sa.
3. Ƙwayar cutar nan a karan kan ta ta na da saurin rugujewa, sai dai wannan kariyar da ta ke samu daga siraran mayanin kitse shi ke sanya ta daɗewa ba tare da ta ruguje ba.
Shi ya sa aka ce sabulu ko sinadaran wanki sun kasance muhimman abubuwan kariya daga ƙwayar cutar, domin kumfa ta na tsittsinka kitse ko maiƙo (shi ya sa aka ce mutum ya rinƙa murza kumfa a hannayen sa sosai na tsawon daƙiƙa 20 zuwa sama saboda a samar da kumfa mai yawa a hannu).
Idan aka cimma nasarar tsittsinka wannan mayanin na kitse ko maiƙo, ƙananun sinadaran furotin ɗin can za su tarwatse su lalace da kan su.
Da zarar wannan kariya ta mayanin kitse ta kau, sinadaran furotin ɗin za su kau.
4. Zafi (ko ɗumi) ya na narkar da kitse; shi ya sa aka ga dacewar yin amfani da ruwa mai ɗumi wanda ya zarce ma’aunin digiri salsiyus 25 yayin wanke hannaye ko tufafi da sauran su. Haka kuma, ruwa mai ɗumi ya na ƙara yawan kumfa, don haka amfanin sa ya ruɓanya.
5. Barasa ko kuma duk wani abu da aka cakuɗa da sinadaran barasar da kashi 65 cikin ɗari ya na kawar da kitse nan take, musamman mayanin kitsen da ya lulluɓe ƙwayar cutar.
6. Haɗin kashi 1 na sinadarin bilicin da kashi 5 na ruwa shi ma kai-tsaye ya na kawar da waɗannan sinadaran furotin ɗin ya kuma ruguza su daga tushe.
7. Ruwa mai haɗe da oksijin (‘oxygenated water’) ya na taimakawa ainun bayan sabulu da barasa da sinadarin kulorin. Wannan garwaye na ruwan oksijin ya na tarwatsa ƙwayoyin cutar furotin ɗin nan. Da yake ana amfani da tsuran garwayen ne babu sirki, to ya na iya yi wa fatar mutum lahani (don haka a yi taka-tsantsan wajen amfani da shi).
8. Sinadaran kashe ƙwayoyin bakteriya ba su aiki a nan! Ƙwayar cutar korona ba rayayya ba ce kamar bakteriya, su kuma sinadaran kashe ƙwayoyin bakteriya ba su kashe abin da ba shi da rai. Ko da yake su na kassara yanayin ta.
9. A guji karkaɗe tufafi ko zannuwa ko tsummokara saboda idan an karkaɗe, ƙwayar za ta bazu cikin iska a shaƙe ta, ko ta kai ga baki ko ido. A yayin da ƙwayar cutar ta ke manne a jikin abubuwa masu ‘yan hudoji, ta na rasa karsashi, ta na kuma rugujewa a cikin sa’o’i uku idan ta na jikin tsumma ko abubuwa masu hudojin irin tufafi.
A jikin tagulla (‘copper’) da katako (‘wood’) ta kan yi sa’o’i huɗu. Kuma ta kan yi sa’o’i 24 a jikin kwali, sa’o’i 42 a jikin ƙarfe da kuma sa’o’i 72 a jikin filas (robobi).
To idan aka karkaɗe kayan ko aka share waɗancan abubuwa da mashari kamar na gashi ko tsintsiya, ƙwayoyin cutar su kan tashi su rinƙa yawo cikin iska har na tsawon sa’o’i 3 kafin su lalace; a haka su na iya nufa hancin mutum kai-tsaye su shiga.
10. Ƙananan ƙwayoyin cutar korona su na watayawa a sarari mai sanyi, da kuma sanyi irin na AC a gidaje ko motoci. Haka kuma su na buƙatar danshi wanda za su dauwama tare da shi, musamman idan ya haɗu da duhuwa.
Wato kenan gusar da danshi ko busar da wuri ko ɗumama wuri tare da haskake muhalli ya na dakushe wanzuwar ƙwayar cutar da sauri.
11. Hasken UV (ana samun irin wannan haske daga hasken rana kai-tsaye) ya na karya lagon ƙwayoyin cutar furotin ɗin da ke haddasa ƙwayar cutar korona. Sai dai a yi hattara, domin ya na kassara sinadarin kolajin (‘collagen’) wanda shi ma furotin ne da ke amfani a jikin fatar bil’adama, rashin sa ya na haifar da tamoji ko kansar fata.
12. Ƙwayar cutar korona ba ta ratsa lafiyayyar fatar jiki. (Kenan tsabta na da matuƙar muhimmanci a wannan yanayi.)
13. Ruwan bula-lemu (‘vinegar’) ba shi da wani amfani a wannan sabga, domin ba zai iya kassara kariyar nan ta mayanin kitse na ƙwayar cutar ba.
14. Ruwan sifirit (‘ethylated spirit’) ko burkutu ko turare ba su aiki. Burkutu mafi ƙarfi ta na da sirkin barasa ne kashi 40 cikin 100, a yayin daƙile ƙwayar cutar korona kuma ana buƙatar kashi 65 cikin 100 ne.
15. Haɗaɗɗen sinadarin kurkure baki na musamman mai ɗauke da kashi 65 cikin 100 na barasa ya na kashe ƙwayoyin sinadaran furotin mai ɗauke da ƙwayar cutar korona.
16. Daidai tsawon rufewar da aka yi wa wuri mai ɗauke da ƙwayar cutar korona, daidai tsawon lokacin da za ta ɗauka a wurin kenan. Saboda haka barin iska ta na kaɗawa a wuri ya na kawar da ita.
17. Sanin wannan ya na da matuƙar muhimmanci! Dole ne mutum ya rinƙa wanke hannayen sa kafin da kuma bayan ya shafi fuskar sa (ido, hanci da baki), da kuma kafin da bayan cin abinci ko taɓa kuɗi ko makulli ko mariƙin ƙofa ko makunnar lantarki ko rimot ko wayar hannu ko agogo ko komfuta ko tebura ko talbijin da makamantan su. Haka kuma a tsabtace hannu bayan an fito daga banɗaki.
18. A yawaita damsasa hannaye ta hanyar wanke su a kai a kai, domin ƙananan ƙwayoyin sinadaran su na maƙalewa a kowane loko da kwalogo.
19. A rinƙa yanke farce domin kar wannan ƙwayar cuta ta sami mafaka.
(Fassara daga Ingilishi zuwa Hausa:
©Hafiz Koza.
07060438556
Da taimakon Mai Girma Galadiman Daura, Hakimin Mai’aduwa, Alhaji Ahmad Diddiri Ahmad)